2025-10-14@19:51:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10178

«da ake zargin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A yayin wani zaman aiki na bunkasa samar da abinci, shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya yi kira ga al’ummar kasar da su shiga cikin ” atisayen tsaron farar hula na kasa ” a ranar Asabar mai zuwa. Atisayen na da nufin “shirya mutane ga bala’o’i ko duk wani rikici na makami da ka iya faruwa,” yayin da yake tabbatar da hadin kan al’ummar Colombia da Venezuela. Maduro ya ce, “Mutanen Colombia da Venezuela na da hadin kai, idan da kun san adadin sakon da na samu daga Colombia, na samu sakonni daga maza da mata na jama’ar kasar domin nuna goyon baya ga Venezuela.” Ya kara da cewa, “Na samu har ma da sakonni daga mazajen da suka gaya...
    Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma wasu lamuran da suka shafi al’ada a fadin kasar, wanda ya kai kaso 15. Misali, yankin Arewa Maso Gabas, kacal irin wadannan hare-haren babu kakkautawa da mahara ke kai wa ya dakatar da yara miliyan biyu daga zuwa Makaranta inda hare-haren suka lalata gine-genen Makarantu da dama hakan kuma ya kara haifar da karancin Malaman. Malamai 915,913 kacal ne a matakin karatun Firamare ke koyar...
    Dakarun Yaman sun sanar da cewa, sun kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Falasdinawa 2” mai dauke da kawuna da dama, kan wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a yankin Jaffa da ta mamaye. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ya karanta, rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da cewa farmakin ya cimma manufofinta tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Lod (Filin jirgin sama na Ben Gurion). A gefe guda kuma, Dakarun Yaman sun jaddada cewa, dakarun tsaron sama sun kame wasu jerin hare-haren Isra’ila da makamai masu linzami na sama zuwa sama, lamarin da ya dakile wani...
    Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar. An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba.   Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki. A wasu lokuta masu tsanani, cutar na iya kai mutum asibiti ko ta yi barazana ga rayuwa, musamman ga yara ƙanana, mata masu ciki, tsofaffi, da masu raunin garkuwar jiki. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC DAGA LARABA:...
    Gwamna Nasir Idris ya ba da umarnin gaggauta rufe wurin haƙar zinare da ke Mararrabar Birnin Yauri a Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi. Yayin da yake ba da wannan umarnin, ya ce an dauki matakin ne domin kawar da matsalar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma daƙile duk wata barazana da za kawo tarnaƙi a cikin al’umma. Majalisar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi Naira biliyan 75 Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a Filato Aminiya ta ruwaito cewa, ziyarar bazata da gwamnan ya kai cibiyar haƙar zinaren a ranar Alhamis, na zuwa ne bayan rikicin da aka yi tsakanin mazauna yankin da kuma jami’an gwamnatin tarayya da ke...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na Naira biliyan 75 na kasafin kuɗin jihar da ƙananan hukumomi. An amince da kasafin kuɗin ya zama doka ne a yayin zaman majalisar wanda mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Sani Isiya ya jagoranta. Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a Filato An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar wanda Hon Ibrahim Hamza Adamu ya gabatar. Ƙarin kasafin kuɗin da aka amince da shi ya ƙunshi Naira biliyan 58 na Gwamnatin Jiha da kuma Naira biliyan 17 na Ƙananan Hukumomi 27, wanda ya ƙunshi kashe kuɗaɗe na yau da...
    Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba, kamar dai yadda muka gani a baya. Don haka, a wannan gaba da ake ta samun karin sakamakon kyautata muamala da gudanar da shawarwari, kamata ya yi bangaren Amurka ya kauracewa kakaba shingen cinikayya, wanda ka iya gurgunta nasarorin da aka riga aka cimma. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaie yayi tir da shugaban kasar Amurka Donal Trump bayan ya bayyana cewa Amurka tana son ta sake shiga tattaunawa da Iran kan shirinta na makamashin nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaie yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa shugaban ya yi wannan tayin a farkon shigabarsa fadar white house kuma munga matijar wanda itace yakin kwanaki 12 a cikin watan yunin da yagabata. A jawabinsa a babban zauren MDD shugaba Trump ya bayyana  yadda jiragen yakin kasar samfurin B2 suka sauke boma-bomai har paund 30,000 a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar a Natanz da fordo da kuma Esfahan da nufin wargaza su....
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 9:30 na safe. An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni a 2027 — Atiku Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa, wanda ake zargin ya yi zazzafar taƙaddama da kakansa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75 da kuma kakarsa, Hadiza Tasidi...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattaunawa da kuma diblomasiyya basa da amfani idan har kasashen E3 sun maida takunkuman tattalin arziki a kan kasarsa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Swiss  Karin Keller-Sutter a gefen taron babban zauren MDD karo na 80. Ya ce mata ‘muna maraba da tattaunawa ko diblomasiyya amma idan kasashe E3 suka maida takunkuman MDD a kan kasar mu tattaunawa da diblomasiyya basu da amfani a wajemmu’. Wadannan kasashen turai 3 ko traiko dai sun tada baton maido da takunkuman tattalin arziki na MDD ne a cikin watan Augustan da ya gabata, bayan sun ga Amurka da HKI sun...
    Daga nan sai ya jaddada aniyar Sin, ta ci gaba da goyon bayan matsayi da ikon MDD, tare da mara baya ga sassan kasa da kasa wajen cimma nasarar amfani da dandalin MDDr a matsayin fagen karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da tsare-tsare da aiwatar da matakai yadda ya kamata.   Haka kuma, a yayin zantawarsa da shugabar taron MDD karo 80 Annalena Baerbock, a gefen babban taron muhawarar majalissar dake gudana a halin yanzu, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin na goyon bayan gina MDD mai karin inganci da hangen nesa, ta hanyar gudanar da sauye-sauyen kyautata karko da nagartar ayyukanta. Ya kuma bayyana kakkarfan goyon bayan Sin ga ikon MDD, da rawar da take takawa a...
    Idan aka zo batun “salon zamanantarwa irin na kasar Sin”, za ku so ku ji shin: Takamaime wace irin hanya ce wannan? Me ya bambanta ta da zamanantarwa irin ta sauran kasashe a duniya? A gaskiya dai, fahimtar salon zamanantarwa irin na Sin babu sarkakiya a ciki. Tana nan lullube a cikin harkokin yau da kullum na jama’ar kasar Sin, da ma alakar da ke tsakanin wannan kasar da sassan duniya. Salon zamanantarwa irin na kasar Sin wani tsarin zamanantarwa ne na dimbin jama’a, da zamanantar da samun wadata ta bai-daya domin daukacin al’umma, da zamanantar da tsarin dunkulewar kayayyaki da ruhin wayewar kai, da zamanantar da zaman lumana tsakanin mutum da dabi’ar halitta, da kuma zamanantar da bin hanyar...
    Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United. Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya. Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029. Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
    Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
    Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
    A wani labarin kuma, Sakataren Ilimi na ƙananan hukumomi, ya gabatar da ma’aikata 24 na bogi domin tantancewa, abin da ya nuna girman almundahanar da ake yi a ɓangare ilimi. Gwamna Umaru Dikko Radda ya umarci a hanzarta fitar da takardar da su domin aiwatar da shawarwarin kwamitin. Ya ce gyare-gyaren za su taimaka wajen mayar da kuɗaɗe ga ci gaban ƙananan hukumomi tare da kare jihar daga almundahana. Yanzu haka, ƙananan hukumomi sun ajiye Naira miliyan 500, kuma ana sa ran adadin zai kai Naira biliyan 5.7 idan aka dakatar da biyan ma’aikatan bogi. Gwamnan ya jaddada cewa duk da gargaɗin cewa irin wannan gyara na iya cutar da siyasarsa, jihar ta fi buƙatar gaskiya da tsari wajen kashe...
    Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da babban tsarin ban ruwa a wurin, har ya mai da sassan hamada su zama gonaki. A cikin hamadar da ke gundumar Qiemo, ana ta kara samun dausayi, inda masarar da malam Li Wenbin ya shuka ta kusan nuna. A cikin shekaru goma da suka gabata, karuwar gonaki a jihar Xinjiang ta kai fiye da muraba’in kilomita 8000, wanda ya sa jihar zamanto yankin da ya...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shawarci matasa da ’yan siyasa masu tasowa da su fahimci cewa harkar siyasa ba ta tafiya da rowa, illa juriya da sadaukarwa da biyayya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake rantsar da sabon Alƙalin alƙalai na jihar (Grand Khadi) tare da wasu Masu Ba da Shawara na Musamman, Memba na dindindin a hukumar SUBEB, da kuma Sabbin sakararorin dindindin guda 13 a wani taro da aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu. An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri A jawabinsa, Gwamna Buni ya ce matasa da...
    An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488 Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun...
    Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali. Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD Shugaban ya ƙara da cewa, duk da cewar sakamakon yanayin yadda lamurran rayuwa suke ga al’umma wadda ya kai da ba su samu damar cika yawan kujerun da aka bai wa Jihar ba, amma duk da haka kusan mahajjata 1098 ne suka...
    Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci. Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi. Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa. A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan...
    Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 na kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kai, a babban zauren taron jama’a na Xinjiang. Kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin. Memba dindindin na ofishin siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ko CPPCC, kuma shugaban tawagar kwamitin kolin jam’iyyar Wang Huning, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Kazalika, memba dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Cai Qi shi ma ya halarci taron. A cikin jawabinsa, Wang Huning ya bayyana cewa, kwamitin kolin JKS a karkashin jagorancin Xi Jinping, ya ci gaba da dubawa, da...
    Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala. Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana da takardun bogi, takardun daukar aiki na ƙarya, wasu kuma suka ki bayyana a gaban kwamitin. Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD FBI ta sanya la’adar N15m kan dan Najeriyar da take nema ruwa a jallo An gabatar da rahoton a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar, inda manyan jami’an gwamnati da mambobin kwamitin tantancewa suka halarta. A cewar rahoton,...
    Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985.   A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 80, Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Jawabinsa ya ƙunshi kira ga gyare-gyare, adalci a harkokin tattalin arziki, da goyon bayan zaman lafiya da haɗin kai na duniya. Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Ga muhimman batutuwa bakwai da Najeriya ta jaddada a yayin jawabinta a wannan taron: Bai wa Najeriya kujera a Kwamitin Tsaro na majalisar Najeriya ta buƙaci samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro/Sulhu na majalisar, tana mai cewa rashin wakilcin Afirka a matakin yanke shawara na duniya yana rage...
    A wajen ɗalibin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya. A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin zanen fuska. Kamfanin Indomie ne zai tallafa wa ɗalibin domin gwada bajintarsa wajen shiga kundin Guinness World Record. Burinsa shi ne zana fuskar mutane 12 ko sama da haka a cikin minti uku da kuma fuskar mutane 220 ko sama da hakan cikin sa’a guda, inda yake ƙoƙarin ƙwace kambun da Emilia Zakonnova, wadda ke riƙe da shi, wadda ta zana fuskar mutane 12 cikin...
    Hukumar Leken Asiri ta Iran ta fitar da wasu bayanai na sirri da suke da alaka da ayyukan cibiyar makaman Nukiliyar HKI. Bayanan da ma’aikatar leken asirin ta Iran ta fitar wadanda aka watsa a kafafen watsa labarun kasar, sun kuma kunshi ayyukan da wasu masana a fagen Nukiliya na turai suke gudanarwa.  Majiyar tsaron ta Iran ta kuma ce bayanan da ta samu suna kunshe a cikin miliyoyin shafukan takardu, sun kuma same su ne ta hanyar wasu cibiyoyi na ‘yan sahayoniya da kuma cibiyarta ta Nukiliya.”  Ministan hukumar leken asirin ta Iran ya ce, an shigo da miliyoyin takardun masu kunshe da wadannan bayanan zuwa cikin Iran, suna kuma kunshe da bayanai masu kima. Share 0 0 votes...
    Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila tana shirin kai musu hari. Jiragen ruwan  dake son kawo karshen killace sun kai  50, suna kuma dauke da kayan agaji HKI ta aike da jiragen sama marasa matuki wadanda suke yin shawagi na tsokana a samansu da kuma watsa musu wasu sanadarori masu guba. A jiya da dare jiragen ruwan su ka  bar gabar ruwan ‘ Girka su ka shiga iyakokin ruwan kasa da kasa da zai nausa ya nufi gabar ruwan Gaza. A gefe daya, ministan tsaron kasar Italiya  Guido Crosetto ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da jirgin yaki na biyu...
    Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Muhamamd Islami ya bayyana cewa nan gaba kadan Iran za ta rika samar da megawatti 5000 na wutar lantarki daga tashar Nukiliya dake Bushehr. Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ ya ambato shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran yana cewa; Ba da jimawa ba, tashar ta Nukilkiya dake Bushehr za ta zama cikin Shirin da za ta iya bayar da wutar lantarki mai karfin megawatti 5000, tare da cewa, yin hakan yana a karkashin tsarin da ake da shi akan Shirin Nukiliya a Iran. Har ila yau ya kara da cewa; A lokacin ziyarar da mu ka kai zuwa kasar Rasha, mun yi tattaunawa akan aiki tare a fagen fasahar Nukiliya. Bugu da kari ya...
    Indomie, a matsayin jigo da ta daɗe wajen nasarar samar da abinci mai gina jiki ga al’umma, tana alfahari da tallafawa wannan yunƙuri na kafa tarihi na Collins. Shekaru da dama, Indomie ta tallafa wa shirye-shiryen tallafawa a fannin ƙirƙira da ilimi da sana’o’i ga matasa. Tallafawa Collins, wata alamar nasara ce da take nuna ƙoƙarin Indomie na isar da saƙo mai ƙarfi ga jama’a wajen cimma manyan burika da muradan rayuwa da suke bukatar samun goyon baya da ƙarfafa guiwa. Shigar cikin wannan al’amari wata babbar alama ce da take tabbatar da cewa wannan taron na tarihi ya sami haske da karramawa kamar yadda ya dace, taro ne da yake ƙarfafa wa matasan Nijeriya guiwa domin su samu nasarar...
    Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran. Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama. ’Yan bindiga sun harbi wani saboda rashin isassun kuɗi a asusunsa Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki A cewar sanarwa da aka wallafa a shafin FBI a ranar Laraba, ana tuhumar shi da laifukan zamba a banki, zamba da takardun shaida, laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun shekarar 2001. Adediran, mai shekaru 56, yana amfani da sunaye...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓar Naira miliyan biyu a hannun wani mutum, sannan suka harbe shi saboda kuɗin ba su kai adadin da suke nema ba. Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka mai shekaru 25, Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma. Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas Sun harbi mutumin a ƙafa bayan sun gano ba shi da kuɗi sosai a asusun bankinsa. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce sun samu kiran gaggawa cewa an yi garkuwa da wani mutum a gidansa da ke Ogwashi-Uku. ’Yan sanda sun bi sahun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ƴansandan Jihar Delta ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da garkuwa da wani matashi, inda suka karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan biyu (₦2m) amma duk da haka suka harbe shi saboda rashin isassun kuɗi a asusun bankinsa. Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka (25), da Uche Okechukwu da Somto Chukwuma, waɗanda suka yi garkuwa da wanda abin ya shafa daga gidansa da ke Ogwashi-Uku. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana cewa an gano wanda aka sace a cikin daji da ke yankin tare da raunin harbin bindiga a ƙafarsa. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da...
    Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata. A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da...
    Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata. A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da...
    Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata. A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da...
    Shugaban kasar Iran masud pezishkiyan ya gana da shugaban kasar faransa Emmanuel Macron a gefe taron majalisar dinkin duniya  kuma sun mayar da hankali kan matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na sake dawo da takunkumi majalisar dinkin duniya da kuma matsayarta kan shirinta na nukiliya. Taro ya guda ne adaidai lokacin da ake fuskantar zaman tankiya tsakanin iran da kasashen faransa, jamus,  da kasar birtaniya inda suka hada kai da Amurka wajen sake dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya akan Iran, wanda hakan karya alkawari ne a bangaren diplomasiya, Kasar Iran ta jaddada cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne ,kana ta zargi kasashen turai da siyasantar da lamarin , Iran na kallon hadin kai tsakanin Amurka...
    Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda zai iya barin Bayern Munich a bazara mai zuwa.(Star), external Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce Kane, wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din, ‘za su karbe shi da hannu biyu” idan ya dawo , amma ba ya tsammanin dan wasan zai bar kungiyarsa ta Jamus a yanzu.(Sky Sports), external Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, ya soma shirin barin Manchester United a watan Janairu domin neman wata kungiyar kwallon kafa .Ya samu wata kungiya da ta nemi a ba ta shi aro sai dai Man U ta yi watsi da tayin a bazara . (Mirror), external Bayern Munich na tunanin sabunta kwantiragin dan wasan Faransa Michael Olise, mai...
    Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027. Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da suka ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace shekara. Wannan sabuwar hanyar riga-kafin za ta bai wa miliyoyin mutane damar ci gaba da rayuwa da kuma kauce wa haɗarin kamuwa da cutar HIV. Za a riƙa samar da maganin mai rahusa a Indiya, sannan kuma za a watsa shi a duniya ta hannun gamayyar wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya a ƙasashe guda 120.
    A ƙarshe, Shugaban ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka kamar cire tallafin mai da sauya tsarin kuɗi, duk duk sanya shan wahala amma wajibi ne domin tabbatar da cigaba. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam, da haɗin kai da zaman lafiya, inda ya gargaɗi duniya da cewa babu wanda zai tsira sai idan duk mun tsira tare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta fannin kiwon lafiya a jihar.   Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idris Mohamed Gobir ya bayyana cewa yayin da ya karbi bakuncin sabuwar wakiliyar Unicef ​​ta kasa Mrs Wafaa Sa’eed da ta kai ziyarar fahimtar da jihar.   Alhaji Idris Gobir ya ce a kan haka ne bangaren ke samun mafi yawan kasafin kudi tun hawan gwamnatin mai ci.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai (Mataimakin Gwamnan) Garba Muhammed ya raba wa manema labarai, Mataimakin Gwamnan ya ce manufar ita ce a tabbatar da cewa mutane suna samun ayyukan kiwon lafiya cikin sauki.   Ya kuma nuna jin dadinsa da tallafin daban-daban da gwamnatin...
    Akalla yara miliyan 4.8 ne ake shirin yi wa allurar rigakafin cutar kyanda da cutar shan inna a jihar Katsina a wani bangare na shirin allurar riga-kafi da aka shirya yi a wata mai zuwa.   Shugabar ofishin kula da kananan yara ta UNICEF, Rahama Farah, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Katsina a wani bangare na shirye-shiryen rigakafin da ke tafe.   Ya bayyana cewa za a yi allurar rigakafin cutar kyanda ga yara ‘yan tsakanin watanni 9 zuwa 14 yayin da za a yi allurar rigakafin cutar shan inna ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar.   Mista Farah...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta amince da fara shirin karbar lasisin aiki don kafa sabbin Kananan bankunan guda 5 a wasu wurare da aka zaba a fadin jihar.   Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.   A cewarsa, shirin wani bangare ne na dabarun gwamnatin jihar na fadada hanyoyin samar da kudade da zurfafa shiga harkokin tattalin arziki a yankunan karkara da marasa galihu.   Ya bayyana cewa, za a kafa bankunan masu karamin karfi a kananan hukumomin Birniwa, Gujungu – Taura, Guri, Gwaram da Kaugama.   Ya ce, shawarar da majalisar ta yanke ya nuna irin sadaukarwar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta yi na bunkasa hada-hadar...
    Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar.   Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren ’yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen samar da ilimi kyauta da kuma wayar da kan al’umma don bunkasa ilimi.   Dokta Makoda ya bayyana sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su, da suka hada da daukar malamai aiki, gyaran makarantu, da samar da kayayyakin koyarwa, inda ya bayyana su a matsayin matakan farfado da harkar ilimi.   Ya danganta fitowar jihar Kano a matsayin...
    Prime ministan  kasar spain pedro Sanches ya fitar da wannan sanarwar ne a birnin new York inda ya bayyana cewa za’a aike da jirgin ruwa na soji mai dauke da kayan aiki na bada kariya daga Cartagena ,don daukar mataki  ko da bukatar Haka ta taso na taimakawa  tawagar agaji na Flotilla da ke kan hanyar zuwa Gaza dauke da kayan Agaji domin bada taimakon gaggawa ga yankin falasdinu. Wadanda ke kula da tawagar ta Flotilla sun bada rahoton cewa abubuwan 12 ne suka fashe a lokaci da aka kaiwa jiragen ruwa guda 9 hari acikin ruwan kasa da kasa, sai dai yazuwa yanzu Isra’ila da take ta yi musu barazana na hana tawagar zuwa ko ina ta yi shiru...
    Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga.   Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya.   Sanarwar ta ruwaito shugaban majalisar na cewa rasuwar tsohon sanata mai wakiltar nasarawa ta arewa, mutuwa ce da ta girgiza al’ummar jihar Egu da ma jihar baki daya ba.   “Bishiyar Iroko ta fado, mai taimakon jama’a kuma fitaccen dan siyasa ya je gida ya huta, Allah ya kara masa yarda.” Inji Shugaban Majalisar.   Kakakin Majalisar Danladi Jatau ya bayyana...
    Gwamnatin jihar Kwara ta jaddada kudirinta na sake gyarawa da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a matakin farko.   Sakatariyar zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWPHCDA), Farfesa Nusirat Elelu, ta bayyana hakan a lokacin da ta karbi bakuncin kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) da masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Oke-Ero da kuma shugaban ma’aikatar lafiya a Ilorin.   Ta lura cewa gwamnatin na ci gaba da nuna himma wajen samar da kiwon lafiya mafi dacewa ga kowane dan kasa, musamman a yankunan karkarar da ba a yi musu hidima ba.   Farfesa Elelu ya bayyana cewa, jihar ta bayar da makudan kudade wajen farfado da fannin kiwon...
    Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula.   Rundunar Sojoji da ma’aikatan kwalejin su ta Jaji, ta kammala wani shiri na musamman wanda ke nuna wa ‘yan jarida da sauran masu halartar atisaye, sani da gogewar al’amuran yau da kullum a irin salon rayuwar sojan da ke cikin rukunin.   A wata sanarwa da kakakin kwalejin, Laftanar Kanar Victor Olukoya ya fitar, ya ce an shirya wannan horon ne da nufin samar da kyakkyawar fahimta da hadin gwiwa tsakanin sojoji da masu ruwa da tsaki na farar hula domin samun kyakkyawar alakar aiki wadda a karshe za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron kasa cikin...
    A wani samame na kwanaki hudu na hadin gwiwa na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan tituna, rundunar hadin guiwa mai wanzar da zaman lafiya da farfado da matasa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 78 da ake zargi a manyan wuraren da ke jihar.     A wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA a Kano Sadiq Mohammad Maigatari ya fitar, ya ce rundunar ta yi aiki tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya.     Wannan farmakin dai ya shafi fitattun wuraren da ake aikata miyagun laifuka da suka hada da Mariri Yan’itace, Fagge, Badawa,...
    Da yake magana a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya Yarima mai jiran gado na kasar Kuwait shaikh sabah khalid al-hamad Al-sabah ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin gaza a matsayin babban bala’I, yace alumma faladinu da basu da wani mai basu kariya suna fuskantar wahalhalu mafi muni a tarihi. Har ila yau  ya kara da cewa abin da ke faruwa a Gaza kisan kare dangi ne,da kuma share kabilu, don haka wannan ba zai tafi da yin shiru ba, kana ya yi tir da harin da HKI takai kan kasar Qatar kuma yayi barazanar cewa kai hari kan daya daga cikin mambobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa, kamar kai hari ne akan dukkansu baki daya, Yarima yayi...
    Rahotanni sun bayyana cewa kimanin yahudawa 22 ne suka jikkata biyu daga cikinsu yayi muni sosai a wani hari da dakarun sojin kasar Yamen suka kai da jirgin sama mara matuki  da ya fada garin Eilat na HKI. Bayan keta naurara kariya da ta kafa. Wannan yana faruwa ne ajiya laraba bayan da wasu fayafayen bidiyo ke yawo a yanar gizo yana nuna yadda  mazauna garin ke neman mafaka bayan da bamabamai suka fado cikin birinin wanda ke iyakar birnin da Isra’ila ta mamaye, Yanzu haka dai Isra’ila ta fara gudanar da birncike domin gano dalilan da suka sanya makaman kariyanta basa iya kakkabo makaman da ake harbawa, duk da sake kafa wasu sabbin makaman kariya  guda biyu a yankin....
    Rahotanni sn bayyana cewa shugaban kasar Iran Masud pezeshkyan  ya gana da shugaban  kungiyAr tarayyar turai Antonio costa a gefen taron majalisar dinkin duniya a birnin newyork,Kuma ya fadi cewa wadanda suka fice a tattaunawar JCPOA su suka haddasa aka fada a halin da ake ciki yanzu. Har ila yau ya kara da cewa Iran  bata da niyyar mallakar makamin nukiliya kuma ba za ta taba nemansa  ba, don haka Tehran a shirye take ta yi hadaka domin fayyace gaskiya da kuma karyata zarge-zarge marasa tushe balle madafa da ake yi mata kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya. Yace nauyi ya rataya ne a wuyan wanda suka fice daga yarjejeniyar JCPOA , wato shugaban Amurka ke nan da ya...
    Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ya gana da tsohon shugaban riƙo na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya). Ya fadar ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya gana da Ibas. Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko cikin kusan shekaru 60 Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Tinubu, ya naɗa Ibas a watan Maris domin jagorantar jihar bayan rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin tsohon gwamna Nyesom Wike da wanda ya gaje shi, Siminalayi Fubara. Domin shawo kan rikicin, Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a ranar 18 ga...
    Ranar 22 ga wata, an shirya bikin kadddamar da shirin gaskiya na talabijin mai suna “Laszlo Hudec” cikin harshen Slovak a birnin Bratislava, hedkwatar kasar Slovakia, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da ofishin jakadancin kasar Sin a Slovakia da ma’aikatar harkokin wajen kasar Slovakia suka shirya cikin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata. Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace...
    Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa...
    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya. Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD. Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981. Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya...
      Ta kuma tabbatar da yin garkuwa da mutane shida a yankunan biyu, inda ta kara da cewa wasu shida sun samu raunuka a harbin bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau, jihar Xinjiang tana bikin cika shekaru 70 da kafuwa cikin alfahari da kuma kyakkyawar manufa. Sauye-sauyen aikin gona a yankin suna nuna juriyar mutanensa da karfin hangen nesa yayin da karfin tattalin arzikinsa ya zuwa tsakiyar 2025, ya kai kudin Sin fiye da yuan tiriliyan 9.84 (kwatankwacin dala tiriliyan 1.35), bisa samun ci gaba da kaso 5.7 a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Bako wacce ta bayyana hakan bayan ta duba ɗaya daga cikin cibiyoyin CBT, ta ce, ana gudanar da jarrabawar a cibiyoyi uku da aka keɓe, da suka haɗa da Jami’ar Jihar Kaduna a shiyya ta 2), Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya (Shiyya ta 1) da Jami’ar Jihar Kaduna ta Kafanchan (shiyya ta 3). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Li, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manyan jami’ai dangane da shawarar nan ta tsarin shugabanci da Sin ta gabatar, a gefen babban taron MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka. A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan cinikayya na Sin Li Chenggang, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya ta Sin, a matsayin alkawari dake mayar da hankali ga yanayi da...
    An kammala shirin gudanar da taron lafiya karo na farko a tarihin Jihar Gombe, wanda za a fara a ranar 2 ga Oktoba. Da yake zantawa da manema labarai wannan Larabar a Gombe, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu domin tattauna matsalolin bangaren lafiya da zummar samo mafita. An sake raba Naira biliyan 5 haƙƙoƙin ’yan fansho a Kano Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Ya ce, taron zai samu halartar manyan baki ciki har da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu; Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed; Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate; tare da wasu abokan hulda, ‘yan...
    Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a yau Laraba, game da cika shekaru 70 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai, a wata cibiyar raya al’adu dake birnin Urumqi, fadar mulkin jihar. Bikin nune-nunen ya samar da bayanai masu fadi, dangane da ci gaban da aka cimma sakamakon dunkulewa, da jajircewa, da kwazon al’ummun mabanbantan kabilun jihar ta Xinjiang cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, karkashin kakkarfan jagorancin JKS, da goyon baya mai tasirin gaske daga sauran sassan kasar ta Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya yi kira da a kafa rundinar soji ta kasa da kasa don ‘yantar da Falasdinu da adawa da ‘yan mulkin kama karya da Amurka da NATO ke yadawa.   A jawabin da ya gabatar a zauren MDD,  Petro ya bukaci kasashen da ke adawa da kisan kiyashi da su hada karfi da karfe, domin kare rayukan al’ummar Palasdinu. “Muna bukatar sojoji masu karfi da suka kunshi kasashen da ba su amince da kisan kare dangi ba, Dole ne mu ‘yantar da Falasdinu,” in ji shi. Petro ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ayyukan Washington da NATO ke gurgunta mulkin dimokuradiyya da kuma taimakawa wajen sake dawo da mulkin kama-karya a duniya. Kiran da Petro na...
    Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine. Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar kasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki. Peskov ya tabbatar wa manema labarai cewa babban kuskure ne a yadda ake cewa Ukraine za ta iya yin nasara wajen karbe ikon yankunanta da ke hannun Rasha. Bayan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a New York, Trump ya ce Ukraine na iya kwato dukkan yankunan da ta rasa, inda ya bayyana Rasha a matsayin kyanwar Lami. Ya kuma ce tattalin arzikin Rasha na cikin gagarumar matsala. Tun da farko...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida saboda zargin karya ƙa’idojin majalisar. Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Ko da yake Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatarwar “ta yi tsauri kuma an yi ta ba bisa ƙa’ida ba.” Da yake mayar da martani, Atiku ya ce sake buɗe...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yuni a kan kasar. A lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 ya shaidawa mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a yau Larabar cewa, hare-haren wani babban rauni ne ga zaman lafiya a yankin. Shugaban ya ce hare-haren, wadanda suka afkawa garuruwa, gidaje, da ababen more rayuwa na Iran, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya, “babban cin amanar diflomasiyya da raunana kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne.” Pezeshkian ya zargi Washington da Tel Aviv da ruguza tattaunawar da gangan da karfin soji. Shugaban na...
    Jiya Talata 23 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci babban taro kan shawarar samar da ci gaba ga duniya baki daya, tare da gabatar da jawabi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka. A gun taron da kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, firaminista Li ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya duniya baki daya a wajen babban taron MDD a shekara ta 2021, shawarar da ta mayar da hankali kan muradun daukacin bil’adama. Li ya kuma jaddada cewa, Sin za ta kara zama kasar dake nuna goyon-baya, da taimakawa samar da ci gaba na bai daya, da ci gaba da daukar matakan zahiri, da kara daukar nauyin...
    “Bayan tattaunawa mai yawa, aka samu damar tara ₦100,000, wanda ya biya a cikin asusun da masu garkuwa da mutanen suka bayar, bayan wata ɗaya, sai aka bukaci ya biya wani Abdulmajid Dan-Azumi karin ₦10,000, ba tare da sun saki yaron ba,” Abiodun ya bayyana.   Waliyyin da ya fahimci lamarin ba mai ƙarewa ba ne, sai ya kai rahoto ga ‘yansanda a watan Satumba, inda nan take aka mayar da karar zuwa sashin yaki da garkuwa da mutane na SCID.   ‘Yansandan sun bi sawun Abdulmajid Dan-Azumi mai shekaru 32 dan garin Kwana, wanda, daga nan aka yi nasarar kama abokin hulɗarsa, Abdulnafiu Usman wanda suke zaune duk a unguwa ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.36 a hukumance, inda hakan ya nuna samun sauyi idan aka kwatanta da Naira 1,488.60 da aka sayar da ita a baya. Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama. Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025) Shaidu sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a babura, inda suka dinga harbi ba ƙaƙƙautawa wanda ya sa mazauna ƙauyukan suka gudu. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Motokun, Egboro da Fanagun. Wani mai suna James Ibrahim, ya ce: “Mun farka da safe muka ga mutane suna gudu daga Motokun bayan harin. An harbi wata mace wadda daga bisani ta rasu a asibitin Patigi....
    Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025. Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240). Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Sabuwar motar ta 2025 na dauke da sabon fasali mai ban sha’awa da kuma Zubin da ya sa ta fi tsofaffin nau’ikan da suka gabace ta inganci. A wani bidiyo da Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, an ga lokacin...
    A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Kafar watsa laabrun Politico ta fitar da wani rahoto a jiya Talata wanda yake cewa, hukumar bincike ta ‘yan sandan Amurka ta sami bayanan sirri da su ka shafi muhimman matakan siyasa na gwamnatin Amurka da kuma masu alaka da makaman kare dangi.  Majiyar ta ambaci cewa binciken da aka yi a ranar 22 ga watan Ogusta da ya shude ya sami bayanan da aka bayyana a matsayin “Na sirri’ matuka”. Kafar watsa labarun ta ” Politico” ta kuma ce bayan binciken ofishin bolton da a ka yi, da aka sami na’urar kwamfuta mai cike da bayanan sirri, an kuma kai wani samamen a gidansa dake Jahar Maryland, said ai kuma babu wani bayanai akan nau’oin abubuwan da aka samu...
    Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin  nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
     HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai. Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha. A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya        ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro. Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin...
    A ranar Talata, 1 ga Rabi’ul Thani 1447H, daidai da 23 ga Satumba 2025, Allah Ya yi wa Babban Mai Bayar da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh, rasuwa. An yi jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a ranar Talata bayan sallar La’asar, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya jagoranci manyan malamai da jami’an gwamnati da dubban mutane. Haka kuma, an yi masa Salatul Gaib a Masallacin Ka’aba da ke Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad (SAW), da kuma sauran daukacin masallatan da ke kasar bisa umarnin masarautar UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya...
    Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a ranar Laraba zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin duniya (UNGA) karo na 80 da ke gudana a birnin New York na Amurka. Zai yi jawabin ne a madadin Shugaban Kasa Bola Tinubu tsakanin karfe 3:00 na yamma zuwa 9:00 na dare agogon birnin New York. Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudurorinta na kasa (NDCs) da aka sabunta a karkashin yarjejeniyar Paris yayin wannan jawabi. A baya, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima,...
    Da6n uwansa, Chuks, ya tabbatar da kama shi, amma ya ce Victor ba shi da laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon binciken kudi kamfanin ya fitar, wanda ya ƙare ranar 30 ga Yuni, 2025. Bankin ya kuma ce amma ribar kafin a cire haraji ce, idan aka cire kuma za ta koma biliyan 449.01, idan aka kwatanta da biliyan 905.57...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za su cimma manufa da manufofin da suka cimma ba. A yammacin ranar Talatar da ta gabata a wani jawabi da ya gabatar ga al’ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa;“Na ga ya wajaba a wadannan kwanaki, a ranar shahadar shahidan Sayyid Hassan Nasrallah, a tuna da shi. Sayyed Hassan Nasrallah ya kasance wata babbar kadara ga duniyar Musulunci...
    Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su ne ake bi bashi.” A cewar Pars Today, Larijani ya kara da cewa Iran tana da tsayin daka wajen kare tsaron kasarta, kuma ba za ta bari a sanya wasu sharudda na wulakanci ba, kamar takunkuman da aka dora wa makamai masu linzami. Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa kafa sharadin takaita iyaka da makamai masu linzami zuwa kasa da kilomita...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da inganta uranium ba, kuma tattaunawa da Amurka za ta haifar da illa A jawabin da ya yi wa al’ummar Iran ta gidan talabijin a yammacin jiya Talata, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce: Ba za su mika wuya ga matsin lamba kan wani lamari na su ba. A cikin jawabinsa ta gidan talabijin ga al’ummar Iran a daren jiya, Jagoran ya taya al’ummar Iran murnar shigowar watan Mehr (23 ga watan Satumba, bisa kalandar Iran), da watan komawa makarantu da jami’o’i da ilmantarwa, da kuma shirin kaddamar da miliyoyin matasa a fadin kasar wajen samun ilimi da mulki. Wannan...
    Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan. Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A yayin ganawar da aka yi a ranar Talata, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Iran da Norway, tare da yin musayar ra’ayi kan ci gaban yankin da kasa da kasa. Taron dai ya yi tsokaci kan matsalar jin kai da Falasdinawa ke fuskanta daga sojojin mamayar Isra’ila sakamakon kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran. Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za...
    Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso, Benguendé Gilbert Ouédraogo ya karanta, ta ce: Gwamnatocin Burkina Faso, Jamhuriyar Mali, da Jamhuriyar Nijar, wadanda suka kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel, sun sanar da ra’ayin jama’a na wannan kungiyar da al’ummar duniya kan matakin da suka dauka na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya nan take. A baya, kasashen uku sun bayyana kotun da aka ambata a matsayin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.   Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata. Domin sauke shirin, latsa nan
    A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya isa birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang da safiyar yau, domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Sanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya, kana zai gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashe masu ruwa da tsaki. Yayin tarukan cudanyar mabanbantan sassa, da na bangaren Sin da daidaikun kasashen, Li zai yi karin haske dangane da mahangar kasar Sin game da yanayin da ake ciki a harkokin kasa da kasa a halin yanzu, da manyan batutuwa da ayyukan MDD. Zai kuma fayyace manufofin kasar Sin na...