Dorinar ruwa ta kashe mutum 2, ta jikkata 6 a Gombe
Published: 5th, December 2025 GMT
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.
Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.
Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.
Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”
A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.
Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.
Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.
Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.
Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dadin Kowa Dorinar Ruwa ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha
Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta fara wani atisayen soji a yankin kudancin Iran a Tekun Fasha, wanda ya kunshi rundunonin sojoji da dama.
An yi wa atisayen lakabi da “Eightedar” (Ikon Kasa), domin girmama kwamandan da ya yi shahada Mohammad Nazeri, wani babban jami’in sojin ruwa na IRGC.
Ana gudanar da atisayen a cikin ruwan Tekun Fasha, yankin tekun Nazeat (Abu Musa, Greater Tunb, Lesser Tunb, da Tsibiran Siri), Mashigar Hormuz.
Abin lura ne cewa Mohammad Nazeri shi ne kwamandan rundunonin kwamando na rundunar sojin ruwa ta IRGC.
An san shi sosai a Iran saboda rawar da ya taka wajen kama ma’aikatan jirgin ruwan Amurka goma—maza tara da mace daya—wadanda suka shiga ruwan Iran a ranar 12 ga Janairu, 2016.
An kama su ne bayan da jirgin ruwansu ya nutse cikin ruwan Iran kusa da Tsibirin Farsi, wani sansani a tsakiyar Tekun Farisa wanda ya kasance sansanin jiragen ruwan kai hari na gaggawa na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci tun daga shekarun 1980.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro December 4, 2025 Jagora: Musulunci Ya Daukaka Mata Matukar Dauka December 3, 2025 MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI December 3, 2025 An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela December 3, 2025 Kamfanonin jiragen Sama Na Kasashen Yamma Na Neman Izinin Amurka Don Komawa Iran December 3, 2025 Kungiyar Guinness Ta Rigistan Ayyukan Bajinta Ta Duniya Ta Dakatar Da Karban Daga HKI December 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci