Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 na kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kai, a babban zauren taron jama’a na Xinjiang. Kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin.

Memba dindindin na ofishin siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ko CPPCC, kuma shugaban tawagar kwamitin kolin jam’iyyar Wang Huning, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.

Kazalika, memba dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Cai Qi shi ma ya halarci taron.

A cikin jawabinsa, Wang Huning ya bayyana cewa, kwamitin kolin JKS a karkashin jagorancin Xi Jinping, ya ci gaba da dubawa, da tsai da tsare-tsaren gudanar da harkokin Xinjiang daga mahangar dabarun siyasa na zamani, ta yadda za a ingiza ci gaban wuri a mabambantan bangarori, tare da cimma nasarar kawar da kangin talauci tare da al’umomin yankin. Kana da gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni, da zurfafa hadin kan al’ummar Xinjiang, ta yadda jama’a za su kasance tare kamar ’ya’yan rumman, su yi tafiya bai daya a kan hanyar ci gaban Sin.

Wang Huning ya kara da cewa, Xinjiang na kan wani sabon mataki na tarihi na samun ci gaba. Don haka dole ne a ci gaba da bin salon jagorancin Xi Jinping bisa ruhin tsarin gurguzu mai sigar musamman a sabon zamani, kuma a aiwatar da tsarin gudanar da harkokin Xinjiang da JKS ta tsara yadda ya kamata. Har ila yau, a nace da kyautata tsarin cin gashin kai a yankin. Kana ya bukaci a yi kokari don gina Xinjiang mai hadin kai, da zaman lafiya, da wadata, da ci gaban al’adu da kuma muhalli mai kyau. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kwamitin kolin

এছাড়াও পড়ুন:

Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata

 

Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta  October 11, 2025 Daga Birnin Sin Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025 October 11, 2025 Daga Birnin Sin Tarihin Hassan Usman Katsina (1) October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang
  • Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
  • Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace
  • Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata
  • Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
  • Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
  • Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya