Gwamnatin Jihar Za Ta Ci Gaba Da Bullowa Da Dubarun Bunkasar Ta
Published: 1st, May 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta sake jaddada kudirinta na kara bude kofa ga al’umma domin ci gaba da kuma sanya jihar ta yadda za ta yi tasiri a duniya ta hanyar sanya hannun jari mai inganci.
Kwamishinan Ayyuka na Jiha Injiniya. Abdulquawiy Olododo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da ayukkan ma’aikatar a taron manema labarai na wata 3 na farkon shekara ta 2025, wanda aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar kudi, Ilorin.
A cewarsa jimillar ayyuka 46 da ake ci gaba da gudanarwa a cikin kwata na farko na shekarar 2025, daga cikin su 33 an kammala su baki daya, inda a yanzu haka ayyuka 11 ke ci gaba da gudana.
Ya kara da cewa, an bayar da sabbin ayyukan tituna guda 24 a shekarar 2025 kadai, inda 6 tuni aka kammala su.
Kwamishinan ya bayyana yadda ake ci gaba da gudanar da aikin titin Agbamu – Ila-Orangun, hanya ce mai matukar muhimmanci a tsakanin jahohin kasar da nufin bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma inganta hanyoyin shiga tsakanin jihohin Kwara da Osun.
Kwamishinan ya kuma sanar da cewa, hukumar kashe gobara ta jihar, ta tanadi kadarorin da darajarsu ta kai ₦728,478,052,012, wanda hakan ke nuni da karfafa tsarin bayar da agajin gaggawa na gwamnati.
Ya ci gaba da cewa, aikin titin RAAMP mai tsawon kilomita 209.77 da ake yi ya samu lambar yabo ta kasa guda biyu – Best in Counterpart Funding and Best in General Disbursement – wanda ya nuna kwazon gwamnati.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.
A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.
Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.
Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.
Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.
Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.
Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.
A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.
Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani ya wakilta, ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.
Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.
Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.
Usman Muhammad Zaria