2025-09-17@21:54:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2944

«duk shekara»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta ne domin nuna gamsuwa da irin ci gaban da Gwamna Idris ya kawo wa talakawa. Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire “Mun tuntubi mutane da yawa kafin a zaɓe shi, kuma kowa ya tabbatar cewa shi ya cancanta.” A nasa jawabin, Sarkin Zabarmawa na Jihar Kebbi, wanda kuma shi ne tsohon...
    Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha. Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar. Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen...
    Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48. An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa. ’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi NDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike. Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi. Daga kanmu, magana ta...
    Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu. Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen. Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin. Sai dai kuma Sanata Ndume...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin. Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin. Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa...
    Kasar Venezuela ta sami sakon tallafi daga kasar Iran a lokacinda ministan harkokin wajen kasar Vanezuela ya gaba da jakadan Iran a Caracas. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa zasu kara karfafa dangantaka ta musamman dake tsakaninsu na tsaro da sauran bangariri masu musammancin da ke tsakaninsu. Saboda kare diyaucinsu da kuma iko a kan kasashensu. Ministan harkokin wajen Venezuela Efan Jeel ya bayyana cewa sun tattauna da Jakadan Iran a Venezuela Ali Shagni a ranar litinin da ta gabata. Ministan ya kara da cewa Venezuela ta sami sakon tallafawa daga kasar Iran don tunkarar barazanar da kasar take fuskanta daga kasar Amurka. Share 0 0 votes Article...
    Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki. Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum...
    ’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa. Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar. Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford,...
    shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean. Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa. “Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su...
    Manchester United ta amince za ta ɗauki golan tawagar Belgium, Senne Lammens daga Royal Antwerp kan fam miliyan 18.1 har da karin tsarabe-tsarabe. Sasashen wasanni na BBC ya ruwaito cewa hakan ya kawo karshen zawarcin golan Aston Villa, Emiliano Martinez da ta yi. An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe Lammens, mai shekara 23, zai saka hannu a ƙungiyar Old Trafford kan yarjejeniyar kaka biyar. United na fatan ɗinke ɓarakar gurbin mai tsaron raga, bayan da Altay Bayindir ke kuskure a wasannin Firimiya, yayin da ake zargin Andre Onana da sakacin da ya janyo aka fitar da United a Carabao Cup...
    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban. A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin...
    Shawarar da Iran ta gabatar ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zai durkusar da darajar kudin dalar Amurka A jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a kasar China, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da shawarar kafa tsarin hada-hadar kudi ga kungiyar da rage dogaro da kudin dala. A rana ta biyu ta taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, wanda aka shirya a birnin Tianjin na kasar China, tare da halartar shugabannin kasashe fiye da 20, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, da inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi, domin dakile illar da takunkumin da ake kakaba wa kasashe na bangare guda zai haifar....
    Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare. Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi. Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Ya bayyana cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu ta hannun sashen da ke bincike cin zarafin mata na rundunar da ke Ikeja. A cewar Hundeyin, lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, inda ƙanwar wacce abin ya faru da ita ta kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Meiran, daga nan...
    A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604.   Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna amfana da manyan hanyoyi, layukan dogo da kuma hukumomin raya yankuna.   Ministan ya ce daga cikin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa akwai Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da kuma Hanyar Gadar Neja ta 2.   Haka kuma, gwamnati ta samar da fiye da naira biliyan 250 don ayyukan...
    Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda ya ce ya shirya yin “alwashi” akan wannan nasara. Wike ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, yana mai ƙaryata hasashen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce Tinubu ba zai yi nasara ba a zaɓen mai zuwa. Wike ya ce, “Ina da tabbacin Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Na ji wani yana cewa zai zo na uku, ban san irin lissafin da ya yi ba. Idan zai zo na uku, to waye zai zama na farko da na biyu?” Wike...
    Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hari kan wani jirgin daukar man fetur na HKI a arewacin tekun maliya a safiyar yau litinin. Mai magana da yawun sojojin kasar ta Yemen Burgediya Yahyah Saree ne ya bada wannan sanarwan a wani jawabin da ya gabatar a faifai bidiya a safiyar yau Litinin, tare da amfani da makamai mai linzami samfurin Bailistik. Ya kuma tabbatar da cewa harin ya kai ga hadafinsa ya kuma wargaza jirgin ruwan na HKI dauke da manfetur zuwa haramtacciyar kasar. Gwamnatin kasar Yemen dai tana yaki da HKI tun bayan fara yakin tufanul Aksa a cikin watan Octoban shekara da 2023. Kuma HKI ta sha kaimata hare-hare, amma a wannan karon ta kai hare-hare kan...
    Sojojin HKI sun kashe wata yar jarida mai aikiwa tashar talabijin ta “Qudsul- Yau” a wani harin da ta kai a zirin gaza. Islam Abed ta hadu da ajalinta a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan birnin gaza a jiya Lahadi da yamma. Wanda ya kara yawan yan jaridan da HKI ta kashe a wannan yakin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ‘Al-asksal Yau’ tana yin All..wadai da HKI, sannan ta kara da cewa, kissan Islam Abed ba zai kawo karshen rahotannin da yan jaridu suke aikawa duniya dangane da ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye ba. Haka ma ofishin tashar talabijin ta Al-aksa a...
    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.   Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa? NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya  a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya  bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
    Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya  bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa. A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan  Lahadin  cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na fadada Shirin da ake kira da Isra’ila Babba a cikin yankin kasashen Larabawa. Kasashen mambobi sun yi gargadin illar da wadannan buri ke ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya kara da cewa mambobin kawancen sun tsaya tsayin daka tare da al’ummar Palasdinu dangane da harin wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza, musamman yin Allah wadai da...
    Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...
      Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.   Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa za ta riƙa bai wa kowane masallacin Juma’a a jihar kuɗi daga Naira 300,000 zuwa 500,000 duk wata domin tallafa musu. Haka kuma gwamnatin za ta riƙa biyan limaman masallatan, na’ibansu da ladanai alawus na kowane wata domin sauƙaƙa wa hidimominsu. Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3 Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Mai magana da yawun gwamnatin, Abubakar Bawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce manufar shirin shi ne ƙarfafa karatun Alƙur’ani da koyar da ilimin addini ga yara da matasa a jihar. Gwamna Ahmed Aliyu, ya sanar da wannan mataki ne a ranar Asabar yayin...
    Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar. Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu Shugaban hukumar, Dokta Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a cibiyar hukumar da ke kan titin Aba Fatakwal, da yammacin ranar Lahadi.   Ƙarin bayani na tafe…
    Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno. A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan. Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja A Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri. Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin. Wannan farmaki ya...
      A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Amma Andrew na jihar Taraba, an kama shi ne a ranar Talata, 26 ga watan Agusta lokacin da jami’an NDLEA da hadin gwiwar jami’an Sojin Nijeriya, da Hukumar Tsaron Daji, da kungiyar matasan Mambila da ‘yan banga, suka kai farmaki a gonarsa mai fadin hekta 71.5 ta tabar wiwi da ke dajin Mayodoga, gundumar Mayosabere a karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba, inda suka lalata ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta? Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai. Manchester United na tsaka da sake gina kungiyar karkashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin kungiyar na Premier League. Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna kwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko wadanda duka kungiyar ta sayo a wannan kakar domin kara karfin...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin. Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin...
    Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi a kan birnin Gaza, tare da la’akari da shi a matsayin wani muhimmin mataki da ke kara habaka matsayar kasashen duniya na neman kawo karshen wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu. Kasashen da ake magana a kai su ne: Iceland, Ireland, Luxembourg, Norway, Slovenia, da Spain. Ministocin harkokin wajensu sun bayyana rashin amincewarsu da hare-haren wuce gona da iri kan...
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari. Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal. Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa. “Babban yayana...
    Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta hadin gwiwa, Dakta Goni Shetima,wanda shi horarwa ne ta bangaren tsarin TaRL,da Malam Abdulrahman Ibrahim Ado, kwararre jami’in ilimi na UNICEF, sun bayyana cewa tsarin an fara gudanar da shi a karamar hukumar Alkaleri. Kamar yadda suka ce, an fara tsarin ne da makarantu 190, ‘yan makaranta 10,865, sai kuma Malaman makarantar gwamnati 290. Shi ma darektan shiyya na hukumar (UBEC), wanda Abdulsalam Abubakar ya...
    Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar. A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor. Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata. Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya...
    Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18. Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas. A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma,...
    A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a tarurruka da kuma kafafen yana labarai na gwamnati. Wannan dai ya sami suka daga yan jarida wadanda suke ganin kundin tsarin mulkin kasar na kowa da kowa don haka hana kafafen yada labarai masu zaman kansu gudanar da tattaunawar bai dace ba. Hakama hana jamiyyun adawa, wadanda basa dasawa da gwamnati shima bai kamata ba. Sékou Jamal Pendessa na kungiyar yan jaridu a kasar ya...
    Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar. An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin. A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa. Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin. Editan BBC Hausa ya magantu...
    “A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar.   An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki.   Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi.   “Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani.  ...
    Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.”   Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.  ...
    A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin. “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.” Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin. Idris-Ahmad ya kuma yaba wa shugaban hukumar NDLEA na kasa, Tsohon Birgediya-Janar mai ritaya, Mohamed Buba-Marwa, bisa goyon baya da jagoranci da yake bayarwa. “NDLEA a Jihar Kano ta dage wajen aiwatar da manufarta ta kawar da miyagun kwayoyi a jihar, tare da gode wa hadin kai da goyon bayan jama’a wajen cimma wannan buri,” in ji shi. A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa...
    “Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi.   Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta. “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare,...
    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.   Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba.   Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
    Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke garin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta (JNIM) ta sanar a wasu jerin sakonni da ta fitar cewa,  ta kwace garin tare da kafa abin da ta kira tsarin shari’a musulunci. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto wasu jami’an yankin da suka tsere daga Farabougou na cewa yanzu haka garin na karkashin ikon kungiyar JNIM. A makon da ya gabata ne aka tilastawa sojojin ficewa daga sansaninsu da ke Farabougou, daya daga cikin sansanoni mafi girma a yankin, bayan wani hari da mayakan masu ikirarin jihadi suka kai musu. Tun daga...
    Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.   Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da yadda manya-,manyan kasashen duniya suka kyale HKI take yin abinda taga dama a kasar Falasdinu da ta mamaye. Kuma hakan zai sa kasashe da dama su kauravewa HKI. Labarin ya kara da cewa HKI a cikin shekaru kimani biyu da suka gabata, sun kashe falasdinawa fiye da dubu 62, amma MDD da kuma sauran kasashen yamma sun hana hatta shigar abinci a cikin zirin gaza....
    Ajayi-Kadri ya ce kungiyar ta yi cikakken nazari kan sake gabatar da harajin na FOB wanda ta tabbatar zai kara dagula lamura ne kawai da sake jefa masana’antu cikin mawuyacin hali.   “Gaskiyar lamarin ita ce, farashin kashi hudu cikin 100 na kamfanonin ya yi yawa fiye da yadda aka samu karin kashi bakwai cikin dari da kuma karin kashi daya cikin dari na harajin tsarin shigo da kayayyaki,” in ji shi.   Ya kara da cewa, a sauran kasashen yammacin Afirka kamar Ghana, Cote d’Iboire, da Senegal, ana tsare-tsaren da aka yi niyya ko tattara kudade a tsakanin kashi 0.5 zuwa kashi daya cikin 100 na FOB, tare da karin haraji kawai kan kayan alatu ko kuma wadanda ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanata Kabiru Garba Marafa tsohon ɗan Majalisar Dattawa da ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya jigo a Jam’iyar APC a jihar ya fice daga jam’iyar. Sanata Marafa ya bayyana ficewarsa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Jumu’a ya ce bayan tattaunawa da magoya bayansa sun cimma matsayar barin Jam’iyyar APC kan ta zalunce su. An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Ƙara Kuɗin Fasfo: Gwamnati na jefa ’yan Najeriya cikin matsi — Obi “Bayan mun yi waiwaye a shekara biyu da rabi da suka gabata mun gano cewa, APC a matakin ƙasa da jiha ta zalunce mu, a matakin jiha lalacewar jam’iyar ya kai matuƙa tun bayan kafa kwamitin riƙon...
    Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi.   Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin.   Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa.   “Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Obi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, inda ya ce wannan ƙarin ba adalci ba ne duba da halin matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta. “Wannan gwamnati kullum na ƙara jefa mutane cikin wahala a maimakon ta sauƙaƙa musu rayuwa,” in ji shi. “An ƙara kuɗin fasfo sau uku cikin shekaru biyu...
    Kungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi da mazabu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi.     —   Wannan sigar za ta fi ja hankalin masu karatu a yanar gizo. Kana so in ƙara ƙaramin taken ƙasa (sub-headline) da ke ƙara jan hankali, irin na jaridu, misali: “Tsohon Sanatan Ya Ce Zamfara Ta Fi Kowa Fama da Sace-Sace Amma Gwamnati T a Yi Watsi da Ita”?   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar.   Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi.   Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.   Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.   Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
    Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba.   Tabbas, muna jinjina masa kan yunkurin da yake ci gaba da yi na rage kalubalen rashin tsaro da Gwamnatin mai ci ta gada.   Amma mummunan harin da wasu mahara suka kai a watannin baya a yankin Yelwata, inda suka yi wa wasu al’umomin yankin kisan kiyashi da kuma harin da ‘yan bindiga suka kai kan Masallaci a garin Malumfashi ta Jihar Katsina, ba...
    Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna.   Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin.   A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa.   Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma,...
    Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce daga watan Junairu zuwa Yulin bana, darajar abubuwan da Sin ta shigo da su kasar daga kasashe masu karancin ci gaba na Afrika, ta kai dala biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 kan na bara.   Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, inda ta ce wani rahoto da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, karkashin jagorancin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ya zama wani muhimmin karfi mai ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar. Ta ce cinikayya tsakanin...
    Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci.   Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun  DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi. A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki  wadanda ake sarrafasu daga nesa. Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa...
    Shugaban gamayyar masu goyon bayan Gwagwarmaya a kasar Lebanon suna tare da kungiyar sannan wadanda suke nanata cewa sai an takaita makamai a hannun gwamnati sun aiki ne wa HKI da Amurka . Tashar talabijan ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto shugaban gamayyar Mohammad Ra’ad yana fadar haka ya kuma kara da cewa abinda ya faru a ranar 5 ga watan Augustan mai karewa wani kuskure ne wanda gwamnatin kasar Lebanon bata taba irinsa ba. Kuma yana dai da kamar abinda ya faru a karbala ne, inda wani sojan yazid ya fadawa yan uwansa kan cewa ku shaida mani wanin nYazid kann cewa ni na fara harban kibiya kan Al-Hussain. Abinda gwamnatin kasar Lebanon tayi na neman yardar Amurka da...
    Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma. ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar. Ambaliyar...
    “A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan.   Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar.   Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin...
    3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka. Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci. Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na...
    Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025. A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne. Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar “A yanzu duk fasfo mai shafi 32 ya koma N100,000 wanda zai yi shekara biyar kafin ya daina aiki, yayin da mai shafi 64 da zai shekara 10 ya koma N200,000,” in ji sanarwar. Sai dai sanarwar ta ce har yanzu kudaden da...
    Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki tun daga ranar 19 ga Oktoban shekara ta 2023. Jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila sun bayyana bangaren Yemen a matsayin “wanda ya fi kowa hauka a yankin,” suna masu gargadin cewa shiga fafatawar da suke yi da su zai haifar da mummunan sakamako ga haramtacciyar kasar Isra’ila, ganin yadda suke ganin dakarun Yemen...
    Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya. Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa. Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu. Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin...
    A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya. Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa. Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu. Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin...
      Bikin CIFTIS na bana, zai kunshi nune-nune daga kasashe, da hukumomin kasa da kasa sama da 70. Kuma kusan kamfanoni 2,000 ne suka shirya shiga bikin a zahiri. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19. Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta, 2025. ’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan kasuwa a Kaduna ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Sarkin ɗan ƙasar Amurka ne, da ke zaune a Ohio. Bayan ya fito daga gidan yari, zai yi shekara uku ƙarƙashin kulawa, sannan dole ne ya biya sama da dala miliyan 4.4. Kotun ta kuma ƙwace gidansa da ke Ohio da...
    Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19. Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta, 2025. ’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan kasuwa a Kaduna ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Sarkin ɗan ƙasar Amurka ne, da ke zaune a Ohio. Bayan ya fito daga gidan yari, zai yi shekara uku ƙarƙashin kulawa, sannan dole ne ya biya sama da dala miliyan 4.4. Kotun ta kuma ƙwace gidansa da ke Ohio da...
    Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar tun shekara ta 2023 da ta gabata Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar a ranar Talata, tun bayan barkewar yaki a kasar a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023. Kamfanin dillancin labaran Sudan ya bayar da rahoton cewa, “Gwamnatin bege” karkashin jagorancin fira ministan kasar Kamil Idris, “ta tattauna, a zamanta na farko na hukuma a birnin Khartoum bayan kafuwarta, game da tsare-tsaren ma’aikatun na wannan shekara, inda suka mai da hankali kan ayyukan jama’a da rayuwar jama’a, tsaro na ‘yan kasa, sake gina kasa, da tabbatar da dawowar ‘yan kasar da suka yi gudun hijira bisa radin kansu....
    Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa NRC ta dakatar da jigilar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja Rahotanni sun ce an kai harin ne wajen misalin ƙarfe 3:00 na daren Litinin inda maharan suka sace magidancin mai suna Malam Anas tare da matarsa mai suna Halimatu ​​da ’yarsa. Bayanai sun kuma nuna wani dan bangar da yayi ƙoƙarin kai musu ɗauki ya rasa...
    Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni. A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi. Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa. Ta sha alwashin cewa...
    Cutar kwalara ta ɓarke a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a Jihar Zamfara, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai tare da kwantar da kusan mutum 200 a asibiti. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa. Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaɗuwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune. Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba. Daga...
    Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.   A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.”   Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan.   Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
    Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi. A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban. A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a watan Satumban bara a Beijing, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakarsu. Firaminista Li ya ce yana fatan...
    Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci.   A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa: “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.”   Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo...
    A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing.   Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano. Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida. Hisbah ta haramta al’adun gargajiya yayin bukukuwan aure a Bauchi Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Bayanai sun ce an yi arba da gawar Fatima Sulaiman rataye a jikin wata taga a cikin gidansu, lamarin da ya jefa shakku da ayoyin tambaya kan musabbabin mutuwarta. Aminiya ta zanta da mahaifiyar marigayiyar, Malama Madina Inuwa Makwalla, wadda ta bayyana ganawa ta ƙarshe da ta yi da...
    Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
    A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin bikin Ranar Hausa ta Duniya. Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasaitaccen bikin ke gudana.                      
    Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Kakaba yunwa ga dukkan al’umma laifi ne da ya wajaba a dakatar da ita nan take Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce yunwar da al’ummar zirin Gaza suke ciki wani laifi ne da ya zama dole a dakatar da ita nan take. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Macron ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya litinin ya tattauna da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani game da mummunan halin da ake ciki a Gaza. Ya ci gaba da cewa, “Suna aiki kafada da kafada da Qatar don tabbatar da nasarar kokarin masu shiga tsakani da kuma shirya taron kan abin da ya...
    Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
    Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari. Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage… Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana. Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani....
    Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba. Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Albarkacin taron koli na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) na 2025, an yi bikin kaddamarwa na kasashen SCO, da shiri mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ta shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing. Tun daga yau, za a fara watsa shirin a manyan gidajen talibijin na Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Pakistan, Iran, da Belarus da sauransu. Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, shirin ya zabi labarai masu ban sha’awa na yadda Shugaba Xi Jinping ke kula da al’adu da ci gabansu, don bayyana muhimman ra’ayoyinsa game da al’adu. A karkashin ruhin “Shanghai”, za a ci gaba da rubuta sabon labari na hadin kai da rabon makoma tsakanin al’adu, tare da kafa kyakkyawar makoma ta bil’adama...
    Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025. Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina. Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin. Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa...
    Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan Isra’ila da aka mamaye. Waɗannan tashoshi na yahudawan sahayoniyya sun yi imani cewa; Da’awar iya dakile hare-haren sojojin Yemen kan yankunan Isra’ila, rudu ne kawai na jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ganin tsawon lokacin da   za a iya dauka domin hana kai waɗannan ayyuka saboda “haɗarinsu.” Tashar talabijin ta yahudawa ta 13 ta yarda cewa harin na baya-bayan nan da aka kai kan kasar Yemen ba...
    A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II.   Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya. Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu. Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba...