Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15
Published: 5th, December 2025 GMT
Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na Naira tiriliyan 12.8 daga watan Agustan 2024 zuwa Oktoba 2025, bisa ga bayanan da Hukumar Kula da Rarraba Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fitar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ƙoƙarin ƙara samar da man fetur a cikin gida, duk kuma da aikin da matatar Dangote ke yi.
Bisa amfani da matsakaicin farashin lita ɗaya na ₦829.77, an ƙididdige jimillar lita 15,435,000,000 da aka shigo da su a wannan lokaci.
Bincike ya nuna cewa mafi yawan shigo da man fetur ya kasance ne a watan Satumban 2024 lokacin da ba a samar da man ba a cikin gida, inda aka shigo da lita biliyan 1.52, sai Agusta 2024 da lita biliyan 1.38, sannan Disamba 2024 da lita biliyan 1.31.
A Oktoba 2025, an shigo da lita biliyan 1.17, sai Nuwamba da lita biliyan 1.12. Amma a Janairu 2025, adadin ya ragu sosai zuwa lita miliyan 765.7, kafin ya ɗan ƙaru zuwa lita miliyan 770 a Fabrairu, sannan miliyan 889.7 a Maris.
A Afrilu, an samu lita miliyan 861, sai kuma Mayu da ya haura zuwa 1.19 biliyan, kafin ya ragu zuwa 978 miliyan a Yuni, sannan ya ƙaru zuwa 1.11 biliyan a Yuli, kafin ya sauka zuwa 818.4 miliyan a Agusta, 663 miliyan a Satumba, da 855.6 miliyan a Oktoba.
Samarwa da mai a cikin gidaA ɓangaren samarwa a cikin gida, jimillar lita biliyan 7.2 aka samar a wannan lokaci, dukkansu daga matatar man Dangote.
Bayanan sun nuna cewa ba a samu gudunmawar samarwa daga cikin gida ba a watan Agusta 2024, amma a Satumba 2024, Dangote ya samar da lita miliyan 102, wanda ya ƙaru zuwa miliyan 300.7 a Oktoba 2024, sannan miliyan 558 a Nuwamba 2024.
Bayanan sun nuna cewa har yanzu ƙasar na dogaro sosai da shigo da man fetur duk da ƙoƙarin kawo ƙarshen shigo da shi domin tallafa wa samarwa a cikin gida.
Dangote ya sha bayyana cewa matatar man shi karfin tace ganga 650,000 a kullum na iya wadatar da Najeriya.
Sai dai masana a fannin sun ce haramta shigo da man fetur zai iya haifar da babakere a fannin, wanda suka ce bai dace da kasuwar man fetur ba a kasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: da lita biliyan 1 lita miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.
Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar.
“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.
A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.
Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.
Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.