Gwamnan Gombe Ya Taya Al’umma Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 65 Da Samun ‘Yancin Kai
Published: 2nd, October 2025 GMT
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM).
Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin kiwon lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa, tsaro, noma, masana’antu, da gyara harkokin mulki.
Ya bayyana cewa, an gina tituna sama da kilomita 900 a dukkan kananan hukumomin, da yawa da fitulun titi masu amfani da hasken rana, yayin da aka inganta cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu, an gina karin ajujuwa da daukar malamai.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta biya sama da Naira biliyan 25 tare da biyan basussukan fensho da aka dade ana bin su tun a shekarar 2012. Ya kuma kara da cewa an samu ci gaba wajen magance matsalolin muhalli da bunkasar tattalin arziki ta hanyar hada-hadar noma da kiwo.
Ya yi alkawarin ci gaba da karfafa wa matasa gwiwa, da tallafa wa manoma, da kuma inganta rayuwar mazauna yankin baki daya, inda ya bukaci ‘yan kasar da su kasance da hadin kai da hakuri yayin da ake samun sauye-sauyen tattalin arziki.
A matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi murna da farin ciki da ci gaban da kasar ta samu, kuma su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da wadata.
HUDU Shehu/Gombe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing November 16, 2025
Daga Birnin Sin Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30 November 16, 2025
Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan November 15, 2025