Aminiya:
2025-10-13@17:53:39 GMT

’Yan bindiga sun harbi wani saboda rashin isassun kuɗi a asusunsa

Published: 25th, September 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓar Naira miliyan biyu a hannun wani mutum, sannan suka harbe shi saboda kuɗin ba su kai adadin da suke nema ba.

Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka mai shekaru 25, Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma.

Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas

Sun harbi mutumin a ƙafa bayan sun gano ba shi da kuɗi sosai a asusun bankinsa.

Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce sun samu kiran gaggawa cewa an yi garkuwa da wani mutum a gidansa da ke Ogwashi-Uku.

’Yan sanda sun bi sahun masu garkuwar har cikin daji a yankin Ogwashi-Uku, inda suka ceto mutumin da da raunin harbin bindiga.

Bincike ya kai ga kama Nka da Okechukwu a Jihar Anambra, inda aka kuma gano motar mutumin da suka harba, ƙirar Toyota Venza.

Bayan amsar laifin da suka yi, ’yan sanda sun kai samame wata mafakarsu da ke ƙauyen Agidiase, Ogwashi-Uku, inda suka kama wanda ake zargi na uku.

Masu garkuwar kuma sun nuna wa ’yan sanda inda suke ɓoye kayan aikinsu, inda aka gano motar da suke amfani da ita da kuma na’urar katse sadarwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda harbi hari

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.

Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.

Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.

Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.

Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.

Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi 
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara