Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump
Published: 5th, December 2025 GMT
A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa kasar za ta dauki hutu daga halartar tarukan G20 yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke jagorantar kungiyar a karkashin tsarin karba-karba, bayan da gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ba za ta gayyaci Afirka ta Kudu a taro mai zuwa ba.
Amurka ta karbi shugabancin G20 na karba-karba a makon da ya gabata, bayan kauracewa taron da Shugaba Cyril Ramaphosa ya shirya a Johannesburg.
“A wannan lokacin a shekara mai zuwa, Birtaniya za ta karbi shugabancin G20. Za mu iya shiga cikin batutuwan da suka shafi duniya,” in ji mai magana da yawun Ramaphosa, Vincent Magwenya.
“A yanzu haka, za mu dakatar da shirye-shiryen kasuwanci har sai lokacin da muka sake dawowa a cikin dukkanin harkokin kungiyar,” in ji shi a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tabbatar a ranar Laraba cewa “Afirka ta Kudu ba za ta iya shiga cikin duk wani taron G20 a shekara mai zuwa ba,” yana mai cewa “Shugaba Trump da Amurka ba za su mika goron gayyata ga gwamnatin Afirka ta Kudu don shiga cikin tarukan G20 a lokacin shugabancinmu ba.” Inji shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025 Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025 An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota
Rahotanni daga Ramallah sun ce a kalla sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila 3 ne su ka jikkata sanadiyyar taka su da mota da wani Bapalasdine ya yi , a yau Talata.
Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ambaci cewa; Wani Bafalasdine ya soka wa dan shaayoniya wuka da aka dauke shi zuwa asibiti domin karbar magani.”
Majiyar ta ce da akwai sojojin a wurin da aka kai hari, don haka su ka bude wuta akan maharin Bapalasdine.”
Su kuwa jaridun Falasdinawa a Ramallah sun ce wanda ya kai harin na Yau Talata ya yi shahada bayan da sojojin mamaya su ka bude masa wuta.
A gefe daya, kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinawa sun yi maraba da harin akan ‘yan sahayoniya a kusa da Ramallah, tare da bayyana shi a matsayin mayar da martani ga laifukan yakin da suke tafkawa akan al’ummar Falasdinu.
Kungiyar Hamas da ta fitar da bayani ta yi jinjina akan ci gaban gwagwarmaya a yammacin kogin Jordan, duk da matsin lamba da takurawar da sojojin mamaya suke yi.
Haka kuma ta ce; jinanen shahidai za su ci gaba da zama masu karfafa gwiwar mutane domin ci gaba da yin gwgawarmaya.
Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta bayyana harin da cewa, Na jarunta ne’ kuma mayar da martani ne akan laifukan ‘yan mamaya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci