Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148
Published: 2nd, October 2025 GMT
Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.
Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza.
A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana wadanda abin ya shafa na ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, inda motar daukar marasa lafiya da ma’aikatan agaji suka kasa isa gare su, sakamakon tarin baraguzan gine-gine da kuma hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaddamarwa.
Bugu da kari, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe wasu Falasdinawa hudu tare da jikkata wasu 57 sakamakon harin da ‘yan ta’addan suka kai kan masu neman agaji, lamarin da ya kai adadin mutanen da suka yi shahada a fafutukar neman abinci zuwa 2,580 da kuma jikkatar wasu sama da 18,930.
A cikin wannan lokaci, ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta ba da rahoton shahadar mutane biyu a sakamakon kamuwa da matsananciyar yunwa da Isra’il ta haifar a yankin, daga cikinsu har da wani yaro. Wannan ya Sanya adadin wadanda yunwa ta kashe ya karu mutane 455, ciki har da yara 151.
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya kuma tabbatar da cewa ikirarin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi game da ba da izinin zirga-zirgar ‘yanci zuwa kudu tsabar karya ce da kuma kokarin wawantar da duniya domin boye gaskiyar abin da yake faruwa na ayyukan yakin da take tafkawa a kan mazauna yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza. October 1, 2025 Iran Ta yi Kira Da A Gaggauta Kakabawa HKI Takunkumi October 1, 2025 A yau Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun yancin kai October 1, 2025 Aragchi: Za’a Fara Tattaunawa Ta Karshe Dangane Da Shirin Snapback October 1, 2025 Tinubu: Na Gaji Rusashen Tattalin Arziki A Sanda Na Karbi Ikon Kasar October 1, 2025 Iran: Dakarun Ruwa Na Iran A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Kowa Don Kare Kasa October 1, 2025 Pezeshkiya: Aiki Ta Kasar China Yana Da Matukar Muhimmanci Musamman A Wannan Halin Da Ake Ciki October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: adadin wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza
Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza.
An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na hadin guiwa da zai hada da mafiyawancin daga kasashen musulmi da zai kunshi kasashen Masar, Indonesia, da kuma kasar Azarbaijan,
Kungiyar Hamas ta yi watsi da wannan kuduri da zai kunshi dakarun kasada kasa domin baya wakiltar hakkokin falasdinawa kuma an yi shi ne domin kwabe dammarar dakarun gwagwarmayar neman yancin falasdinu.
Haka zalika ta kara da cewa kudurin bai kunshi bukatun siyasa da taimakon jinkai da kuma hakkokin alummar falasdinu ba, don haka cewa duk wani sojan kasa da kasa da zaa aika zuwa iyakar gaza ne kawai, domin sa ido kan yadda ake aiki da dakatar da bude wuta karkashin kulawar majalisar dinkin duniya.
Sai dai kasashen rasha da china sun kada kuriar nuna rashin amincewa da kudurin na Amurka .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza November 18, 2025 Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci