Aminiya:
2025-12-05@06:15:11 GMT

Matashi ya rasu yayin rikici a wajen radin suna a Bauchi

Published: 5th, December 2025 GMT

Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa.

Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa

“Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2 ga watan Disamba, 2025,” in ji Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin arewa maso gabas.

Ya kara da cewa rashin jituwa tsakanin wasu matasa a wajen bikin ta rikide zuwa fada, lamarin da ya bar wanda abin ya shafa ya suma nan take.

An ce an garzaya da Haruna zuwa Asibitin Gwamnati na Warji, amma ya rasu a yayin da ake masa jinya.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na jihar, Ahmed Wakili, ya ce yana cikin taro kuma ya yi alƙawarin dawowa da bayani, sai dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: radin suna

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu

Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci.

Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba.

Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja

Sanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin da ke jefa jama’a cikin tsoro da kuma daƙile karatun yara a jihohi da dama.

Sanatoci da dama sun goyi bayan hukuncin kisa, inda suka bayyana cewa hakan zai zama gargaɗi ga masu aikata wannan mummunan laifi.

Wasu kuma sun nemi a hukunta bankunan da ke taimakawa wajen aikewa ko karɓar kuɗaɗen fansa, yayin da wasu suka ce ya kamata a daina yi wa ’yan ta’adda afuwa.

Majalisar ta tura ƙudirin zuwa kwamitoci na musamman domin bincike, tare da umarnin su kawo rahoto cikin makonni biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro
  • Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu
  • Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja
  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina
  • An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran