Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa.

Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa.

Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu

Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi.

Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.

Ya ce: “Da na ga irin martanin mutane bayan an ambaci sunana, na san cewa ba zan bari na gaza ba, ba zan bai wa ’yan ƙasata kunya ba. Duk abin da ya kamata mu yi, za mu yi, kuma na san da taimakon Allah za mu yi nasara.”

Musa ya ƙara da cewa abin ya ba shi mamaki ganin irin goyon bayan da aka ba shi a kafafen sada zumunta.

“Na je kafafen sada zumunta kuma abin ya ba ni mamaki ganin irin martanin mutane. Wannan yana nuna cewa mutane suna son ganin Najeriya ta zauna lafiya.”

Ya ce wasu suna cewa ’yan Najeriya ba sa son Najeriya, amma bai yadda da wannan batu ba.

“Idan wasu suna cewa ’yan Najeriya ba sa son ƙasarsu ina cewa ba haka abun yake ba, ba su san ’yan Najeriya ba.”

Ya kuma yi magana kan kashe-kashen da ake fama da su a wasu sassan ƙasar nan.

“Ko a kira shi kisan ƙare-dangi ko akasin haka, matsalar na shafarmu baki ɗaya. Ana kashe mutane ko ina,” in ji shi.

Ya jaddada cewa dole ne a haɗa kai don shawo kan matsalar.

“Shi ya sa ya zama dole mu yi aiki tare. Idan muka bar giɓi, su ne za su samu wajen shiga. Ba sa damuwa da wanda za su kashe. Waɗannan mutane mugaye ne, da yawa daga cikinsu ma suna shan miyagun ƙwayoyi.

“Saboda haka dole a kawo ƙarshen kashe-kashen nan. Manufarmu ita ce mu fuskance su kai-tsaye mu kuma dakatar da waɗannan kashe-kashen.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Janar Majalisar Dattawa Ministan tsaro Tatancewa Tsaro yan Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa

An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa.  

Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan.

Sanarwar rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, inda aka samu musayar wuta.

A yayin arangamar, biyu daga cikin jami’an sun samu munanan raunuka, aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus An kama ’yan bindiga 4 a Kano

Washegari, ɗaya daga cikin waɗanda suka ji rauni ya rasu a sakamakon tsananin raunukan da ya samu.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, Ɗahiru Muhammad, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da abokan aikinsa, yana mai tabbatar da cewa rundunar ta fara bincike na musamman domin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.

Bayan harin, rundunar ta ƙara tsaurara matakan tsaro ta hanyar yawaita sintiri da sanya ido a Aujara da maƙwabtan garuruwan domin hana sake faruwar irin wannan barazana.

Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya roƙi al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka wa binciken da ake yi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai
  • Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru
  • Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
  • DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher CG Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar