Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
Published: 6th, December 2025 GMT
Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar.
Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da ake dauka a kasar ba a aike wa da su zuwa fadar shugaban kasa,abinda ake aikewa fadar shi ne dokokin da majalisar dokokin kasar ta yi, domin a sake tantancewa da kuma amincewa.
Haka nan kuma sanarwar ta ce; wasu daga cikin abubuwan da ake aikewa fadar mulkin kasar sun hada da tsare-tsaren fadar shugaban kasa,amma abinda ya shafi matakan majalisar ministoci, da na kwamitin dake dakatar da kudaden ‘yan ta’adda da na kwamitin da yake sa ido akan masu wanke kudaden haram, ba a aikewa fadar gwamatin kasar.”
A karshe bayanin ya ce, fadar gwamantin kasar ba ta da wata masaniya akan matakan da aka dauka na bayyana Ansrullah da Hizbullah a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da daukar matakan hana amfani da kudadensu a cikin bankunan kasar ta Iraki.
Sanarawar da aka yi a kasqar Iraki a shekarun jiya Alhamis na cewa an hana wasu kungiyoyi da su ka hada “Isis, alka’ida, Ansarullah da kuma Hizbullah, amfani da bankunan kasar domin hada-hadar kudade, ya tayar da kura a cikin da wajen kasar. Mutane sun fito kan titutan kasar ta Iraki domin yin tir da wannan sanarwa.
Sai dai daga baya gwamantin kasar ta janye wannan sanarwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo
Shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya jagoranci taron rattaba hannu kan yarjeniyar sulhuntawa da kuma kawo karshen yakin gabacin Kongo tsakanin shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da tokwaransa na kasar Kongo Felix Tsetsekedi a birnin Washington a jiya Alhamis.
Shafinyanar gizo na labarai ‘AfricaNews” ya bayyana cewa, shuwagabannin biyu sun rattaba hannun kan wannan yarjeniyar ne a gaban kafafen yada labarai da dama a duniya. Kuma a ganin masana shugaba Trump yana neman suna ne kawai da wannan yarjeniyar.
Saboda babu tabbas kan cewa zaman lafiya zai dawo yankin Kivu na gabacin kasar Kongo. Banda haka, sun bayyana cewa hatta a dai dai lokacinda ake bikin rattaba hannu a kan yarjeniyar akwai labaran da suke tabbatar da cewa ana musayar wuta tsakanin kungiyar M23 da sojojin gwamnatin Kongo.
Banda haka kungiyar yan tawaye na M23 bata dauki shugaban kasar Rwanda a matsayin wakilanta a bikin na washingtopn ba. Sai dai akwai wani shirin zaman lafiya da take tattaunwa da gwamnatin kongo a kasar Qatar, inda suka cimma wani abu na ci gaba a tsagaita budewa juna wuta, amma bai kai ga rattaba hannu na din din din a tsakaninsu ba.
A karshen taron Trump ya ce Amurka da kasashen 2 zasu cimma wata yarjeniya ta hakar ma’adinai masu muhimmanci a kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025 Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025 An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci