Collins Whitworth Zai Kafa Tarihin Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
Published: 25th, September 2025 GMT
Indomie, a matsayin jigo da ta daɗe wajen nasarar samar da abinci mai gina jiki ga al’umma, tana alfahari da tallafawa wannan yunƙuri na kafa tarihi na Collins. Shekaru da dama, Indomie ta tallafa wa shirye-shiryen tallafawa a fannin ƙirƙira da ilimi da sana’o’i ga matasa. Tallafawa Collins, wata alamar nasara ce da take nuna ƙoƙarin Indomie na isar da saƙo mai ƙarfi ga jama’a wajen cimma manyan burika da muradan rayuwa da suke bukatar samun goyon baya da ƙarfafa guiwa.
Shigar cikin wannan al’amari wata babbar alama ce da take tabbatar da cewa wannan taron na tarihi ya sami haske da karramawa kamar yadda ya dace, taro ne da yake ƙarfafa wa matasan Nijeriya guiwa domin su samu nasarar cimma burinsu na rayuwa ta hanyar samun ƙwarin guiwa.
An tsara taron zai gudana a Kano a Ranar samun ‘yancin mulkin ƙasa Nijeriya, inda ake sa ran jama’a da iyalai da ɗalibai da masoya fasaha da ƙirƙira da ‘yan jarida daga ko’ina a cikin ƙasa za su hallarci taron. Masu kallo za su samu damar shaida tarihin da Collins zai kafa a lokaci wajen zana fuskar mutane sama da 12 a cikin minti 3 da kuma zana fuskar mutane fiye da 220 cikin awa 1.
Wannan taro da zai samu halartar jama’a zai bunƙasa al’ada da ƙirƙira kuma zai sa ranar ta kasance ta musanman ba kawai taro kadai ba, inda ranar za ta zama muhimmiyar ranar biki ta baje-kolin nuna baiwa da samar da haɗin kai.
Ƙoƙarin kafa wannan wannan tarihin da karbe kambun zai samu goyon baya da bai wa matasa dama ta musanman. Labarin Collins zai ja hankalin matasan Nijeriya waɗanda suke da mafarkin samun shahara a duniya. Kuma zai zama wata shaida ta cimma ƙuduri bayan samun dama da ƙarfafa guiwa daga Indomie a ɓangaren fasaha a Nijeriya.
A yayin da Kano ke shirin karɓar baƙi domin gudanar da wannan gagarumin biki a wannan rana mai ɗumbin tarihi, jama’a na cike da farin ciki a harabar jami’ar da kafafen sada zumunta da wurare daban-daban. Yunƙurin Collins ba kawai nasara ce ta ƙashin kansa ba; lokaci ne na tarihi wanda ke nuna ci gaban fasahar ƙirƙira a Nijeriya a idon duniya, kuma wata ‘yar manuniya ce da take nunawa kowa cewa samun manyan nasarori na farawa ne da sha’awa da ƙuduri da kuma samun tallafi.
Taken Indomie na “Mafarki mai yawa na haifar da nasarori masu yawa” an sanya shi a cikin muradin Collins. A ranar 1 ga Oktoba, duk idanu za su koma Kano domin ganin Collins Whitworth yadda zai kafa tarihi, ba kawai ta zanen fuska ba, har ma ta bayyana irin ƙwazonsa da baiwarsa da yadda zai zama abin alfahari ga ƙasa Nijeriya. Wannan taron wani muhimmin taro ne a duk faɗin Nijeriya a ɓangaren fasaha tare da ƙarfafa guiwar matasa wajen cikar muradan su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Taliya
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.