‘Yan Majalisa Na Ba Da Cin Hancin Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Iya Gabatar Da Ƙudiri – Kamfani.
Published: 14th, August 2025 GMT
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.
“Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”
Dan majalisar ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ake masa na cewa, ya yi watsi da shirye-shiryen tallafawa matasa a mazabarsa, inda ya ce galibin ayyukan da yake yi suna amfanar da matasa kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp