2025-10-14@19:54:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10178
«da ake zargin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Kamaru Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila. Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka. Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra’ila ba.” Ya ce alakarsu na da kwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro. “Isra’ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru,” in ji shi. Isra’ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban kasar....
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kakabawa Iran takunkumman da aka dage wa kasar a karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, matakin da ya biyo bayan zargin da kasashen Turai ke yi kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Kwamitin sulhun ya maido da takunkumin ne a cikin daren jiya, wanda ya hada da toshe kadarorin Iran da ke ketare, da dakatar da kwangilar sayen makamai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma makamai masu linzami na kasar. Wannan shawarar dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Amurka da kawayenta suka yi watsi da daftarin kudurin da kasashen Sin da Rasha suka gabatar, na neman jinkirta matakin dawo da takunkuman. Share 0 0 votes Article Rating...
Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel. Lamine Zein, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar da a zauren babban taron MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York. Nijar ta kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza, da kuma hare haren Isra’ilar kan Iran da Qatar, da kuma yadda ake nuna halin ko in kula game da rikicin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da Sudan dama yankin Sahel tare da hadin bakin wasu manyan kasashen yamma a nahiyar Afrika. Fira ministan na Nijar, Ya kuma kara da cewa gwamnatin Nijar da takwarorinta na Burkina da Mali, a sun sha...
A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar. Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wacce ta fara ranar Juma’a a Rome, Milan, Naples, da Bologna, ta bazu a ranar Asabar zuwa Florence, Pisa, Ancona, Trieste, Bari, da Alessandria. Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga Gaza da al’ummar Palasdinu na karuwa a tashoshin jiragen ruwa, jami’o’i, makarantu, da wuraren taruwar jama’a a Italiya gabanin zanga-zangar kasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Oktoba...
Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar da cewa, Isra’ila ta kashe akalla wasu Falasdinawa 98 a hare-haren da ta kai a yankin Gaza da ta yi wa kawanya a baya baya nan. Hukumar ta ruwaito wasu majiyoyin lafiya na cewa an kai mutum 23 da lamarin zuwa asibitin Al-Shifa, 29 zuwa Asibitin Baftisma na Al-Ahli, 28 zuwa Asibitin Al-Awda, tara zuwa Nasser Medical Complex, sannan tara zuwa Asibitin Al-Aqsa. Tun bayan da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ta kashe Falasdinawa kusan 66,000 tare da raunata fiye da 167,000, yawancinsu mata da yara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new...
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala. Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar bana Bayanai sun an samu wannan sauyi ne bayan Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Najeriya (FIRS), kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dokta Zacch Adedeji ya shiga tsakani. Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin...
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala. Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar bana Bayanai sun an samu wannan sauyi ne bayan Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Najeriya (FIRS), kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dokta Zacch Adedeji ya shiga tsakani. Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin...
Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar “Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A shekarar 2003 ne aka kafa kotun ta ICC wadda aka dorawa alhakin hukunta laifukan da suka shafi kisan kare dangi da cin zarafin bil’Adama da laifukan yaki kuma tun lokacin da fara aiki kotun ta ICC ta saurari kararraki 33 Masu sukar kotun ciki har da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame sun zargi kotun da nuna son zuciya ko rashin adalci saboda ta fai maida hanakli kan kasashen Afrika. Sai dai magoya bayan kotun sun ce rashin tasirin fannin shariar kasashen Afrika ne ya sa mutane ko gwamnatoci ke neman adalci a kotun ta ICC kasashen yannkin Sahel uku wadanda a halin yanzu ke fama da rashin tsaro sakamakon hare-haren mayaka masu ikirarnin jihadi sun yanke alaka da wasu...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi. Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian ya yi karin bayani kan kokarin diflomasiyya a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da ganawa da shugabannin kasashen Faransa, da Finland, da Switzerland, da Norway, da Iraki, da Bolivia, da kuma majalisar kungiyar Tarayyar Turai. Yayin da yake nuni da cewa an cimma yarjejeniya da bangarorin Turai, ya nuna rashin jituwar da cewa duka daga bangaren Amurka ne. “Mun cimma yarjejeniya...
Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata wanda ke yin barazana ga damar da ta ke da ita a karkashin dokar bunkasar Afirka da damammaki (AGOA). Taron bunkasa harkokin kasuwanci na kasashen Afirka ta Kudu da Sin karo na 9, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya jaddada aniyar kasashen biyu na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki. A wajen taron, shugaban kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin da Afirka ta...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa jiragenta da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, za su koma aiki a mako mai zuwa. Mai magana da yawun NRC, Callistus Unyimadu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Asabar, duk da yake bai sanar da haƙiƙanin ranar da za a koma aikin ba. Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Callistus, ya ƙara da cewa matakin ya biyo bayan nasarar kammala gyare-gyare da bincike a ɓangaren da aka samu matsala a baya-bayan nan. A cewarsa, hukumar na yin aiki ba tare da gajiyawa ba don...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sake jadda yin Allah-wadai da kisan tsohon shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, inda ta bayyana cewa, matakin ya kasance karara a matsayin keta dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya. An fitar da sanarwar ne a wannan Asabar, a daidai lokacin da ake bukin cika shekara guda da kisan gillar da aka yi wa Shahid Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine, wadanda aka kashe a shekarar da ta gabata a wasu hare-hare da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Beirut. A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta kira kisan gillar a matsayin wani babban ta’addanci da nufin yi wa kasa mai cin gashin kanta mamba a...
Shugaban kasar Argentina Javier Milei ya bukaci firaminista Benjamin Netanyahu da ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa kasar Argentina gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, saboda hakan na iya kara cutar da farin jininsa da tuni ya ragu. A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila, Netanyahu ya kasance yana shirye-shiryen tafiya zuwa Buenos Aires, amma Milei ya nemi ya jinkirta tafiyar. Da cewa da cewa Milei sananne ne wajen nuna goyon bayan ido rufe ga “Isra’ila”, an ba da rahoton cewa shugaban na Argentina ya damu da cewa ziyarar Netanyahu za ta yi masa mummunar tasiri a siyasance. Kasar Argentina dai na daga cikin kasashen da har yanzu suke da damar karbar Netanyahu, wanda kotun hukunta manyan laifuka...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899. Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kwanakin baya, shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel ya yi hira da wakilin rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, kasarsa ta Cuba ta yi nazari kan kwaskwarimar da kasar Sin ta yi, kamar su yadda kasar Sin ta mika iko ga kananan gwamnatocin kasar don sa kaimi ga daidaita harkokin sassan kasar, da daukar jerin matakai wajen yin kwaskwarima a kauyuka don tabbatar da wadatar abinci, da daidaita huldar dake tsakanin manyan tsare-tsare da mika iko ga kananan gwamnatoci, da kuma kasuwanci, da sa kaimi ga raya kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire, da bunkasa sha’anin al’adu da yawon bude ido a kasar don maida al’adu su zama jigon sha’anin yawon bude...
Sau da yawa wasu mutane suna raina wanka da gyara jikinsu, Inda suka fi gane wanke jiki ko rashin amfani da turare, bayan kuma tsafta tana daga cikin imani. Abubuwan da ke kawo wari mai tashi ya addabi wadanda ke kusa; sun hada da rashin wanke jiki da lungu da sako a yayin wanka. Sannan rashin saka turare a jiki yana haifar da wari ko da ana wanka. Bugu da kari wasu suna yin kwana hudu, biyar, har zuwa sati daya ba tare da sun yi wanka ba. Kayan jiki ma wasu suna maimaita saka su fiye da sau biyu ko uku a cikin sati daya. Hanyoyin da za a bi domin magance matsalar wari mai tashi su ne; yawan...
Birnin Taicang dake lardin Jiangsu na kasar Sin birni ne da ake kiran shi da sunan birnin kamfanonin kasar Jamus a kasar Sin, domin kamfanonin kasar Jamus fiye da 560 suna aiwatar da harkokinsu a wurin, ciki har da kamfanoni fiye da 60 da suka fi samun ci gaba a wasu kananan fannoni. Watakila wadannan kamfanoni ba su yi girma ko yin suna sosai ba, amma sun zama matsayin gaba a duniya a matakan wasu kananan fannoni, me ya sa Sin ta jawo hankalinsu sosai? Shugaban reshen kamfanin Knorr-Bremse AG dake kasar Sin Bi Guanghong ya yi bayanin cewa, masana’antun kasar Sin sun zama matsayin farko a duniya, kana babu bukatar kashe kudi da yawa, da daidaita matsaloli cikin sauri,...
Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, da ke Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba. Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi. Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da fetur a farashin Naira Sai dai a fusace, ɗalibin ya fisge taɓarya daga hannun wata mata, ya buga wa malamin a kai, wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme. Duk da garzayawa da shi da aka yi zuwa asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwarsa. Wata ganau mai suna Lizzy ta ce: “Malamin kawai yaje rabon faɗa ne, amma Ogbeche ya fusata ya ɗauki taɓarya ya...
An raba nakasun bakan baya ko tasgadewar kashin bayan zuwa mataki uku a ma’aunin kusurwa na “Cobb angle”: Mataki na farko: Mafi karancin nakasu (Cobb 10-25°) Mataki na biyu: Matsakaicin nakasu (Cobb 26-40°) Mataki na uku: Matsanancin nakasu (Cobb 50° zuwa sama). A Mataki na daya da na biyu, likitan fisiyo na taimakawa wajen shawo kan matsalar da kuma magance ci gaban matsalar zuwa mataki na uku (Matsanancin nakasu), wanda sai ya bukaci yin aiki ko tiyata, domin gyara tasgadewar kashin bayan. Matsalolin da ke tattare da tasgadewar kashin baya sun hada da: 1- Tawayar surar jiki 2- Matsalolin numfashi 3- Raguwar ingancin rayuwa da sauran makamantansu. Haka nan kuma, matsalar na faruwa kadan da kadan ba tare da jin...
Rahotanni sun bayyana cewa sama da mautane 77 su ne suka mutu a wani hari da HKI ta kai a yankin gaza a yau kawai, da ya hada da wani harin da takai da ya kashe mutane 11 iyalan mutum guda, Ma’aikatar lafiya ta bada rahoton cewa a ranar alhamis da ta gabata kimanin falasdinawa 265 ne suka jikkata yayin da wasu guda 27 na daban kuma suka mutu a ci gaba da yakin da ta kaddamar kan mutanen gaza. Wasu falasdinawa guda 4 sun yi shahada ciki har da wasu guda biyu a wani hari da HKI taki da jirgin sama mara matuki a sansanin yan gudun hijira na Nuseirat dake tsakiyar Gaza, Ya zuwa yanzu isara’ila ta kashe...
Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar. Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin. A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...

Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da yake bayani a wajen taron na tunawa da shahadar sayyid Hassan Nasrullah da kuma sayyid hashim safiyyudden , babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah, shaikh Naim qasem,yace tsayin daka da marigayi sayyid hassan nasrullah yayi ya zarce bangaranci, kuma ya zaburar da musulmi da kirsitoci da duk masu kishin addini , Yace tunani da ruhun nasarallah sunan acikin lamirin yan gwagwarmaya, kuma tafarkinsa a kungiyance yana ci gaba da tafiya akan wannan tsarin har zuwa cin nasara. Har ila yau ya kara da cewa shahadar sayyid nasarullah da zafi sosai acikin zukata, sai dai kasancewarsa acikin zukatan yan gwagwarmaya yana nan a fili. Yace tunani da ruhin sayyid Nasarullah da jininsa suna bayyana hakikanin gwagarmayar da za ta yi...
Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin ciki harda mambobin kwamitin tsaro na mdd wato kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Amurka. Kasar Rasha taki amincewa da wannan lamarin na dawo da takunkumin madd kan kasar iran , kamar yadda ita ma kasar china ta nuna rashin amincewarta afili da wannan mataki. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyaan ya bayyana cewa da sannuu Tehran za ta yi galaba akan wannan batun...
Rafael Grossi babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA a wata hira da yayi da gidan talbijin din Russia 24 ya bayyana cewa shirin nukiliya iran na zaman lafiya ne baki daya. Wannan maganar ta yi karo da kalaman prime minister isra’ila Benjamin Natanyaho inda ya nuna cewa shirin nukiliyar Iran babban barazana ne, don haka kalaman na shugaban IAEA sun tabbatar da ikirarin da iran ta dade tana yi na cewa shirin na zaman lafiya ne. Grossi ya fadi cewa ya amince hare-haren soji sa israila ta kai sun auna cibiyoyin nukiliyarta ta Fordo Natanza da kuma Isfahan inda ake ci gaba da inganta sinadarin yunariyum. Ya tabbatar da cewa iran ta tace yuraniyom kashi 60% ...
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar tsaro na kasar iran Dr Ali larijani ya isa birnin berut na kasar labanon, kuma ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabi birri ya kuma bayyana ta a matsayin mai amfani sosai domin ta mayar da hankali kan yadda zaa kara kyautata alaka tsakani. Haka zalika larijani ya nuna fatansa na ganin an hada kai domin samar da wani karfi guda daya da zai iya tunkarar makircin da Iisra’ila ke kitsawa. Kana ya jinjinawa shirin da sakatare janar din kungiyar hizbullah ya bullo da shi na tattaunawa da kasar Saudiya, kuma ya bayyana hakan a matsayin babbar dabara. Haka zalika ya jaddada matsayin hizbullah a matsayin wani babban shamaki ga Isra’ila, kuma masu...
Tabbas, ko a zamanin yau ma, aikin raya tattalin arziki ba ya rabuwa da wahalhalu. Misali, a cikin gidajen da ake kiwon jatan lande, dole ne mutane su jure yanayi mai zafi da ya kan kai sama da digiri 40 na ma’aunin Celcius, da kuma tarin sauro dake cizon mutum. Har ila yau, akwai wasu kifayen da ake kiwonsu, misali Mullet, wadanda mazauna yankin Xinjiang ba su saba da cinsu ba, don haka ana bukatar karin kokari a fannin tallarsu a kasuwa.Duk da haka, lokacin da ake magana kan makomar harkokinsu, masu samar da kayan noma na Alar suna cike da kwarin gwiwa. Wani mai kiwon kifi ya bayyana cewa, “Bisa fasahar noman abincin ruwa da muka bunkasa a...
An kai gawar Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Solomon Arase, zuwa Birnin Benin, Babban Birnin Jihar Edo, domin yi masa jana’iza. Arase, ya rasu ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025, a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja, bayan fama da rashin lafiya. Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla ’Yan uwa sun samu Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a fanni iri ɗaya A makon da ya gabata, aka gudanar da bikin tunawa da shi a Abuja. Sai kuma a ranar Asabar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai gawarsa Benin domin kammala bukukuwan jana’izarsa. Ga hotuna:
Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Shugaba kuma Wakilin ofishin hukuma da ke Abuja wanda har ila yau wakilin UNESCO, na Nijeriya, Mista Mendy Albert, wanda Misa Manish Joshi ya wakilta, ya ce tsarin da akwai kwas na mako 10- ta kafar sadarwa ta zamani wanda aka kammala a watan Yuli, an shirya shi ne domin a karawa masu halartar taron yadda za su bunkasa da zamantar da ilimin koyon sana’a da fasaha. Yace TBET wata babbar madafa ce da zata iya taimakawa matasa wajen koya masu dabarun da suka dace, wadanda ta haka ne za su damar tsayawa da kafafunsu dpomin samun bunkasar zamantakewa da tattalin arziki. A nata jawabin,darekta ta fasaha da kimiyya ma’aikatar ilimi ta tarayya,...
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu, yayin da wasu guda biyar suka ji rauni bayan wata tirela ta murƙushe motoci biyu a yankin Madalla, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, a Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Juma’a, lokacin da wata tirela ta samu matsalar birki, ta yi awon gaba da wasu motoci biyu. ’Yan uwa sun samu Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a fanni iri ɗaya Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da fetur a farashin Naira Wani ganau, Saleh Haruna, ya ce kafin aukuwar hatsarin, direban wata motar bas ya bugi wata mota a gabansa, wanda hakan ya haddasa hatsaniya. A cewarsa, a lokacin ne tirelar ta taho da sauri...
Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani? Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala karatun jami’ansu da maki iri ɗaya a matakin Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a wannan shekarar daga jami’o’i daban-daban. Maryam Salisu da yayanta Suleiman Salisu kowannensu ya kammala karatun digirinsa na farko ne da maki 4.51 daga fannin Kimiyyar Kwamfuta, a wannan shekara ta 2025 a Jihar Katsina. A halin yanzu Suleiman ya fara aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) a yayin da ƙanwar tasa...
Kamfanin Matatar Man Ɗangote ya sanar da dakatar da sayar da manta ga kwastomomi a kan farashin Naira. Kamfanin ya ce daga ranar Lahadi 28 ga watan nan na Satumba da muke ciki, zai koma sayar da tataccen mansa a kan farashin Dala. Wata samarwa da ya aike wa kwastomominsa ta ce, yin hakan ya zama dole saboda yarjejeniyar da suka ƙulla na sayar masa da ɗanyen man Najeriya a kan farashin Naira ya kawo ƙarshe. Kasancewar za a fara sayar masa da ɗanyen man a farashin Dala, kamfanin ya ce zai dakatar da sayar da tataccen mansa a farashin Naira. In an email sent to customers at 6:42 pm on Friday, the refinery announced that the suspension will...
Gwamnatin Jihar Gombe ta haramta amfani da littattafan karatu da ba sa iya amfani sau biyu da kuma bukukuwan ‘sign-out’ da dalibai ke gudanarwa a bayan jarrabawar kammala karatu. Daraktan Kula da Ingancin Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Sa’idu Dauda Gadam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a. Ya ce yin littattafai masu guraben amsoshi ko sarari na rubutu da ba sa sake amfani yana jefa iyaye cikin halin ƙuncin tattalin arziki, tare da haifar da asarar kuɗaɗe. Don haka, daga ranar 15 ga Satumba, 2026, dukkan makarantu za su daina amfani da irin wadannan littattafai. Yadda A ‘Daidaita Sahu’ ya ƙwace kasuwar bas da tasi Ƙasashen duniya sun ƙaurace wa Isra’ila a...
A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya. Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban. “Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki. Kwamishinan...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadun kasarta a kasashen Biritaniya, faransa da kuma jamus domin tuntuba, a daidai lokacin da takun tsaka tsakaninta da kasashen ke kara kamari sanadin yunkuinsu na ganin an sake dawo ma Iran da takunkuman MDD. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar yau Asabar ta ce “Bayan matakin rashin da’a da wasu kasashen Turan uku suka dauka na cin zarafin yarjeejniyar nukiliyar 2025 na JCPOA na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, an gayyaci jakadun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Jamus, Faransa da Birtaniya zuwa Tehran.” A ranar Juma’a, Amurka, Birtaniya, Faransa, Denmark, Girka, Panama, Saliyo, Slovenia, da Somaliya sun yi watsi da daftarin matakin da Rasha...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin mummunan lamari ga fararen hula a Gaza yayin da sojojin Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama kan yankin da aka yi wa kawanya. Da yake ambato ofishin kula da ayyukan jin kai na OCHA, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya shaidawa manema labarai cewa “Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, tare da yin mummunar illa ga fararen hula. A karamin lissafi, wannan yana nufin Isra’ila na kai hari ta a kowane minti takwas ko tara.” A Zirin. Ya ce tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan motsin jama’a “sun kirga kusan mutane 16,500 daga arewacin Gaza zuwa kudu” a ranar Alhamis kadai. A nasa...
Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders (MSF) ta ce an tilasta mata dakatar da aikinta a birnin Gaza saboda hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Zirin. “Ba a ba mu wani zabi ba illa mu dakatar da ayyukanmu yayin da sojojin Isra’ila ke kewaye da asibitocinmu,” in ji Jacob Granger, jami’in agajin gaggawa na MSF a Gaza. Ya bayyana cewa jarirai da ake kula dasu, wadanda ke fama da larurori – ba za su iya motsawa ba kuma suna cikin hadari.” A halin da ake ciki Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya kusan 65,600 yayin da Isra’ila ke ci gaba da kazamin farmakin. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta gaza ta fitar, an kawo...
Amurka ta sanar a yau Juma’a cewa za ta soke takardar izinin shiga kasar ta shugaban Colombia, Gustavo Petro, biyo bayan kalaman da aka yi a wata zanga-zangar da aka yi a birnin New York, inda ya yi kira ga sojojin Amurka da su bijirewa umarnin shugaba Donald Trump. A cikin wata sanarwa da shafin X, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta zargi Petro da yunkurin tayar da tarzoma. Gustavo Petro, wanda ya je birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya, ya halarci zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a birnin ranar Juma’a. Ya yi kira, ta lasifika, don samar da “Rundunar ceto ta duniya wanda babban aikinta shi ne ‘yantar da Falasdinu.” Ya yi la’akari da cewa sabon matakin...
Mutum huɗu sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar da ramin da suke hakar ma’adanan ya yi, a Unguwar Dura da ke Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato. Mai taimaka wa gwamnan Filato Caleb Mutfwang kan harkokin ma’adanai, Solomon Dung ya bayyana cewa, “Daga abin da aka gaya min, wasu matasa maza suna aiki a cikin wani ramin haƙar ma’adinai, kwatsam ƙasa ta ruguje kan huɗu daga cikinsu. “Uku suka mutu nan take, kuma an kai wani mutum guda asibiti, kuma abin takaici shi ma daga baya ya mutu.” A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis ɗin nan da ta gabata. Wani mazaunin Unguwar, Chuwang Davou ya shaida wa manema labarai a Jos...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani labarin kuma, Jami’an NDLEA sun kama wata ‘yar kasuwa mai shekaru 38, Okolonkwo Ebere Theresa, a ranar Lahadi, 14 ga watan Satumba, bayan da jami’an tsaron jiragen sama na hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Nijeriya tare da hadin gwiwar jami’an hukumar NDLEA suka gano 1.40kg na methamphetamine da ta boye a cikin rigarta domin shiga jirgin saman Katar. A tashar NAHCO da ke filin jirgin saman Legas a ranar Litinin, 15 ga Satumba, NDLEA ta kama wani kayyakin abinci mai kunshe da dauri 40 na methamphetamine mai nauyin kilogiram 2.30 wanda ya nufi Hong Kong ta hanyar jirgin saman Turkish Airlines. An kama wani da ake zargi mai shekaru 59, Umelo Ifeanyi Benatus,...
Gabanin shekarar 2005 da gwamnatin Kano ta hana sana’ar haya da babur saboda matsalar tsaro da ta kunno kai jihar, jigilar fasinjoji ta ta’allaƙa ne da motocin haya na hayis, ko tasi, a kuma farashi mai sauƙi. Sai dai sannu a hankali, waɗannan motocin hayar suna neman zama tarihi musamman a birane saboda zuwan babura masu ƙafa uku, waɗanda aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ a lunguna da saƙo. Wata ƙididdiga da Hukumar Samar da Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano ta fitar, na nuna gwamnatin jihar tana samun aƙalla Naira miliyan shida a kullum daga harajin Naira 100 da ta sanya wa masu sana’ar A Daidata Sahu — wanda a shekara ya kai Naira biliyan 2.1. Haka kuma...
Sagagi ya roƙi jama’a da su zauna cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiya da Kano ta shahara da shi a Arewa maso Yamma. Ya tabbatar da cewa majalisar za ta yi bincike da tattaunawa kafin ta baiwa gwamnati shawara kan matakin da ya dace bisa ga ƙa’idar shari’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna nan a gidan yari kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci. Kwamishinan ’Yansandan Jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa kwazon da DPO da ’yan banga suka yi da gaggawa, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yansanda da al’umma wajen magance miyagun laifuka. Ya kuma tabbatar wa mazauna Jihar Kebbi cewa, rundunar ‘yansandan ta jajirce wajen kawar da masu aikata laifuka da samar da yanayi mai tsaro. Daga nan sai ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa. Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Lagos a jiya Juma’a domin ziyarar aiki yayin da ƙasar ke shirin bikin cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka. A cewar kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya tafi Legas ne bayan ya halarci naɗin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a garin Ibadan, jihar Oyo. Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman Yayin da yake a Lagos, shugaban ƙasa zai gana da manyan ƴan kasuwa da jiga-jigai a ɓangaren gwamnati domin tattaunawa kan ci gaban tattalin arzikin ƙasa. Haka kuma, a ranar Talata, 30 ga Satumba, zai ziyarci...
Wakilan ƙasaahen duniya sun ƙaurace wa jawabin Shugaban Ƙasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya domin su nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasɗinawa. Fiye da rabin wakilan da suka halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) sun miƙe tare da ficewa daga zauren taron ne a yayin da Mista Netanyahu yake shirin gabatar da jawabin ƙasarsa ta Isra’ila. Zauren taron ya kasance kusan wayan, in banda ’yan jarida da jami’an MƊD da wasu tsirarun wakilan ƙasashe da suka rage a ciki a lokacin jawabin Mista Netanyahu wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ba da umarnin kamo shi domin gurfanarwa kan laifukan yaƙi a Zirin Gaza inda dakarun Isra’ila suka kashe mutane kimanin 79,000, akasarinsu ƙananan...
Ya kara da cewa, duba da irin dimbin Kogunan da ake da su a wannan kasa, idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, za a iya bunkasa fannin na kamun kifi a Nijeriya. Omoragbon ya ci gaba da cewa, kalubalen da ake ci gaba da fuskanta a halin yanzu shi ne, na karancin kudade da kuma ci gaba da samun hauhawar farashin abincin da ake ciyar da kifin, wanda wannnan babban kalubale ne da masu sana’ar ke ci gaba da fuskanta a kasar. “Muna sane da cewa, babban kalubalen da masu sana’ar a kasar nan ke ci gaba da fuskanta shi ne, karancin kudade tare da kuma ci gaba da samun hauhawar farashin abincin kifin, amma za mu...
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da farashin aikin Hajjin 2026, inda aka samu ragin kaso 9.7% cikin ɗari idan aka kwatanta da farashin Hajjin bara 2025. A cewar sanarwar da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya fitar ranar Juma’a da daddare, alhazai daga gundumar Maiduguri–Yola (Borno, Yobe, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.67, yayin da sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67. A gefe guda kuma, alhazai daga jihohin Kudu za su biya N8,561,013.67. Wannan na nufin cewa kowanne mai niyyar tafiya Hajji a bana zai samu ragin kimanin N200,000 ƙasa da farashin 2025. EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025 Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77...
Tashar talabijin din “NBC” ta Amurka ta bayar da labarin cewa gwamnatin Amurka tana Shirin kai harin soja akan wasu wurare a cikin kasar Venezuela. Tashar talabijin din na NBC ta ambato wasu majiyoyi 4 na Amurka da su ka bayyana cewa shugaban kasar Donald Trump bai kai ga bayar da umarnin kai harin ba, amma kasar ta Amurka tana tattaunawa da Venezuela ta hanyar wata kasar gabas ta tsakiya. A cikin makwannin bayan nan dai Amurkan ta kai wasu hare-hare akan kananan jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar ta Venezuela tana mai zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi. A ranar 2 ga watan Disamba din nan ne dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya sanar da...
Tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, har yanzu da akwai damar amfani da hanyoyin diplomasiyya domin warware batun Shirin Iran na makamashin Nukiliya da su ka hada da kafa wata cibiya ta tace uranium, da kuma sake sabunta hanyoyin aiki tare da hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa. Tsohon ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da hanyoyin na diplomasiyya sun kunshi sake bude tattaunawa da kasashen turai uku, da kuma Rasha da China, kuma watakila Amurka ta shigo daga baya. Sai dai kuma minstan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa, sharadin samun nasarar ta fuskar diplomasiyya ya ta’allaka da idan kasashen turai sun daina halinsu na fuska...
Har ila yau, ya kara da cewa; kudaden shigar da za a samu, za su karu zuwa dala 657, inda kuma za a kara samun sama da tan miliyan 1.2. Ya ci gaba da cewa, albarkatun da Nijeriya ta ke da su, kashi 20 a cikin dari ne kacal na miliyoyin hektar noman da ake da su a wannan kasa ake nomawa, wanda kuma na hektar noman rani ta haura miliyan uku. Ministan ya kuma sanar da cewa, bisa sauye-sauyen da ake ci gaba da samar wa bangaren shiyoyin sarrafa amfanin gona don samun riba, samar da kayan aiki da kudden aikin noma da bankin manoma ke yi da sauransu. Kyari ya kuma bai wa masu son zuba hannun jarin...
MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen kamfanoni 11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a shekarun baya ne dai MDD ta fara fitar da sunayen kamfanonin da suke aiki tare da HKI a wajen keta dokokin kasa da kasa da keta hakkokin al’ummar Falasdinu. Daga cikin kamfanonin bayan nan da aka kara sunayensu da akwai Heidelberg na kasar Jamus da kuma Ineco na kasar Spain. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, an kuma ci gaba da aikin ceto na fito da mutanen har zuwa jiya juma’a. Wani mazaunin yankin ya ce, an ceto da mutane 13 daga karkashin baraguzai, ana kuma jin cewa da akwai wasu mutane fiye da 100 da suke karkashin kasa. Wani shaidar ganin ido kuwa cewa ya yi, a tsakanin mutanen da sun kai 100 da...
Da dama daga cikin tawagogin da suke halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara sun fice a yayin da Fira ministan HKI ya fara jawabi, domin nuna kin amincewa da kisan kiyashin yankin Gaza. A jawabin nasa wanda tsirarun mutane su ka saurare shi, ya soki kasashen Faransa, Birtaniya, Australia da Canada da su ka bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu. Wani kwamiti da MDD ta kafa na bincike akan abinda yake faruwa a Gaza, ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila” suna aikata laifukan yaki cikin ganganci. HKI tana kara yin bakin jini a tsakanin kasashen duniya saboda yakin Gaza da kuma yadda ta ke take dokokin kasa da kasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
Haka kuma, ya fadi zaben shugaban kasa na 2015 ga dan takarar jam’iyyar APC, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli na wannan shekara. Akwai zazzafar muhawara kan dokar da ta bai wa Jonathan damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin shahararrun jiga-jigan jam’iyyar PDP, Sule Lamido, a kwanan nan ya bayyana Jonathan a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2027. Lamido ya kuma yi kira da shugabancin jam’iyyar na kasa su yi kokarin tabbatar da an tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2027. Jonathan ya ce, “Dimokuradiyya a Nahiyar Afirka na fuskantar babbar barazana, sannan ta kusa da rushewa sai dai masu...
Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun. Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin...
Bisa sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ” shugaban kasa ne zai nada shugaban INEC da mambobin hukumar zabe ta kasa, sannan majalisar dattawa ta tabbatar da su.” Dangane da tanadin da ke cikin tsarin mulki, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya tanadi jerin sunayen ‘yan takara da za su meye gurbin Yakubu. Da yake jawabi kan tsammanin jam’iyyar APC mai mulki, daraktan yada labarai, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa yayin da jam’iyyar ke nufin lashe duk zabe, tana jaddada bukatar samun yin aldaci ga kowa. Ibrahim, a cikin wata hira, ya bayyana cewa, “A matsayinmu na jam’iyya, abin da muka sa a gaba shi ne samun nasarar cin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da su a kotu. ’Yansanda sun bayyana cewa kamen na cikin ƙoƙarin murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar Kaduna da kewaye. Sun ƙara da cewa waɗanda aka kama sun amsa laifukansu, ciki har da fashi, satar waya da kuma sayar da kayan sata. Kwamishinan ’Yansandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya jinjina wa jami’an saboda jajircewarsu wajen gudanar da aikin. Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka kuma, ya buƙaci ’yan kasa su kasance cikin shiri, tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama masu laifi. Ya ce, “Idan muka haɗa kai, za mu tabbatar Kaduna ta kasance...
Yayin da ƙasashe irin su Birtaniya, Kanada da Ostareliya suka amince da kafa ƙasar Falasṭinu, ana tsammanin samun ƙarin wasu ƙasashe. Shugaban Falasɗinu, Mahmud Abbas, ya yaba da wannan mataki tare da kira ga sauran ƙasashe su nuna irin wannan goyon baya. Zargin ɓatanci: Kwamitin Shura na Kano ya fara sauraron koke-koke kan Malam Triumph An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Yawancin ƙasashen Afirka sun riga sun amince da Falasdɗinu tun shekarun 1980. Shugabanni irin su Thomas Sankara da Nelson Mandela sun taɓa danganta gwagwarmayar Falasɗinawa da irin ta Afirka na neman ’yanci. Amma har yanzu akwai ƙasashe biyu da ba su amince da kafa ƙasar Falasɗinu ba; wato Kamaru da Eritrea. Kamaru Kamaru tana da alaƙa...
Da Baba Zube ya mike don yi jawabi bayan an gabatar da shi, sai ya yi waiwaye Wanda masu iya magana suka ce, adon tafiya. Ya kawo takaitaccen bayani kan gwamnati a kasar da yau ake kira Nijeriya. Ya tabo, Daular Usmaniyya mai hedikwata a Sakkwato, wadda kuma ita ce daula ta karshe da Turawa suka rusa a kasar nan. Kuma ya bayan cewa Daular Borno da ta Kwararrafa ne kawai a Arewa ba su cikin Daular Usmaniyya. Sai Kudu maso Yamma da ya zauna a karkashin Daular Yarbawan Oyo. Kudu maso Kudu kuma Daular Benin, yayin da Yankin Kudu maso Gabas ke rayuwa karkashin kananan sarakunan kabilar Ibo. Ya yi takaitaccen bayani kan yadda Turawan Mulkin Mallaka suka ci...

A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri. Ya zuwa yanzu, Chen da Wang sun riga sun koma sashin gwaje-gwaje na Wentian lami lafiya, al’amarin da ya shaida babbar nasarar da suka samu wajen gudanar da ayyuka a wajen kumbon. Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun...
Wanda duk zai gaya maka gaskiya musamman wanda yake zaune ko ya ke zuwa wuraren da aka samu matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi na jihar Katsina zai fada maka cewar an samu zaman lafiya fiye da lokutan baya. An sha ruwaito wadanda wannan bala’i ya shafa suna maida martani ga masu suka sulhu da cewa duk wanda baya goyon bayan wannan sulhu dan ba a wannan yanki yake da zama ba. Sai dai kuma yin sulhu da barayin daji ba yana nufin an samu zaman lafiya dari-bisa-dari ba. Ana dai samun saukin kai hare-haren ‘yan bindigar amma ba wai an daina ba ne baki daya. To, ta ya ya al’umma za su amfana da wannan yarjejeniyar zaman sulhu da...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a Ballon d’Or Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara A cewar kwamitin, za a gayyaci masu ƙorafi da Malam Triump domin su gabatar da hujjoji. Masu ƙorafi za su fayyace abubuwan da suke tuhumar malamin, yayin da shi kuma za a ba shi damar kare kansa. Bayan haka kwamitin zai tattauna bisa ƙa’idojin shari’ar Musulunci. Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida...
A ranar Litinin aka gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a Birnin Paris, inda ake karrama fitattun ’yan ƙwallon duniya. A bana, Ousmane Dembele na Ƙasar Faransa da PSG ne, ya lashe kyautar maza, yayin da Aitana Bonmati ta Spaniya ta lashe ta mata karo na uku a jere. An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Abin farin ciki ga Najeriya shi ne, mai tsaron ragar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta zo ta huɗu a jerin mata, wanda shi ne matsayi mafi girma da wata ’yar Najeriya ta taɓa samu. Ga jerin ’yan Najeriya da suka taɓa shiga cikin jerin waɗanda suka fafata neman kyautar Ballon d’Or:...
Ita kuwa Abuja Babban Birnin Nijeriya ta samu wasu marasa lafiya guda biyu da wani nau’in zazzabi da ke sa mutane zubar da jini amma hukumomi sun ce ba a sami marasa lafiyar da Lassa ko kuma Ebola ba. Cuta mai zagwanye naman jikin dan’adam Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN ya rawaito cewa cutar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai a Jihar Adamawa tana faraway ne daga kuraje. Daga nan kuma sai su fashe tare da zagwanyewa inda wani lokacin ma suke side fatar har su tarar da kashi a gabar da cutar ta shafa. Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cutar kuraje ta Buruli Ulcer da daya daga cikin cutukan da ba a fiya mayar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya. Sakataren Majalisar ta Iran Ali Larijani ya sake nanata kudurin Iran na cewa ba da ta niyyar yin amfani da makamin nukiliya – ko dai a yanzu ko a nan gaba. Ya kuma ce ayyukan wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni ya sanya tattaunawar ta zama “bazara”. Yau Juma’a ne kwamitin sulhu na...
Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake jaddada ƙudirinta na ci gaba da tallafawa dukkan hukumomin tsaro da ke yaƙar ’yan bindiga da ta’addanci a jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya tarbi Daraktan Yaɗa Labaran Sojoji, Birgediya Janar T. I. Gusau, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Birnin Kebbi. Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Neja Alhaji Yakubu ya bayyana irin muhimman tallafin da Gwamna Nasir Idris ke bayarwa tun daga lokacin da ya fara mulki shekaru biyu da suka gabata, wanda ya haɗa da kayayyakin aiki da alawus...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fashewar abin damuwa ne Shugaban ya ziyarci Kaduna, “Kuma abu na gaba da muka ji shi ne an samu fashewar wani abu bayan tafiyarsa, don haka abin da ya fara zuwa a raina shi ne ko zagon kasa ne ko kuma barazana ce ta tsaro. “Na kuma damu da sanin ko an samu mace-mace, da lokaci ya yi, mun fahimci cewa yawan mace-macen ya yi kadan, a yanzu, babu wata alama da ke nuna zagon kasa ne, sannan kuma yadda gwamnati ta mayar da martani abin yabawa ne.” Ya kara da cewa, “An kafa wani kwamiti da zai binciki abin da ya faru.” Masanin tsaro ya ce za a iya dakile fashewar. “Za a iya hana fashewar, amma kamar yadda...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun rundunar sojoji ta 22 Armored Brigade da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike V tare da haɗin gwiwar Jami’an tsaron gandun daji sun kashe wasu ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba a dajin Kainji da ke Ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja. Hakazalika an samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da babura 4 daga hannun maharan. Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 22 da ke Ilorin, Captain Stephen Nwankwo, a wata sanarwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce, ɗaya daga cikin jami’an da suke kula da gandun dajin yankin...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
Dakarun rundunar sojoji ta 22 Armored Brigade da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike V tare da haɗin gwiwar Jami’an tsaron gandun daji sun kashe wasu ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba a dajin Kainji da ke Ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja. Hakazalika an samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da babura 4 daga hannun maharan. Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 22 da ke Ilorin, Captain Stephen Nwankwo, a wata sanarwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce, ɗaya daga cikin jami’an da suke kula da gandun dajin yankin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin. ‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad Store’ Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata. Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin...
Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan aka bar mu sai dai halal da haram kawai! Su ma din an hana ma halal din gurbin ta, ba mu da wata magana sai dai haram! Da a ce malamai biyar za su taru, to za ka ga ba za su kago komai ba sai haram. Amma sauran malaman kasar Turai kuwa da zarar sun hadu sai ka ga sun kago wata sabuwar kira,...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Mallakar makamashin nukiliya hakkin Iran ne, kuma tattaunawa da Amurka ya kai ga toshasshiyar hanya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa ta gidan talabijin, inda ya yi jawabi kan batutuwan cikin gida da na shiyya da kuma kasa da kasa. Jagoran ya dauki matakin wuce gona da iri da yahudawan sahayaniyya suka yi wa kasar Iran da nufin kifar da gwamnati, amma hadin kan al’ummar kasar ya hana hakan. Dangane da batun makamashin nukiliya kuwa, ya jaddada cewa Iran ba za ta yi watsi da haƙƙinta ba, yana mai nuni da mahimmancin makamashin nukiliya a fagage daban-daban. Dangane da tattaunawar da aka yi da Amurka,...

Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Martanin Iran zai yi daidai da sabon halin da ake ciki idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan kasarsa Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Bolivia Luis Arce Catacora a birnin New York na kasar Amurka, ya jaddada cewa Iran za ta daidaita ayyukanta daidai da duk wani sauyi na al’amuran kasa da kasa idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan Kasarsa. Pezeshkian ya bayyana cewa, manufofin bai-daya na Amurka suna yin illa ba wai ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kadai ba, har ma da dukkan kasashen da ba su dace da alkiblarta ba. Ya kuma jaddada bukatar kasashe masu cin gashin kansu su...
Kasashen China da Rasha sun yi kira da a jinkirta mayar da takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kasashen China da Rasha sun bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya kada kuri’a kan tsawaita lokacin sake kakaba takunkumi kan Iran zuwa tsawon watanni shida nan gaba a yau Juma’a. Kasashen China da Rasha sun gabatar da wani daftarin kudiri na hadin gwiwa da ke neman tsawaita dage takunkumin har zuwa ranar 18 ga Afrilun shekara ta 2026. Kasashen China da Rasha sun tabbatar da “ci gaba da hadin gwiwa” tsakanin kasar Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, inda suka yi kira ga bangarorin da ke cikin shirin hadin gwiwa na JCPOA da su gaggauta dawo...
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar. Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar. Aminiya ta rawaito yadda majijoyi masu tushe suka tabbatar da cewa tuni Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, a kan batun komawar. Kwankwaso ya fara tattaunawa da Nentawe kan maganar komawa APC Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Amma a cikin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, ranar Juma’a Ganduje ya ce jam’iyyar tana da dokoki da sharudda,...
Magajin garin Landan ya caccaki shugaban Amurka Trump, yana mai cewa shi mai nuna wariyar al’umma ce tare da kyamar musulmi Magajin garin Landan Sadiq Khan ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai nuna wariyar al’umma kuma mai kyamar musulmi,” bayan da Trump ya zarge shi da neman aiwatar da shari’ar Musulunci a babban birnin Birtaniya. Khan ya shaida wa tashar Sky News cewa: “Yana ganin Trump a matsayin mai nuna wariyar al’umma, mai dabi’ar bunsuro, mai son zuciya, kuma mai kyamar musulmi.” Ya yi nuni da cewa, Landan ce ta farko a cikin alamomi da dama, kamar zuba hannun jari na kasashen waje, ya kuma jaddada cewa “yana matukar alfahari da cewa Landan ce birni mafi girma...
Sojojin Yemen sun kaddamar da mummunan farmaki kan yankin Jaffa da makami mai linzami Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Alhamis cewa; Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da aka mamaye. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Rundunar sojinta ta kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2 mai dauke da kawuna da dama, inda harin ya yi mummunan barna a yankin Jaffa da aka mamaye. Sanarwar ta kara da cewa, wannan farmakin ya samu nasarar cimma manufofinsa, kuma ya sa miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya sun tsere zuwa matsugunin karkashin kasa tare da dakatar da zirga-zirga a filin jirgin...

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari. Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas. Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru...
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo. Bikin da ba a taba yin irinsa a Ibadan ba Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Dattawa ’Yan asalin Ibadan (CCII), Cif Ajeniyi Ajewole ya ce, dukkan attajirai ’yan asalin Ibadan an dora masu haraji daga Naira miliyan 10 zuwa sama a matsayin gudunmawarsu ga wannan biki da aka fara da addu’ar rokon Allah a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce, “mun kammala shirin yin bukukuwan nada...
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a bangaren na TTP tun lokacin da aka faro sun hada da, sanya ido kan sama da manyan motocin miliyan uku da ke shiga cikin Tashoshin musamman bisa nufin rage cunkoson da kuma sake fitarsu, daga cikin Tashoshin a kan lokaci Ya sanar da cewa, kirkiro da tsarin biyan kudade kan lokaci na shigar motocin cikin Tashoshin hakan ya taimaka matuka, wanda kuma bisa hadakar da...
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama da kuma martani daga ƙungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi kwanan nan a jihar. A cewar sanarwar da ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Musa Tanko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a miƙa batun ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin yin nazari da tattaunawa. Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97 Tinubu Ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Babban Ɗan Jarida Kabir Yusuf Ƙungiyoyin da suka shigar da ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria, da Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da Interfaith Parties for Peace and...
Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai uku da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, inda ya zarge su da yin “ba bisa ka’ida ba da kuma rashin da’a” ta hanyar neman mayar da takunkumin da kwamitin sulhu na MDD ya kakabawa Iran ta hanyar da ta dace. A wata tattaunawa da ta yi da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper a ranar Alhamis, Araghchi ya bayyana cewa, kasashen Turai ba su da hujja kan kokarin da suke yi na maido da kudurorin da aka soke a baya. Araghchi “ya yi kakkausar suka kan matsayin kasashen Turai uku da cewa bai dace ba, ba bisa ka’ida ba kuma maras nauyi,” in...