Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai
Published: 4th, December 2025 GMT
Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci.
Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce lamarin tsaro ya kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.
Ya bayyana cewa wuraren haƙar ma’adinai sun zama mafakar ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ƙungiyoyin ta’addanci, inda suke tara kuɗi da shirya hare-hare.
Ya ce ’yan ta’adda suna amfani da waɗannan wurare wajen ɓoye makamai da tsara kai hare-hare.
“Dkatar da haƙar ma’adinai ne zai kawo zaman lafiya, dole mu ɗauki wannan mataki.”
Gwamnan ya ce Arewa na fuskantar matsaloli da dama; garkuwa da mutane, Boko Haram, rikice-rikicen karkara da talauci, wanda ke ƙara dagula tsaron yankin.
Ya ce dole a inganta tsaro tare da magance tushen matsalolin.
Ya kuma goyi bayan tsarin ’yan sandan jihohi, inda ya bayyana cewa bai kamata siyasa ta hana ɗaukar matakan tsaro ba.
Taron ya buƙaci Sarakunan Gargajiya da malamai su ƙara ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna.
Hakazalika, an tattauna yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da buƙatar inganta ilimi da sauran ɓangarorin tattalin arziƙi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnonin Arewa taro Tsaro haƙar ma adinai
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.
Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.
Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”
Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”
Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.
Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.