Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
Published: 13th, March 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a AbujaYa ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da APC ba cikin shekaru biyu da suka gabata.
Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya sanar da Buhari kafin ya fice daga APC.
“Na faɗa masa game da shawarar da na yanke a ranar Juma’a. Ina yawan tuntuɓarsa kan harkokin siyasata,” in ji shi.
El-Rufa’i ya kuma tuna cewa lokacin da yake gwamna, ya taɓa miƙa wa Buhari jerin sunayen kwamishinonin da zai naɗa domin ya duba su, don tabbatar da cewa babu wanda ya taɓa zaginsa.
Da aka tambaye shi ko yana da shugabannin siyasa da yake bi, El-Rufa’i ya ce, “Ina da mutanen da nake tuntuɓa kafin na yanke hukunci, kuma Buhari shi ne na farko a cikinsu.”
Game da ko yana nadamar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sai ya ce, “Ba na nadama, amma wasu abubuwa sun ba ni mamaki.
“Na goyi bayan Tinubu ne saboda wasu shugabannin Musulmi na Yarbawa sun faɗa min cewa an mayar da su saniyar ware a siyasa, kuma na yi imanin cewa dole a bai wa Kudancin Najeriya mulki domin yin adalci da daidaito.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buhari tsohon gwamna El Rufa i ya
এছাড়াও পড়ুন:
Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar.
Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.
Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya.
Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka.
Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar.
“Ina son na bayyana a fili cewa ba na goyon bayan korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike daga PDP. Wannan mataki ba zai amfani jam’iyya ba. Ba zan shiga cikin abin da zai ƙara ruguza jam’iyya ba,” in ji shi.
Fintiri, ya ce yana ganin zaman lafiya da haɗin kai sun ɗore a jam’iyyar PDP.
Ya roƙi ’ya’yan jam’iyyar da su mayar da hankali kan yin sulhu maimakon ƙara haddasa rikice-rikice.
“Na yi imani cewa sulhu da fahimtar juna su ne hanyar da ta fi dacewa. Ina kira ga kowa ya yi aiki don ganin an samu haɗin kai a cikin jam’iyya.”
Fintiri, na cikin gwamnoni huɗu da suka halarci taron, kuma shi ne Shugaban Kwamitin Shirya Taron.
Gwamnonin Jihar Osun, Ademola Adeleke; Taraba, Agbu Kefas; da Ribas, Siminalayi Fubara ba su halarci taron ba.