Aminiya:
2025-08-08@19:36:36 GMT

Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji

Published: 1st, May 2025 GMT

A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kaptin Reuben Kovangiya, a hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso gabas ta Operation HAƊIN KAI.

’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta

Ya fayyace cewa fashewar ta faru ne ba sakamakon wani harin maƙiya ba, illa dai lamarin ya faru ne sakamakon yanayin zafi da ake fama da shi a halin yanzu da ya shafi makaman da aka ajiye a cikin ginin.

“Fashewar ta faru ne saboda yanayin zafi da ake ciki a Maiduguri, wanda ya kai ga fashewar wasu alburusai,” in ji Koɓangiya.

Ya ƙara da cewa, tuni an shawo kan lamarin ba tare da ɓata lokaci ba ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Borno da sauran sassan bayar da agajin gaggawa daga jami’an tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “An tura dakarun Operation HAƊIN KAI domin kare jama’a da kuma hana miyagu yin amfani da abin da ke faruwa.”

Don haka rundunar ta buƙaci mazauna yankin da su yi watsi da duk wani jita-jita na kai hari a ƙaramar hukumar Maiduguri kuma su kwantar da hankalinsu akan hakan.

“Don haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani hasashe na harin… kuma su kwantar da hankula,” in ji Koɓangiya.

Rundunar Operation HAƊIN KAI dai na ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas ba dare ba rana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Operation Haɗin Kai

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan karɓar belin wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ya yi.

Namadi ya yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ya kafa kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne don “amfanin jama’a gaba daya” da kuma kare gwamnatin a “yaƙin da take yi da sayarwa da shan miyagun kwayoyi.”

Sai dai ya dage kan cewa ba shi da laifi, amma ya yarda cewa ra’ayin jama’a na da muhimmanci, kuma yana da kyau ya kare kimar gwamnatin.

Tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan alheri.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci da yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.

Gwamna Abba ya kuma jaddada muhimmancin dukkan jami’an gwamnati su riƙa yin taka-tsantsan da neman izini daga manyan hukumomi kan batutuwa masu mahimmanci na jama’a.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bango Ya Kashe Mutum 6, Ya Raunata Wasu A Katsina
  • Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
  • Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo
  • An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
  • Jama’a Suke Tona Asirin Gurɓattun Jami’anmu – Kwamishinan ‘Yansandan Kano
  • Rundunar NSCDC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Hada-hadar Miyagun Kwayoyi A Kano
  • Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
  • ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’
  • Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano
  • Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina