Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi
Published: 14th, August 2025 GMT
Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi.
Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja.
“Shugaban ƙasa [Tinubu] da muƙarrabansa sun yi ƙoƙari sosai wajen daidaita tattalin arzikin Nijeriya.
“Wannan namijin ƙoƙarin na Tinubu abu ne da ya zama dole a yaba masa da ba kowa zai iya yi ba.
Tsohuwar Ministar Kuɗin ta Nijeriyar ta ƙara da cewa, yanzu aikin da ke gaban shugaban shi ne ya haɓaka tattalin arzikin ta yadda kowane ɗan ƙasa zai samu na kansa cikin sauƙi.
Ngozi ta yi kira ga gwamnatin Nijeriyar ta tanadi hanyoyi da dabarun sauƙaƙa wa talakawan ƙasar da ke fama da raɗaɗin tsare-tsaren tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Duk da ta yaba wa shugaban ƙasar kan tsare-tsarensa na tattalin arziki da suka haɗa da cire tallafin man fetur, tsohuwar Ministar Kuɗin ta ce dole ne gwamnatin ta tallafa wa ’yan ƙasar.
Iweala ta ce “muna ganin shugaban ƙasar da gwamnatinsa sun daidaita tattalin arzikin Najeriya, amma duk da haka sai sun tabbatar da ɗorewar sauyin mai kyau da aka samu zuwa yanzu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tattalin Arziki daidaita tattalin arzikin
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA