Xi Ya Halarci Nune-Nune Game Da Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Jihar Xinjiang
Published: 24th, September 2025 GMT
Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a yau Laraba, game da cika shekaru 70 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai, a wata cibiyar raya al’adu dake birnin Urumqi, fadar mulkin jihar.
Bikin nune-nunen ya samar da bayanai masu fadi, dangane da ci gaban da aka cimma sakamakon dunkulewa, da jajircewa, da kwazon al’ummun mabanbantan kabilun jihar ta Xinjiang cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, karkashin kakkarfan jagorancin JKS, da goyon baya mai tasirin gaske daga sauran sassan kasar ta Sin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp