’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano
Published: 6th, December 2025 GMT
’Yan sanda sun kama tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Rahotanni sun nuna cewar wasu ’yan sanda ɗauke makamai ne suka kama shi a ofishinsa da ke Kano, bayan tafka jayayya a ranar Juma’a.
Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026 Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — ZulumWaɗanda lamarin ya faru a kan idonsu, sun ce manyan motocin ’yan sanda cike da jami’an da ke ɗauke da makamai ne suka dira ofishinsa da ke kan titin zuwa Zariya.
Sun gargaɗi mutane da kada kowa ya kusanci ofishin, inda suka yi barazanar buɗe wa duk wanda ya yi yunƙurin tsoma baki a lamarin wuta.
Muhuyi, ya nemi jami’an su nuna masa takardar kama shi ko su bayyana dalilin kama shi.
Sai dai jami’an sun ƙi bayyana komai, face cewar umarni aka ba su daga Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ƙasa da ke Abuja.
Lauya Ridwan Zakariyya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan tafka jayayya, daga bisani an kai Muhuyi hedikwatar ’yan sanda ta Kano da ke Bompai.
Ya ce jami’an sun ce su wani rukuni ne na musamman na Sufeto Janar na ’Yan Sanda da aka aiko daga Abuja.
Zakariyya, ya ƙara da cewa jami’an sun yi yunƙurin ƙwace wayar Muhuyi tare da yin barazanar harbi.
Wannan shi ne karo na biyu da ake kama Muhuyi a shekarar 2025.
A farkon watan Janairu, rundunar IGP Monitoring Unit ta kama shi kan almundahanar wasu kuɗaɗe da ake zargin suna da alaƙa da wani jigo na jam’iyyar APC, amma daga baya aka sake shi.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ci tura, domin bai amsa wayarsa ba, zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Barazana harbi hedikwata Lauya zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele.
Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan TsaroSanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take.
Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya jinkirta irin wannan buƙata ba a wannan lokaci mai muhimmanci, domin ta shafi muhimman abubuwan da suka shafi ƙasar.
A ranar Talat ace Tinubu ya aike da sunan Christopher gaban majalisar domin amincewa bayan murabus din tsohon Ministan, Muhammad Bdaru Abubakar.
Kafin nadin nasa dai, Christopher shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya da Tinubu ya sauke tare da ragowar manyan hafsoshi a kwanakin baya.