Aminiya:
2025-11-27@23:00:10 GMT

Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni

Published: 25th, September 2025 GMT

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shawarci matasa da ’yan siyasa masu tasowa da su fahimci cewa harkar siyasa ba ta tafiya da rowa, illa juriya da sadaukarwa da biyayya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake rantsar da sabon Alƙalin alƙalai na jihar (Grand Khadi) tare da wasu Masu Ba da Shawara na Musamman, Memba na dindindin a hukumar SUBEB, da kuma Sabbin sakararorin dindindin guda 13 a wani taro da aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu.

An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri

A jawabinsa, Gwamna Buni ya ce matasa da ’yan siyasa masu neman gina makoma a wannan fage dole ne su yi haƙuri da biyayya ga shugabanni, tare da nuna ƙwarewa da ɗa’a domin su samun ci gaba.

A cewarsa “siyasa aiki ne na haƙuri, biyayya da sadaukarwa”, ba za a cimma nasara da rowa ko gaggawa ba. Idan matasa suka rungumi juriya, gobe suma za su zama shugabanni a matakai daban-daban.”

Ya ƙara da cewa, siyasa tana buƙatar haɗin kai, fahimta da tsayin daka wajen bautar da al’umma, ba don amfanin kai kaɗai ba. A cewarsa wannan shi ne ginshiƙin da ya kamata kowanne ɗan siyasa ya yi koyi da shi.

Gwamnan ya kuma ja hankalin sabbin jami’an da aka rantsar da su kasance masu gaskiya, nagarta da aiki tuƙuru domin tabbatar da kyakkyawan tsarin mulki a Jihar Yobe.

“Aikin da aka ba ku nauyi ne daga Allah da kuma al’umma. Ku tabbatar da cewa kun yi shi da gaskiya, aminci da sadaukarwa. Idan kuka yi haka, za ku bar tarihi mai kyau ga al’ummar Jihar Yobe,” in ji Buni.

Wannan taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai da ɗimbin jama’a daga sassa daban-dabam na jihar, inda aka yaba wa Gwamna Buni bisa ga ƙoƙarinsa na gina al’umma mai dogaro da kai, tare da cusa nagarta a cikin shugabanci nagari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja

Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.

Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.

Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.

Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a Borno

A wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.

Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.

Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.

Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja