Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza
Published: 4th, December 2025 GMT
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya.
“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da gaske suna jagoranta, ba da izini, ɗaukar nauyi, goyon baya, ko aiwatar da take hakkin ’yancin yin addini. Wadannan manufofin biza sun shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zaluntar jama’a saboda addininsu,” in ji Rubio.
Maganganun Rubio sun zo ne kwana guda bayan ’yan majalisar Amurka sun gudanar da taron jin ra’ayi a Washington tare da masana kan ’yancin yin addini da dangantakar ƙasashen waje domin tattauna ƙaruwa da tashin hankali a Najeriya da kuma “zaluncin da aka fi karkata ga Kiristoci.”
Taron majalisar ya kasance wani ɓangare na bincike da ake ci gaba da yi kan batun, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Donald Trump.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zargin kisan Kiristoci
এছাড়াও পড়ুন:
Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita.
Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba an mika shi ga wani jami’in Amurka.
Bayan kauracewa taron shugabannin G20 da aka gudanar a Johannesburg a ranar 22-23 ga Nuwamba a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu, Trump ya maimaita ikirarinsa na cewa gwamnatin kasar mai rinjayen bakaken fata tana nuna wariya ga tsirarun fararen fata.
A jawabinsa, Ramaphosa ya kira zarge-zargen Trump na kisan kare dangi da kwace filaye daga fararen fata da cewa ba gaskiya ba ne, zargui ne maras hujja balantana makama, yana mai sake jaddada cewa “Afirka ta Kudu cikakkiyar memba ce da aka kafa G20 tare da ita.”
Rikicin da ke tsakanin Washington da Pretoria ya fara kamari ne a farkon 2025. A ranar 14 ga Maris, Amurka ta kori jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, bayan ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da abokansa da haɓaka ajandar duniya ta masu ra’ayin wariyar launin fata
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci