Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a)
Published: 14th, August 2025 GMT
Miliyoyin musulmi daga ko ina sun taru a hubbaren Imam Hussain (a) da ke birnin Karbaka na kudancin kasar Iraki, don girmama limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wanda ya zama a bin buga misali a duk tsawon tarihin musulunci na nuna turjiya da kuma fada da azzalumai.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Iran ta bayyana cewa miliyoyin musul daga cikin kasar Iraki da kuma wajensa ne suke tattaki da kafa daga ko ko ta ina a cikin kasar zuwa hubbaren Imam Hussain (a). Sannan a kan hanyarsu ta zuwa Karbala akwai dubban mutane masu sa kai, suna raba ruwa da abinci da samarda wuraren hutawa da kuma magani ga wadanda suke bukata. Inda suke neman al-barkan Imam Hussain (a) da masu ziyararsa.
Imam Husain(a), a ranar ashoora ko 10 ga watan muharram na shekara ta 61 bayan hijira ko kuma 680 miladiyya tare da magoya bayansa 72 suka fuskanci rundunar azzalumin sarki na lokacin Yazid dan Mu’wiya wadanda suka kai akalla dubu 30,000. Ba tare da wani tsoro ba suka fuskanci makiyan har zuwa karshensu.
Da wannan kuma da shi da sahabbansa suka zama abin buga misali na jarunta da kuma fada da zalunci, a duniya, sannan a yanzun da kuma nan gaba sun zasu ci gaba da zama abin tsoro ga azzalumai har duniya ta dane.
Labarin ya kara da cewa daga kasar Iran kadai iraniyawa 5,291,005 ne suka tsallaka kan iyakar kasashen biyu daga kofofin 6 don halattar juyayin 40 na Imam Hussain (a) na bana a Karabala.
Sannan a cikin gida kuma an gudanar da juyayin a garuruwa kimani 500. A nan Tehran an gudanar da tattaki daga dandalin Imam Hussain (a) zuwa Haramin sha Abdulazim alhassani da ke garin Rey wajen birnin Tehran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta August 14, 2025 An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London August 14, 2025 Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar August 14, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan August 14, 2025 Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon August 14, 2025 Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: A Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama.
A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni, amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.”
Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda Amurka ta kakabawa—na iya zama mai kisa kamar tashe-tashen hankula.
Ya kara da cewa; “Tun daga shekara ta 1970, sama da mutane 500,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon takunkumin da aka sanya musu, inda akasarin wadanda abin ya shafa yara ne da kuma tsofaffi.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida August 13, 2025 Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci