Fani-Kayode ya zargi Isra’ila da Hannu a tashe-tashen hankula a Najeriya
Published: 18th, April 2025 GMT
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci.
Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar 2015, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan tashin hankali.
“Haka aka shirya a shekarar 2014 kafin a kayar da Goodluck Jonathan, yanzu kuma sun fara shirin irin haka domin tunkarar 2027,” in ji shi. “Mun san su wane ne, kasashen waje ne daga cikinsu har da kasashen Yamma da Isra’ila, da wasu da dama. Ba sa son kwanciyar hankali a Nijeriya.” In ji Femi Fani-Kayode.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Fani Kayode
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya Bayyana Yadda Iran Da Mayar Da Martani Mai Gauni Kan Isra’ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Mayar da martanin Iran ga ‘yan sahayoniyya sun murkushe girman kan makiya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Martanin da Iran ta mayar wa yahudawan sahayoniyya a lokacin arangamar da suka yi a baya-bayan nan abin nuni ne, domin kuwa a duk tsawon tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta taba samun irin wannan martanin mai gauni ba.
Ghalibaf, wanda ya karbi bakwancin jakadan Belarus a birnin Tehran, Dmitry Kaltsov, a jiya Laraba, ya yaba da matakin da gwamnatin Belarus ta dauka dangane da hare-haren da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauika na kai wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran hare-haren wuce gona da iri. Yana mai cewa, hare-haren da suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasar Iran na daga cikin munanan ayyukan da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka aikata, idan aka yi la’akari da kasancewar Iran mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta NPT da kuma yadda ayyukan kasarta suke gudana karkashin kulawar hukumar ta kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta IAEA.
Shugaban Majalisar Shawarar Musuluncin ya kuma jaddada cewa: A lokacin da aka kai wa Iran hari mahukuntan ta suna gudanar da shawarwari ne da Amurka kan batun shirin, har ma an sanya ranar da za a yi shawarwarin zagaye na shida. Ya kara da cewa: A cikin irin wannan yanayi, Iran ta ga irin yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai wa Iran hari, yayin da a baya ta yi gargadin cewa, za ta mayar da martani mai karfi kan masu wuce gona da iri a duk wani harin da aka kai kan yankin kasarta. A kan haka, duniya ta shaida yadda Iran ta mayar da martani kan hare-haren wuce gona da irin gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka.