Aminiya:
2025-05-02@05:22:51 GMT

Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas

Published: 13th, February 2025 GMT

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (Kwastam) reshen yanki 2 da ke Onne a Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro sun lalata kimanin kwantena 60 na kayayyakin da ba su da inganci da magungunan da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba.

Kayayyakin da  kuɗinsu ya haura Naira biliyan 100.

Lamarin ya faru ne a wurin da ake zubar da shara a Jihar Ribas daura da titin filin jirgin sama na Fatakwal a ranar Laraba.

Malaman Firamare sun sake tsunduma yajin aiki kan rashin albashi a Abuja Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf

Da yake jawabi a wurin da aka gudanar da aikin, mataimakin shugaban hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam daga sashin tabbatar da doka da bincike na Kwastam, Timi Bomodi, ya ce wannan aiki na haɗin gwiwa ne da kwamitin da aka kafa wanda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya kafa.

Bomodi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da ke kula da lalata magunguna da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba, ya ce, “Kwamiti ne da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya kafa wanda ya ƙunshi dukkan hukumomin da suka dace.

“Saboda haka, muna nan a yau don aiwatar da babban maƙasudin aikin, wanda shi ne lalata irin wannan. Aikin da aka bai wa wannan kwamiti shi ne gano da ware kayayyakin da lalata magungunan da aka shigo da su ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba.

“A nan Fatakwal, muna lalata kimanin kwantena 64 masu tsawon ƙafa 40 da darajar kuɗinsu ta kai ɗaruruwan biliyoyin Naira.

“Kuma kamar yadda yake a yau, muna aiwatar da aikin ba tare da tsoro ko yi wa wasu alfarma ba, kuma muna aika saƙo a bayyane ga duk masu irin wannan aiki da ya kamata su daina.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwastam

এছাড়াও পড়ুন:

Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Trump Kwanaki 100 Bayan Kama Aiki

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Yadda naira biliyan ɗaya ta salwanta a gobarar Kasuwar Jos
  • Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan
  • Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas
  • Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Trump Kwanaki 100 Bayan Kama Aiki
  • Mutum 20,000 Sun Nemi Gurbin Aikin Mutum 4,000 Cikin Kwana Ɗaya A Adamawa
  • Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
  • Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani