Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC
Published: 15th, August 2025 GMT
Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da kammala duk shirye-shiryen zaben ciki gurbi a kananan hukumomin Bagwai, Shanono da kuma Ghari (Kunchi) da ke Kano wanda za a gudanar a ranar Asabar.
Kwamishinan INEC a Kano, Zango Abdu, wanda ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai, ya ce an riga an raba kayan zabe masu muhimmanci da wadanda ba su da muhimmanci a kananan hukumomi da abin ya shafa.
Ya ce, “Tun kusan makonni uku da suka gabata aka riga da tura kayayyakin da ba su da muhimmanci wadanda aka tanadar wa mazabu da rumfunan zabe.
“Yanzu haka kayan zaben masu muhimmanci sun iso, kuma za a tura su kananan hukumomi yau da yamma tare da wakilan jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro.”
Ya kuma bayyana cewa an kammala horas da dukkan ma’aikatan wucin gadi kuma an tura su wuraren da za su yi aikin, yayin da jami’an tsaro karkashin kwamitin tsaro na haɗin gwiwa sun ba da tabbacin duk wasu tanade-tanade da suka kamata.
Da yake karin haske, Zango ya ce duk na’urorin BVAS wadanda za a yi amfani da su wajen tantance masu kada kuri’a su ma an tanade su tare da tabbatar da nagartarsu.
Ya jaddada kudirin INEC na gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci, inda ya ce hukumar za ta sanar da wanda ya yi nasara ne kawai bisa kuri’un da aka kada.
“Babbar damuwarmu a yanzu ita ce ’yan siyasa. Amma dai su ma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, sun kuma shaida mana za su yi zabe cikin lumana. Saboda kwanciyar hankali ne kawai zai ba ’yan kasa ’yancin zaben shugabanninsu,” in ji shi.
Dangane da yadda za a tattara sakamako, Zango ya ce za a bayyana sakamakon akwatuna a duk rumfunan zabe kafin a kai shi cibiyoyin tattarawa na mazabu.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Yunin da ya gabata ne INEC ta ayyana 16 ga watan Agustan bana, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomin na Kano.
Za a gudanar da zaben ne sakamakon rasuwar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bagwai da Shonono, Halilu Ibrahim Kundila na jam’iyyar APC, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar 6 ga watan Afrilun 2024.
Sai dai kuma za a gudanar da zaben cike gurbin ne a Karamar Hukumar Ghari — wadda a baya ake kira Kunc— a rumfunan zabe 10 da masu kada kuria 5200 bisa umarnin kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano za a gudanar a gudanar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da ci gaba da ba kungiyar goyon baya, amma kuma wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yan wasan 3SC da aka jikkata tareda raunuka a jikinsu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA