Isra’ila ta kashe Falasdinawa 44 a ranar Laraba
Published: 2nd, October 2025 GMT
Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya.
Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke birnin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu da dama, wasu ma sun makalle a karkashin baraguzan gine-gine.
Wasu mutane 11 kuma sun yi shahada, sannan wasu da dama sun jikkata a harin bam din da aka kai a makarantar Al-Falah da ke unguwar Al-Zeitoun a kudu maso gabashin wannan birni. Makarantar tana dauke da iyalai da suka yi gudun hijira.
A wani labara na daban Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta sanar cewa Sojojin Isra’ila na kashe akalla Falasdinawa 100 a kowace rana a zirin Gaza, ciki har da wadanda ke mutuwa saboda yunwa da rashin kula ta lafiya.
tun daga watan Oktoban shekarar 2023, Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 66,100, akasari mata da kananan yara sakamakon kisan kare dangin da takeyi a Gaza.
Ana ci gaba da kokarin tsagaita bude wuta da kuma cimma yarjejeniyar zaman lafiya don sake gina Gaza, a wani bangare na wani shiri mai dauke da kudurori 20 da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a ranar Litinin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bukaci a gaggauta kakaba wa Isra’ila takunkumi kan kisan kiyashin Gaza October 2, 2025 Mohajerani: Iran ba ta maraba da yaki amma ta shirya don kare kanta October 2, 2025 Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla October 2, 2025 Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD October 2, 2025 Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza. October 1, 2025 Iran Ta yi Kira Da A Gaggauta Kakabawa HKI Takunkumi October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba.
“Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin.
A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afrika ta kudu a cikin wata sanarwa.
A halin yanzu, ofishin jakadancin Falasdinu a Afirka ta Kudu ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa ‘yan Falasdinu 153 sun iso ba tare da wata sanarwa ko hadin gwiwa ba.
An bayyana cewa wata kungiyar mayaudara ce ta shirya jirgin.
Ofishin jakadancin ya ce kungiyar ta yi amfani da mummunan halin jin kai na al’ummar Gaza, ta yaudari iyalai, ta karbi kudi gare su, ta samar musu tafiyar ta hanyar da ba ta dace ba, saidai kungiyar agaji ta Gift of the Givers, ta shaida wa tashar talabijin ta Afirka ta Kudu SABC cewa Isra’ila ce ke da alhakin shigar ‘yan gudun hijirar Falasdinawa cikin kasar ba bisa ka’ida ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci