Aminiya:
2025-11-27@21:42:42 GMT

2027: Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni Shugaban Ƙasa — Atiku

Published: 25th, September 2025 GMT

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.

An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri

“Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson.

Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar ya jaddada cewa alaƙar aurensa da Yarbawa ya sa irin wannan fargabar bata da tushe balle makama.

Ya ce, “Na yi matuƙar farin ciki da na sami mata daga cikin wannan nau’in jinsin, wanda hakan ke nuna cewa dangantakar da ke tsakanina da Yarbawa ta yi daidai da nasabar jinsin iyali.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa Yarbawa, ko ɗaiɗaiku ko kuma rukunin jama’a, sun kasance suna da matsayi na musamman a cikin zuciyata.”

Ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi, yankin Kudu-maso-maso-Yamma zai kasance jigon aiwatar da manufofinsa.

“Haka kuma a dalilin haka ne muradin Yarbawa za su kasance a kodayaushe wajen aiwatar da manufofina da gudanar da mulkina da yardar Allah idan na yi sa’ar nasarar zama shugaban ƙasa a 2027.

“Saboda haka, tsoron zama na shugaban ƙasa na iya haifar da mulkin bai wa Hausa/Fulani fifiko a kan Yarabawa ko wasu ƙabilu kawai bai taso ba, har ma ba shi da tushe balle makama domin ɗaukacin kabilar Yarabawa dangi ne da kuma surukaina,” in ji shi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da misali da aurensa na farko da Titi ’yar Yarbawa ce ’yar Ijesha, wadda ya aura a shekarun 1970, a matsayin hujjar alaƙarsa da yankin Kudu maso Yamma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Alhaji Atiku Abubakar idan aka zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.

Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.

Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.

Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.

Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”

“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.

Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.

Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.

Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia