Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla
Published: 2nd, October 2025 GMT
Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen Ruwan, sannan kuma suka killace su.
Baya ga haka kuma sun kama dukkanin mutanen da suke cikin wasu jiragen sun tafi da su.
Sanarwar ta ce, kyamarorin da ke cikin jirgin sun samu matsala, sannan sojojin Isra’ila sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka umurci jiragen da su karkata zuwa tashar jiragen ruwa ta Asdod da ke karkashin ikon su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun ayyana dokar ta baci kan jiragen ruwa, tare da dakile hanyoyin sadarwa da kuma kakkabe kyamarorin sa ido. An rasa hanyoyin tuntuɓar jiragen ruwa da dama, yayin da aka gano nakiyoyin sojan ruwa guda huɗu a kusa da wurin, kuma an ga jiragen yaƙin Isra’ila fiye da 20 sun kewaye su.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa sojojin ruwan kasar sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka kwace jiragen ruwan Alma da Sirius tare da kame wadanda suke a cikinsu.
Masu fafutuka daga kasashe 44 ne suka shiga cikin wannan tawaga wadda ta hada mutane fiye da 500, da suka hada da ‘yan siyasa da kuma fitattun mutane masu fafutuka a duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD October 2, 2025 Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza. October 1, 2025 Iran Ta yi Kira Da A Gaggauta Kakabawa HKI Takunkumi October 1, 2025 A yau Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun yancin kai October 1, 2025 Aragchi: Za’a Fara Tattaunawa Ta Karshe Dangane Da Shirin Snapback October 1, 2025 Tinubu: Na Gaji Rusashen Tattalin Arziki A Sanda Na Karbi Ikon Kasar October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila sun jiragen ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin.
Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance.
Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya ƙara da cewa “hawa da suka yi cikin gaggawa ya sa gadar da suka gina a kan wani rami da ambaliyar ruwa ta mamaye ta ruguje.”
Jami’in ya bayyana cewa zuwa yanzu ƙungiyoyin ceto sun gano gawawwaki 32 daga cikin tarkacen, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci