NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci
Published: 26th, September 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba.
Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki. A wasu lokuta masu tsanani, cutar na iya kai mutum asibiti ko ta yi barazana ga rayuwa, musamman ga yara ƙanana, mata masu ciki, tsofaffi, da masu raunin garkuwar jiki.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamatawannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba.
Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a KadunaWaɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke.
Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.”
Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu.
Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun.
Amma wasu na ganin aike sunayen jakadun na da alaƙa da barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na ɗaukar matakin soji a kan Najeriya, kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
A wata hira da aka yi da shi a watan Satumba, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce babu wata matsala game da jinkirin.
Ya ce, “Dukkanin ofisoshin jakadancinmu suna aiki yadda ya kamata. Kowace ofishi yana gudanar da ayyukansa yadda ya dace. Rashin jakadu ba zai haifar da giɓi ba.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa jakada shi ne shugaban ofishin jakadanci, akwai kwamishinoni, wakilai da ma’aikatan diflomasiyya da ke tafiyar da harkokin yau da kullum.
A cewarsa, “Diflomasiyya ba aikin mutum ɗaya ba ne. Tsarin ya tanadi irin wannan yanayi.”
Tuggar, ya kuma ce shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon naɗa jakadu, kuma zai yi hakan a lokacin da ya dace.
Ya bayyana cewa, “Shugaban ƙasa yana duba batun, kuma za a sanar da sunayen a lokacin da ya dace.”
Ya ƙara da cewa, “’Yan Najeriya a ƙasashen waje har yanzu suna samun ayyuka, kuma mu’amala da ƙasashen da muke hulɗa da su ba ta ragu ba.”
Ya ce kuma akwai ƙasashe da dama da suka shafe dogon lokaci ba tare da jakadu ba, amma hakan bai lalata dangantakarsu da wasu ƙasashe ba.
Ya ce, “Wannan ba sabon abu ba ne. Diflomasiyya tana da tanadin irin wannan yanayi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne aiki, ba kwaikwayo ba.”
A ƙarshe ya ce Najeriya tana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran ƙasashen duniya.
“Manufofin ƙasashen waje na Najeriya sun bayyana, kuma ana jinmu a duniya. Abin da muke yi shi ne tabbatar da cewa ofisoshinmu suna samar da sakamako mai amfani ga ’yan Najeriya.”