2025-05-01@08:19:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 615

«ya kara da cewa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Yanzu shekarar ta 2025 muke ciki, kuma matakin da duniya ke daukawa wajen gudanar da al’amura ya bambanta da shekaru goma da suka gabata. Amma abin takaici shi ne, wasu har yanzu sun nace ma tsoffin dabaru, suna ganin barazanar haraji da takunkumi na iya mamaye duniya, na san kun riga kun san inda na dosa. Shugaban Amurka Donald Trump da aka rantsar a baya-bayan nan ya yi barazanar sanya harajin kashi 100 bisa 100 kan kasashen BRICS idan suka ci gaba da kokarin rage tasirin dala. “A matsayinsu na al’ummar BRICS, za a kakaba musu harajin kashi 100 bisa 100 idan har suna tunanin aiwatar da abin da suke tunani, don haka za su yi watsi da hakan nan...
    A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP. ‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a  ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar Borno. Wani soja da ya tsira daga wannan harin ya fadi cewa harin ‘yan ta’addar ya dauki sa’oi 3, kuma sun je wurin ne a cikin manyan motoci tare da shammatar sojojin. Kamfanin dillancin labarun Reuters wanda ya ambato sojan ya ce, maharan sun rika harbinsu ta kowace kusurwa, sai dai sun mayar da wuta.Haka nan kuma ya tabbatar da cewa an kashe kwamandnsu. Mazaunan...
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a yankunansu domin samun ci gaba a jihar.   Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin murnar cika shekaru 5 akan mulki da kuma murnar cika shekaru 50 da haihuwar HRH, Chim Nku, Mista Habila Adamu Aboki a karamar hukumar Akwanga.   Mista Danladi Jatau, wanda ya bayyana muhimmancin hadin kai da zaman lafiya ga ci gaban al’umma, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su ci gaba da sasanta al’ummarsu domin zaman lafiya.   Ya taya sarkin mai daraja ta biyu murnar tare da yi masa fatan Allah...
    Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe. Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da ke Mai-Saleh a tsakanin jihohin biyu. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro mai barin gado, Manjo-Janar Edward Buba, ya tabbatar da rasuwar sojoji 22 a harin. “Jimillar sojoji 22 ne suka rasu wasu da dama sun jikkata a yayin artabun,” in ji Edward Buba. Amma wasu majiyoyi sun ce sojojin da suka kwanta dama sun haura 27. Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da...
    Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025. Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin. Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar...
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa a kafafen yada labarai na masu gwagwarmaya. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu yakamata mutanen kasar su maida hankali wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma dogaro da kai kan dukkan abubuwan da yakamata ba zasu nemi shi nan gaba daga wajen makiya ba. Mutanen kasar Yemen karkashin kungiyar dai ta yaki kasar Saudiya da kawayenta na tsawon shekaru 8 ba tare da...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey  Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
    A kwanakin nan ne wani asibitin kula da dabbobi a kasar Turkiyya ya wallafa wani labari mai ratsa jiki na wata karya da ba ta da masauki ta ɗauki ɗanta da ya suma a bakinta ta ajiye shi a kofar asibitin kamar mai neman taimako. Idan ba don gajeran bidiyon da kyamarorin na’urar CCTV suka ɗauka ba, da alama yawancin mutane za su yi tunanin wannan labarin ba zai iya zama gaskiya ba. ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Wani asibitin dabbobi a Unguwar Adnan Kahveci da ke Beylikduzu, a lardin Istanbul na ƙasar Turkiyya, kwanan ya fitar da rahoton ɗaya daga cikin muhimman harkokin asibitin....
    Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
    Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
    Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana  wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau. Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin  wasannin gargajiya na wannan  yankin na Afirka. Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu  cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen  shekara. Janar...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...