Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
Published: 18th, April 2025 GMT
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani.
Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don tallafa wa kasashen yankin manyan tabkuna wajen magance tushen matsalolin da ke haifar da gazawar shugabanci da rashin daidaituwar ci gaba a yankin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin.
Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda iyaye ke bada hadin kai da goyan baya ga shirin.
Ya kuma ja hankalin ma’aikatan rigakafin da su sanya kishi da kwazo wajen samun nasarar aikin.
A sakon da ya aike da shi a taron tattara bayanan aikin rigakafi na yankin, Shugaban Karamar Hukumar, Mallam Badamasi Garba Dabi ya jaddada kudirin Karamar Hukumar na ci gaba da bada gudunmuwa wajen samun nasarar shirin rigakafin.