Iran: Dakarun Ruwa Na Iran A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Kowa Don Kare Kasa
Published: 1st, October 2025 GMT
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun,
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa na sojojin kasar da kuma na rundunar IRGC a lardin Hurmuzgan.
Musawi ya ganewa idanunsa makamai na kariya da kuma na kai hare-hare kan makiya wadanda rundunonin ruwa a bangarorin biyu suke da shi da kuma lafiyar sojojin, inda ya bayyana amincewar sa da shirye-shiryen nasu.
Musawi ya kara da cewa daga karshen kallafeffen yakin kwanaki 12 wanda HKI da kuma Amurka suka dorawa kasar a cikin watan yunin da ya gabata. An gabatar da sauye sauye da kuma shirye-shirye masu muhimmanci a cikin sojojin ruwa na kasar, wanda ya kara karfin sojojin.
Musavi har’ila yau ya ziyarci banganen dakarun IRGC na ruwa, inda ya ganewa idanunsa irin tanajin da suke ciki don fuskantar duk wata barazana daga makiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkiya: Aiki Ta Kasar China Yana Da Matukar Muhimmanci Musamman A Wannan Halin Da Ake Ciki October 1, 2025 Tawagar Jiragen ‘Assumud’: Yahudawan Isra’ila Sun Kai Mana Hare-Hare Da Safe October 1, 2025 Shahadar Nasrallah Ta Gadar Da Juriya A Kan Gwagwarmaya Ga Al’ummomi Masu ‘Yanci October 1, 2025 Muhammad ElBaradei Ya Yi Kakkausar Suka Ga Shirin Trump Akan Gaza October 1, 2025 Trump Ya Bayar Da Umarnin Aike Wa Da Jiragen Ruwa Na Nukiliya Zuwa Kusa Da Rasha October 1, 2025 Gaza: ‘Yan Gwagwarmaya Suna Ci Gaba Da Kai Wa Sojojin Mamaya Hare-hare October 1, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwa Da Ya Nufi HKI October 1, 2025 Pezeshkian: Iran Zata Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kawo Zaman Lafiya A Duniya September 30, 2025 Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Hari Kan Iran Gwajin Karfinta Ne A Fagen Kimiyya Da Fasaha September 30, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Ana Musayar Sakonni Tsakanin Kasar Iran Da Amurka September 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
Tankar yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bude wuta akan dakarun zaman lafiya na MDD dake kudancin Lebanon
Dakarun zaman lafiyar na MDD dake kudancin Lebanon (UNIFiL) sun sanar da cewa tankar yakin “Isra’ila” ta buder wuta akansu, da hakan ya tilasta musu guduwa zuwa inda za su buya.
Rundunar ta “UNIFIL” ta kuma bayyana abinda ya faru da cewa keta kudurin MDD ne mail amba 1701, tare da yin kira ga “Isra’ila’ da ta dakatar da abinda take yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da dakarun zaman lafiyar na MDD suke keta kudurin MDD ta hanyar kai hare-hare da kuma yin kutse a cikin yankunan dake kan iyaka.
A ranar 27 ga watan Oktoba ma dai rundunar ta MDD ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin sama maras matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ya rika shawagi akan sojojinta masu sintiri da zummar kai musu hari. Haka nan kuma a waccan ranar wani jirgin saman maras matuki na “Isra’ila” ya jefa bom a kusa da dakarun a garin Kafar-kalla.
A baya a ranar 12 ga watan Oktoba wani jirgin na “Isra’ila” da ya jefa bom, ya jikkata daya daga cikin dakarun zaman lafiyar na MDD.
An kafa rundunar UNFEL ne dai a 1978 bayan da sojojin Haramtacicyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin kudancin Lebanon, an kuma karfafa ayyukan rundunar a 2006 da fitar da kuduri 1701. Da akwai sojoji 10,000 akarkashin wannan rundunar domin sa ido akan dakatar da yaki daga Isra’ila da kuma karfafa sojojin Lebanon a kudancin tafkin “Litani”.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci