Ranar 22 ga wata, an shirya bikin kadddamar da shirin gaskiya na talabijin mai suna “Laszlo Hudec” cikin harshen Slovak a birnin Bratislava, hedkwatar kasar Slovakia, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da ofishin jakadancin kasar Sin a Slovakia da ma’aikatar harkokin wajen kasar Slovakia suka shirya cikin hadin gwiwa.

(Tasallah Yuan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.

Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.

Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya

Lamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana.

Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.

Sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.

“An hamɓarar da gwamnatina,” in ji Shugaba Umaro Sissoco Embalo cikin wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na ƙasashen waje.

Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido kan zaɓen.

Ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.

Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar.

Sojojin suna kuma ƙoƙarin katse Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.

Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.

A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

“Mun yi Allah-wadai da wannan yunƙuri na daƙile tsarin dimokuraɗiyya, kuma muna kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS su ɗauki matakin dawo da tsarin mulki,” in ji su.

Sun buƙaci mutanen Guinea-Bissau su kwantar da hankalinsu, tare da kira ga sojoji su saki dukkanin jami’an da suka kama domin a ci gaba da gudanar da zaɓe cikin lumana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew
  • Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa
  • Mali: An Dakatar Da  Aikin Kafafen Watsa Labarun Faransa Biyu A Cikin Kasar Mali
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya