Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
Published: 5th, December 2025 GMT
Wasu magidanta a garin Malam-Sidi, da ke Ƙaramar Hukumar Kwami a Jihar Gombe, sun yaba da aikin haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Gombe da UNICEF sula yi wajen rage matsalar ƙarancin abinci a tsakanin ƙananan yara.
Shirin, wanda ake kira PARSNIP, yana bai wa yara masu shekaru 6 zuwa 23 wani nau’in abinci na musamman mai suna SQ-LNS.
Wannan abincin yana ɗauke da sinadarai 24 da ke taimakawa wajen kare yara daga rashin abinci mai gina jiki da kuma bunƙasa lafiyarsu wajen girma.
A ziyarar da manema labarai suka kai, iyaye mata sun bayyana yadda shirin ya taimaka musu.
Malama Hussaina Bappayo ta ce SQ-LNS “abinci ne mai tasiri” saboda yadda ya taimaka wa yaranta sun ƙara ƙarfi da girma sosai.
Hakazalika, Malama Asmau Tela, ta ce ’yarta, wadda ta sha fama da gudawa da wasu ƙananan cututtuka, yanzu ta samy lafiya tun da ta fara cin wannan abinci.
Saboda nasarar shirin, iyaye mata da yawa suna zuwa cibiyoyin lafiya don karɓar SQ-LNS ga yaransu.
Wasu sun ce hakan ya rage musu kuɗin magani saboda yara sun daina yawan yin rashin lafiya.
Sai dai sun roƙi gwamnati da UNICEF su ƙara yawan abincin, domin yanzu ana fama da ƙarancinsa saboda buƙatar ta ƙaru.
Wasu iyayen, sun ce abincin ya taimaka sosai wajen rage yawan yara masu fama d ƙarancin abinci mai gina jiki, amma sun yi gargaɗin cewa idan ba a samun abincin, yara da yawa za su shiga hatsari.
Philomena Irene daga UNICEF ta bayyana cewa daga 2023 zuwa 2025, yara 106,248 ne suka amfana da SQ-LNS a Jihar Gombe.
Ta kuma ce sama da mata 20,347 ne suka samu horo kan kula da lafiyar uwa da jarirai, ciki har da yadda ake amfani da MUAC wajen auna girman yara.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Matashi ya rasu yayin rikici a wajen radin suna a Bauchi
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa.
Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa“Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2 ga watan Disamba, 2025,” in ji Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin arewa maso gabas.
Ya kara da cewa rashin jituwa tsakanin wasu matasa a wajen bikin ta rikide zuwa fada, lamarin da ya bar wanda abin ya shafa ya suma nan take.
An ce an garzaya da Haruna zuwa Asibitin Gwamnati na Warji, amma ya rasu a yayin da ake masa jinya.
Da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na jihar, Ahmed Wakili, ya ce yana cikin taro kuma ya yi alƙawarin dawowa da bayani, sai dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.