Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha
Published: 5th, December 2025 GMT
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghaei ya yi Allah wadai da kakkausar murya da sanarwar bayan taron shugabannin Kasashen Yankin Tekun Farisa (GCC) wanda suka fitar game da tsibiran Iran guda uku.
Baghhaei ya nuna takaici kan dagewar da kungiyar GCC ta yi kan maimaita ikirari maras tushe na Hadaddiyar Daular Larabawa game da tsibiran Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb na Iran.
Ya yi Allah wadai da ikirarin da ke cikin sanarwar karshe ta taron kolin GCC karo na 46 game da wadannan tsibirai na kasar Iran, yana mai jaddada cewa Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb muhimmin bangare ne na yankin Iran kuma duk wani ikirari sabanin hakan ba shi da inganci, kuma a bayyane yake ya saba wa ka’idar girmama mutuncin yankin kasashe da kyakkyawar makwabtaka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ya jaddada manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kyakkyawar maƙwabtaka da haɗin gwiwa da ƙasashen da ke makwabtaka da ita don ƙarfafa dangantaka da kuma kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
Ya yi kira ga Hadaddiyar Daular Larabawa da Majalisar Haɗin Kan Kasashen Gulf da su guji ɗaukar matakai masu tayar da hankali waɗanda suka saɓa wa kyakkyawar alaƙar maƙwabta da Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025 Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025 An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe
Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku ta duniya (IMO) karo na 34.
A wata wasika da ta aike wa Sakatare Janar na IMO Arsenio Dominguez, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kungiyar da ke Landan a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa game da yadd Isra’ila kesarrafa hukumar IMO don manufofinta.
Wasikar ta jaddada cewa wannan dabi’a tana wargaza kwarewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a harkokin teku.
Tawagar Iran ta kara da cewa wadannan zarge-zargen marasa tushe wani bangare ne na wani tsari da Isra’ila ke kokarin lalata dokokin kasa da kasa, raunana hanyoyin da suka shafi bangarori daban-daban, da kuma kawo cikas ga ayyukan tsarin shugabanci na duniya.
A cikin wannan wasikar, Tehran ta bayyana wadannan zarge-zargen a matsayin “masu adawa” da “masu tayar da hankali,” tana ganin su a matsayin wani yunkuri na karkatar da hankalin kasashe mambobin IMO da keta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi akai-akai.
Wasikar ta kuma nanata ayyukan Isra’ila da suka sanya tsaron teku da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa cikin hadari, tana mai ambaton kame jiragen ruwan agaji na duniya da ke kan hanyarsu ta zuwa Gaza da sojojin Isra’ila ke yi yayin da jiragen ruwan ke yankin Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro December 4, 2025 Jagora: Musulunci Ya Daukaka Mata Matukar Dauka December 3, 2025 MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI December 3, 2025 An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela December 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci