’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa
Published: 4th, December 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata.
Ya ce ana zargin matashin ne mai shekaru 17 da aka fi sani da Amir, wanda makanike ne da kashe matar ta hanyar daba mata wuka.
Wani makwabcin wajen ya shaida cewa ana zargin matashin ne da shiga gidan ta hanyar tsallake katanga bayan ya jira ragowar mutanen gidan sun shiga ciki.
A cewar majiyar, matashin ya ɗauki wuƙa ya daba wa matar gidan, wadda ba a bayyana sunanta ba, a ƙirji da wuya, sannan ya tafi da wayarta da na’urar cajin hannu (power bank).
Majiyar ta ƙara da cewa bayan aikata laifin, wanda ake zargin ya koma gidansu ya wanke tufafinsa da kayan da ya yi amfani da su domin kauce wa bin sahunsa.
Rahotanni sun ce ƙanwar mijin wadda aka kashe ce ta fara sanar da jama’a bayan ta ji ihun matar tana neman taimako.
Lokacin da ta fito ta duba, sai ta ga wanda ake zargin yana gudu ya koma gidansu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an ’yan sanda sun kama matashin da misalin ƙarfe 2:30 na rana.
Sai dai kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, bai samu damar yin ƙarin bayani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa.
Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa.
Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyuYa gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi.
Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.
Ya ce: “Da na ga irin martanin mutane bayan an ambaci sunana, na san cewa ba zan bari na gaza ba, ba zan bai wa ’yan ƙasata kunya ba. Duk abin da ya kamata mu yi, za mu yi, kuma na san da taimakon Allah za mu yi nasara.”
Musa ya ƙara da cewa abin ya ba shi mamaki ganin irin goyon bayan da aka ba shi a kafafen sada zumunta.
“Na je kafafen sada zumunta kuma abin ya ba ni mamaki ganin irin martanin mutane. Wannan yana nuna cewa mutane suna son ganin Najeriya ta zauna lafiya.”
Ya ce wasu suna cewa ’yan Najeriya ba sa son Najeriya, amma bai yadda da wannan batu ba.
“Idan wasu suna cewa ’yan Najeriya ba sa son ƙasarsu ina cewa ba haka abun yake ba, ba su san ’yan Najeriya ba.”
Ya kuma yi magana kan kashe-kashen da ake fama da su a wasu sassan ƙasar nan.
“Ko a kira shi kisan ƙare-dangi ko akasin haka, matsalar na shafarmu baki ɗaya. Ana kashe mutane ko ina,” in ji shi.
Ya jaddada cewa dole ne a haɗa kai don shawo kan matsalar.
“Shi ya sa ya zama dole mu yi aiki tare. Idan muka bar giɓi, su ne za su samu wajen shiga. Ba sa damuwa da wanda za su kashe. Waɗannan mutane mugaye ne, da yawa daga cikinsu ma suna shan miyagun ƙwayoyi.
“Saboda haka dole a kawo ƙarshen kashe-kashen nan. Manufarmu ita ce mu fuskance su kai-tsaye mu kuma dakatar da waɗannan kashe-kashen.”