’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
Published: 3rd, December 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan.
Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka wuce, a wani yunƙuri na daƙile cin zarafin mata da yara a faɗin jihar.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani matashi mai shekara 23, Yusuf Garba, da ake zargi yi wa wata yarinya mai shekaru biyar fyaɗe.
An kai yarinyar asibiti sannan ana ci gaba da bincike a kan lamarin.
A wani lamari daban, an yi wa wata yarinya mai shekara 16 fyaɗe yayin da ta ke dawowa gida daga bikin Maulidi a Babbangida.
’Yan sanda sun kama mutum biyu; Audu Ado (22) da Babangida Alhaji Dawaye, inda suka amsa laifin bibiyar yarinyar har suka yi mata rauni.
Dungus, ya ce waɗanda abin ya shafa na samun kulawa, yayin da ake ci gaba da bincike a ofishin SCID kafin gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya la’anci waɗannan mummunan laifuka, inda ya bayyana cewa rundunar za ta gabatar da rahoton bincikenta kafkn gurfanar da waɗanda ake zargin.
Ya kuma shawarci iyaye, shugabannin al’umma da ƙungiyoyi su ƙara kula da yara tare da haɗa kai da ’yan sanda domin kare su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda cin zarafi fyaɗe yara
এছাড়াও পড়ুন:
MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai.
A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da tushe.
Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a BornoYa bayyana zargin a matsayin yunƙurin ɓata wa jami’ar suna.
Ya ce MAAUN na daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi sauƙin farashi a Kano, kuma tana ba da ingantaccen ilimi.
“MAAUN na ɗaya daga cikin jami’o’i masu zaman kansu masu sauƙin farashi a Kano, tana ba da ingantaccen ilimi tare da ƙayatattun gine-gine.
“Wasu jami’o’in a jihar suna cajin kuɗin makaranta ninki uku a kan na MAAUN, amma ba a jin kukan kowa game da su. Me ya sa sai MAAUN?
“Idan ɗalibi ya biya kuɗin makaranta na tsawon shekaru huɗu, me ya sa za a ga laifi idan aka nemi ya biya kuɗin yayewa a jami’a mai zaman kanta?
“Wannan ba wani sabon abu ba ne. Wannan batu gaba ɗaya na nuna wata maƙarƙashiya ce da ke nufin ɓata suna da barazana daga wanda ba a san ko waye ba da yake iƙirarin cewa yana kare muradun ɗalibai da iyaye,” in ji shi.
Ya kuma yi tambaya: “Me ya haɗa MAAUN da hukumar PCACC a kan wannan batu?”
A ƙarshe, ya shawarci wanda ya kafa jami’ar da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da ilimi mai inganci.
A gefe guda kuma, ya yaba masa saboda ƙin ƙara kuɗin makaranta duk da halin matsin tattalin arziƙi da ya sa wasu jami’o’i ƙara ƙudinsu.