Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa
Published: 4th, December 2025 GMT
Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa da nufin sayarwa ya kasa samun mai saye kusan watanni biyar bayan ɗora shi a dandalin sayar da jiragen sama na duniya.
A sakamakon haka, tuni ma kamfanin dillancin da ke kula da sayar da jirgin samfurin Boeing 737-700 Business Jet ya janye jerin sayar da shi daga shafinsa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa jirgin da a baya aka saka a shafin kamfanin, yanzu an cire shi daga kai.
A cikin wata amsa ga sakon imel, Laurie Barringer wanda shi ne Manajan Binciken Kasuwa na JetHQ, ya tabbatar da cewa kamfanin ya cire jirgin daga jerin sayarwa, inda ya ce a nemi karin bayani daga Gwamnatin Najeriya.
“Mun gode da sakonku. Ba mu da jerin Boeing yanzu a shafinmu. Sai dai ku tuntubi Gwamnatin Najeriya don samun bayani kan abin da ya faru da jirgin. Na gode da lokacinku — Laurie Barringer, Manajan Binciken Kasuwanci, JetHQ,” in ji sakon.
Hadimin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa, Ismail Garba, ya yi alƙawarin bayar da amsa amma bai yi hakan ba har bayan kwanaki da dama.
Mataimakin Manajan Binciken Kasuwa na JetHQ, Marinell Nuevo, ya tabbatar da cewa jirgin “yana nan a kasuwa” amma ya tura karin tambayoyi zuwa Barringer.
Daga baya Barringer ya bayyana cewa kamfanin ba zai bayyana wasu bayanai fiye da kasancewar jirgin a kasuwa ba, yana mai cewa irin wannan bayani na sirri ne.
“Ba ma bayar da irin wadannan bayanan ga kowa sai ga mamallakin jirgin kai tsaye. Ana ɗaukar wannan bayani a matsayin sirri. Ina fatan za ku fahimta. Abin kawai da za mu iya bayarwa shi ne cewa jirgin yana nan a kasuwa,” in ji Barringer.
Kafin a cire shi daga jerin sayarwa, bayanai sun nuna cewa an yi wa jirgin gyare-gyare a watan Yuli 2024, ciki har da gyaran kujerun ajin farko, sauya kafet na cikin jirgi da sauran kananan gyare-gyare.
A cewar aircraftcostcalculator.com, jirgin Boeing 737 BBJ da aka taɓa amfani da shi darajarsa a kasuwa ta kai kusan $56m, kwatankwacin Naira sama da Naira biliyan 82.
An sayi jirgin a shekarar 2005 a kan $43m a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, kuma ya kasance wani jerin jiragen Fadar Shugaban Ƙasa.
A watan Yuli 2025, gwamnatin Tinubu ta sanar da shirin sayar da jirgin a matsayin wani ɓangare na dabarar rage kashe kuɗi da daidaita yawan jiragen, a yayin da jama’a ke ƙara sa ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗade.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fadar Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja.
Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba.
CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a KatsinaKawo yanzu dak ba a san musababbin tashin gobarar ba.
Sai dai wasu rahotanni na cewa gobarar na iya farawa ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda wani lokacin wayoyin wuta na faɗowa kan rumfunan kasuwa.
’Yan kasuwa da mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar, amma ta yaɗo cikin sauri saboda katako da sauran kayayyakin gini na da saurin kamawa da wuta.
Wasu gine-gine da ke kusa da kasuwar sun lalace, lamarin da ya tilasta wa jama’a gudu domin tsira da rayukansu.
Daga baya jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya sun isa wajen tare da kashe wutar.
Mutanen da abin ya shafa sun roƙi gwamnati ta taimaka musu, domin sun rasa duk abin da suka dogaro da shi wajen kula da rayuwarsu.