DRC : An yanke wa Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa
Published: 2nd, October 2025 GMT
Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23.
An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar.
An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo.
Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan kiran yaki (a manyan lardunan Goma da Bukavu).
Kabila ya mulki kasar ta Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, daga shekarar 2001 zuwa 2019, amma yana rayuwa ne a Afrika ta Kudu tun daga shekarar 2023.
Amma a farkon wannan shekarar, ya bayyana a gaban jama’a a gabashin Congo tare da bayyana muradinsa na komawa gida don “ba da gudumawar neman mafita” kan rikicin da ake ciki yanzu.
Gabashin Congo ya fuskanci daya daga cikin rikice-rikice mafi dadewa a Afirka.
Tun daga watan Janairu, lamaran tsaro sun tabarbare sosai, inda aka sake samun barkewar fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen M23, wadanda suka kwace wasu muhimman yankuna da suka hada da Goma da Bukavu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta kashe Falasdinawa 44 a ranar Laraba October 2, 2025 Iran ta bukaci a gaggauta kakaba wa Isra’ila takunkumi kan kisan kiyashin Gaza October 2, 2025 Mohajerani: Iran ba ta maraba da yaki amma ta shirya don kare kanta October 2, 2025 Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla October 2, 2025 Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD October 2, 2025 Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza. October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain
A karon farko an yi wani wasan kwallon kafa na sada zumunci da ba a saba gani ba tsakanin ‘yan wasan Basque, da Falasdinu a Spain.
Masu shirya wasan sun ce kimanin ‘yan kallo 50,000 ne suka samu tikitin shiga a filin wasa na San Mames, gidan Athletic Bilbao.
Masoya da yawa sun daga tutocin Falasdinawa, da kuma tutocin yankin arewacin Basque Country.
Duk da cewa an fitar da Falasdinu a zagaye na farko na gasar cin kofin duniya na 2026, wanda za a gudanar a watan Yuni da Yuli a Canada, Amurka, da Mexico, ana ganin murza leda da Falasdinun ta yi a Turai a matsayin mai matukar tasiri idan aka waiwaiyi yakin da Isra’ila ta kwashe tanayi a Gaza da kuma yadda duniya ke cigaba da amincewa da falasdinu a matsayin kasa.
Falasdinu ta sha kashi da ci 3-0 amma babban abin da ke gabanta shi ne haskawa a idon duniya bayan da wasu kasashen turai suka amince da ita bayan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba.
Shekaru shida kenan da Falasdinawa basu buga wasa gida ba.
Tun soma rikicin, Isra’ila ta lalata filayen wasa kusan 289,” a cewar majiyoyi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana November 15, 2025 Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu. November 15, 2025 M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci