Aminiya:
2025-11-18@13:47:42 GMT

Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza

Published: 3rd, October 2025 GMT

Sojin Isra’ila sun kame dukkan jerin jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji da ke ƙoƙarin shiga Zirin Gaza, inda suka kama daruruwan masu kai agajin tare da ɗaruruwan jiragen.

Bidiyon da ken una tafiyar jiragen kai tsaye ya nuna yadda sojojin Isra’ila suka kutsa cikin jirgin ƙarshe da safiyar Juma’a.

Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko

Jirgin Marinette mai tutar ƙasar Poland, wanda ke da ma’aikata shida, shi ne jirgin ƙarshe daga jerin Global Sumud Flotilla, wanda a baya ya ƙunshi jirage 44, da Isra’ila ta kama.

Kwamitin Ƙasa da Ƙasa na Ƙoƙarin Karya Takunkumin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama sun fara yajin cin abinci na sai baba ta gani tun daga lokacin da aka tsare su.

A wata hira ta bidiyo da aka yi da masu shirya tafiyar a daren Alhamis, shugaban jirgin daga ƙasar Australia, wanda ya bayyana kansa da suna Cameron, ya ce jirgin ya samu matsala da injinsa a farko, wanda ya sa ba ya tare da sauran jiragen.

Ya ƙara da cewa jirgin yanzu yana kan hanyar zuwa Gaza.

“Muna da wasu Turkawa a cikin jirgin … akwai wata mata daga Oman da ni kaina, kuma za mu ci gaba da tafiya,” in ji shi.

Bidiyon kai tsaye daga jirgin, wanda ke aiki tun ƙarfe 04:00 GMT, ya nuna ma’aikatan jirgin suna jan jirgin yayin da rana ke fitowa a cikin ruwa na ƙasa da ƙasa a Tekun Bahar Rum.

Na’urar bin sawu ta nuna cewa jirgin yana kimanin mil 43 na ruwa (kimanin kilomita 80) daga iyakar ruwan Gaza.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila ta riga ta gargadi Marinette cewa “ba za ta bar ƙoƙarin shiga yankin da ake fafatawa da kuma karya takunkumi ba.”

Tun daga ranar Laraba, rundunar ruwa ta Isra’ila ta dakatar da ɗaruruwan jiragen ruwa da ke ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza, inda ta kama kusan masu fafutuka 500 daga ƙasashe fiye da 40.

Isra’ila ta zargi masu aikin agaji da ƙoƙarin “karya takunkumin ruwa na doka” — zargi da ke sabawa dokar ƙasa da ƙasa — kuma ta ce za ta yi duk mai yiwuwa don dakatar da su.

Rundunar ruwa ta Isra’ila ta kama dukkan jiragen da ma’aikatansa kafin ta tura su zuwa Isra’ila, daga inda za a fitar da su.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai fitattun mutane kamar Greta Thunberg, tsohuwar magajin garin Barcelona Ada Colau, da mamba a Majalisar Tarayyar Turai Rima Hassan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda.

’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS

Kwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP.

PRNigeria ta ruwaito cewa, kafin rasuwarsa, kwamandan ya aike da wani bidiyo ga manyansa yana bayyana irin nasarar da tawagarsa ta samu a wani farmaki da suka kai.

Sai dai bayan haka ne ISWAP ta bibiyi wurin da yake ta katse sadarwa, sannan ta kama shi.

Rahotanni sun ce mayaƙan sun kama shi ne da ransa, inda bayan sun yi masa tambayoyi, daga bisani kuma su kashe shi.

Da farko dai rundunar sojin Najeriya ta ce kwamandan yana cikin ƙoshin lafiya bisa hujjar bidiyon da ya aika yana tabbatar da irin nasarar da suke samu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta bayyana batun cafke kwamandan nata a matsayin “ƙazon kurege”, tana mai cewa duk da “harbe-harbe masu tsanani” da suka fuskanta daga mayaƙan yayin dawowarsu daga sintiri a gefen Sambisa, an yi nasarar tsira da kwamandan.

Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jami’an sa-kai biyu a harin, amma ta ce kwamandan ba ya cikin waɗanda aka kama.

Sai dai daga bisani, wasu rahotanni na PRNigeria da jaridar PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP sun kama kwamanda ne bayan ya yi ɓata hanya yayin guje wa harin farko.

ISWAP ta yi iƙirarin kashe kwamandan

A wata sanarwa cikin harshen Larabci da ISWAP ta wallafa ranar Litinin a jaridarta mai suna Amaq, ta nuna hoton kwamandan a lokacin da ya ke hannunta, yana fama rauni har jini na zuba a kafarsa.

Ƙungiyar ta ce: “Mun kama kwamandan rundunar Najeriya bayan ya tsere daga harin Wajiroko, daga nan muka yi masa tambayoyi sannan muka kashe shi.”

Ƙungiyar ta kuma yi wa rundunar sojin Najeriya gugar zana, tana mai bayyana bayanan farko da ta fitar a matsayin “ƙarya tsagwaronta da ke tabbatar da gazawarta.”

Kawo yanzu dai Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan yadda aka bar kwamandan cikin haɗari bayan tserewa daga harin farko.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
  • Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
  •  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Fi Sayarwa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza