Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas
Published: 1st, May 2025 GMT
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas.
Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin.
Jami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar Aniaku, ba a samu asarar rai ba, kuma an kuɓutar da akasarin kayayyakin fasinjojin tare da ceto su daga cikin jirgin.
Rundunar sojin ruwan ta ce jami’anta da ke NSS 035 tare da tallafin jiragen ruwa huɗu sun ƙaddamar da aikin bincike mai inganci, inda suka yi nasarar ceto dukkan fasinjoji 99.
“Saboda saurin agajin da tawagar ceto ta yi, ba a sami asarar rayuka ko jikkata ba,” in ji Rundunar Sojan Ruwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fatakwal
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp