Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na fada ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan.

Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne da kuma ja da baya, kuma duk da hakan ba zai sauya matsayar abokan gaba ba, ya daina kai hare-hare ko ya janye daga inda ya mamaye.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Wakilin Lebanon farar hula ya shiga cikin kwamitin amma babu abinda ya karu sai matsin lamba daga “Isra’ila” tare da Amurka da ci gaba da kai wa Lebanon hare-hare.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Wannan abinda ya faru wani Karin koma baya ne, kuma mai makon a dauki matakan da za su bai wa Lebanon karfi, sai ake daukar matakan da ba su ne su ka dace da Isra’ila ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron  Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A  Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa

Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa.

Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya  jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin dan adam a Falasdinu, yana mai kira ga masu hannun jari da su fahimci hadarin da ke tattare da ci gaba da wannan hadin gwiwa.

Wasikar ta bayyana cewa Microsoft tana bai wa sojojin Isra’ila na kasa, sama, da na ruwa bayanai masu mahimmanci duk da amincewa tsakanin kungiyoyin kare hakkin dan adam da kwararru cewa Isra’ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza.

A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar 30 ga Yuni, Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Hakkin Dan Adam, Francesca Albanese, ta nuna cewa kamfanoni sama da sittin daga sassa daban-daban sun ba da gudummawa wajen rusa  Gaza, tallafawa ayyukan gina matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, da kuma tilasta wa Falasdinawa yin hijira, ciki har da manyan kamfanonin Amurka kamar Amazon, Google, IBM, da Microsoft.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025  Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025  An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
  • Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A  Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
  •  Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
  •  An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila
  • An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya
  • MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
  • Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin  Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Yankin Gaza
  • Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza
  • Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta