Pezeshkian: Hadin gwiwar Iran da Saudiyya zai zama abin koyi ga dukkanin kasashen yankin
Published: 18th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman da tawagarsa a birnin Tehran, bayan da ministan na Saudiyya ya isa babban birnin kasar Iran domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin da alakar kasashen biyu.
Shugaban na Iran ya jaddada zurfafa dangantakar addini da al’adu da tarihi a tsakanin kasashen musulmi, yana mai jaddada wajabcin karfafa hadin kai a duniyar musulmi.
Shugabar kasar ta Iran ya ce: al’ummar Saudiyya ‘yan uwanmu ne, kuma tun farkon kama aikin gwamnatinmu, mun yi kokarin karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin dukkanin kasashen musulmi. Ya kara da cewa, idan kasashen musulmi suka cimma matsaya ta bai daya da hadin kai na hakika, to gwamnatin yahudawan sahyoniya ba za ta sake haifar da bala’i irin na kisan bil’adama a yankin ba kamar yadda suke yi yanzu a zirin Gaza.
Ya kuma tabo batun muhimmancin ajiye bambance-bambance a gefe, da inganta hadin gwiwa a yankin.
Pezeshkian ya jaddada cewa, “Shugabannin kasashen musulmi za su iya yin aiki tare, kuma su gabatar da wani abin koyi na rayuwa tare, da wadata, da ci gaba ga sauran al’ummomi na duniya.
Ya kuma yaba da ra’ayin kafa kungiyoyin aiki na hadin gwiwa a bangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziki da tsaro tsakanin Iran da Saudiyya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar.
Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a.
’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin suShugaban Sashen bayar da Agaji na Ƙaramar Hukumar, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula, amma bai bayar da cikakkun bayani ba.
Sai dai a cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Abubakar Usman, ya ce bayan samun bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a yankin.
Sai dai ya ce makarantar da abin ya shafa ta ƙi bin umarnin ta kuma buɗe makarantar.
“Gwamnatin Jihar Neja ta yi matuƙar bakin ciki da labarin sace ɗaliban makarantar St. Mary da ke Ƙaramar Hukumar Agwara. Har yanzu ba a tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace ba yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tantance lamarin.
“Jihar ta samu bayanan sirri tun da farko da ya nuna ƙaruwa barazanar tsaro a wasu sassan yankin arewa.”
“A kan haka ne Gwamnatin jiha ta bayar da umarnin dakatar da dukkan ayyukan gine-gine tare da rufe dukkan makarantun kwana a yankin da abin ya shafa a matsayin kandagarki
“Sai dai makarantar St. Mary ta ci gaba da zama a buɗe da ci gaba da karatu ba tare da sanarwa ko neman izini daga gwamnati ba.”
“Jami’an tsaro sun riga sun fara cikakken bincike da aikin ceto domin tabbatar da an dawo da ɗaliban gida lafiya.”
“Gwamnatin Jihar Neja tana aiki kai tsaye da dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa kuma za ta ci gaba da bayar da rahotanni yayin da bayani kara fitowa.”
“Gwamnati na kira ga masu makarantu, shugabannin al’umma, da duk masu ruwa da tsaki da su bi ƙa’idojin tsaro da aka bayar domin kare rayukan jama’a. Kariya ga rayuka, musamman na ’ya’yanmu, ita ce babban abin da wannan gwamnatin ta sa a gaba,” in ji shi.
A Jihar Kwara makwabciyar Nejan, gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantu fiye da 50 a kananan hukumomi hudu sakamakon sake ƙaruwar hare-hare a yankunansu.