HausaTv:
2025-11-18@12:31:44 GMT

Gaza: ‘Yan Gwagwarmaya Suna Ci Gaba Da Kai Wa Sojojin Mamaya Hare-hare

Published: 1st, October 2025 GMT

Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai  hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’

Rundunonin soja na  “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza.

A jiya Talata dakarun na Kassam sun watsa sanarwar a shafinsa na “Telegram’ da a ciki ya kunshi cewa, sun kai hare-haren ne akan ‘yan mamaya a kusa asibitin Jordan da kudancin unguwar “Tal Hawa” a kudancin birnin Gaza.

Haka nan kuma rundunar ta Kassam ta ce ta kai wani harin akan motar soja da ta shiga cikin wata makaranta ta ” Rahibatul-Wurdiyyah” dake Tallul-Hawa.”.

Har ila yau dakarun na Hamas sun ce, sun yi fada gaba da gaba da sojojin HKI tare da kashe da kuma jikkata adadi mai yawa.

Bugu da kari sun tarwatsa wata tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar dasa mata abubuwa masu fashewa.

An ga jiragen sama masu saukar angulu sun sauka a yankin domin daukar gawawwaki da wadanda su ka jikkata.

 Ita kuwa rundunar ” Sarayal-Qudus” ta jihadul-Islami ta sanar da kai nata hare-haren ne akan sojojin mamaya a arewacin birnin Gaza.

Haka nan kuma sun yi amfani da makamai mai linzami samfurin GBU da ‘yan mamaya su ka bari a Gaza, tare da tarwatsa shi akan sojojin HKI a kan titi na 8 dake kudancin Gaza. A can ma an ga jirgin sama mai saukar  Angulu yana jigilar wadanda su ka jikkata da halaka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwa Da Ya Nufi HKI October 1, 2025 Pezeshkian: Iran Zata Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kawo Zaman Lafiya A Duniya September 30, 2025 Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Hari Kan Iran Gwajin Karfinta Ne A Fagen Kimiyya Da Fasaha September 30, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Ana Musayar Sakonni Tsakanin Kasar Iran Da Amurka September 30, 2025 Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu September 30, 2025 Ambaliyar Ruwa Ya Yi Barna A Sassan Sudan Tare Da Kara Janyo Matsalolin Jin Kai A Kasar September 30, 2025 Hamas : Shirin da Trump ya gabatar yana “Kusa da Hangen Isra’ila” September 30, 2025 Isra’ila : Netanyahu na shan suka bayan ya nemi afuwar Qatar September 30, 2025 Araghchi ya gana da sakatare janar na MDD September 30, 2025 Madagascar : Shugaba Rajoelina ya sanar da korar daukacin gwamnatinsa September 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon

 Tankar yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bude wuta akan dakarun zaman lafiya na MDD dake kudancin Lebanon

Dakarun zaman lafiyar na MDD dake kudancin Lebanon (UNIFiL) sun sanar da cewa tankar yakin “Isra’ila” ta buder wuta akansu, da hakan ya tilasta musu guduwa zuwa inda za su buya.

Rundunar ta “UNIFIL” ta kuma bayyana abinda ya faru da cewa keta kudurin MDD ne mail amba 1701, tare da yin kira ga “Isra’ila’ da ta dakatar da abinda take yi.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da dakarun zaman lafiyar na MDD suke keta kudurin MDD ta hanyar kai hare-hare da kuma yin kutse a cikin yankunan dake kan iyaka.

A ranar 27 ga watan Oktoba ma dai rundunar ta MDD ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin sama maras matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ya rika shawagi akan sojojinta masu sintiri da zummar kai musu hari. Haka nan kuma a waccan ranar wani jirgin  saman maras matuki na “Isra’ila” ya jefa bom a kusa da dakarun a garin Kafar-kalla.

A baya a ranar 12 ga watan Oktoba wani jirgin na “Isra’ila” da ya jefa bom, ya jikkata daya daga cikin dakarun zaman lafiyar na MDD.

An kafa rundunar UNFEL ne dai a 1978 bayan da sojojin Haramtacicyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin kudancin Lebanon, an kuma karfafa ayyukan rundunar a 2006 da fitar da kuduri 1701. Da akwai sojoji 10,000 akarkashin wannan rundunar domin sa ido akan dakatar da yaki daga Isra’ila da kuma karfafa sojojin Lebanon a kudancin tafkin “Litani”.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya  November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza
  • ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
  • Kwamitin tsaron MDD zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza
  • Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar
  • An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya  
  • Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
  • Sanusi ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso