NAJERIYA A YAU: Yadda naira biliyan ɗaya ta salwanta a gobarar Kasuwar Jos
Published: 2nd, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato.
An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo.
Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu.
Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar TatsuniyaWannan na cikin batutuwan da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko
Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya.
Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja
Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai Mai wakiltar Mazaɓar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato, Honorabul Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shiryawa.
A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye-shiryen gasar ta duniya, wanda Gwanayen Alƙur’ani daga faɗin kasar nan suka halarta, Honourable Alkali ya ce tuni an sanar da cibiyar bunƙasa karatun addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sakkwato kuma ta goyi bayan ƙudirin.
Ya ce gasar na da nufin haɓaka harkokin addinin Musulunci da haɗin kan Musulmi, yana mai bayyana muhimmancin tattaunawar karanta Alƙur’ani Mai Girma wanda shi ne babban malamin da ke wanke zuciya da samar da shiriya ga al’ummar Musulmi.
Da yake alƙawarin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Alkali ya bayar da misalin yadda wani bawan Allah ya yi ƙoƙarin shirya gasar karatun Alƙur’ani ta duniya amma ba a samu nasara ba saboda wasu ƙalubale da aka fuskanta.
A jawabinsa, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Gwani Sadiq Zamfara, ya yi bayanin irin ayyukan da kwamitin ya gudanar da nufin ganin an samu nasarar gudanar da gasar ba tare da matsala ba, sannan ya yi godiya ga wanda ya ɗauki nauyin shirya gasar.
Kasashen da ake tsammanin za su halarci gasar sun haɗa da Kamaru da Ghana da Chadi da Senegal da Kenya da Tanzania da Mauritania da Masar da Moroko da Libya da Algeria da Saudiya da Kuwait da Qatar da Malaysia da Ingila da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Amurka.
Ko wace ƙasa zata zo da mahalarta gasar maza da mata da kuma hukumomin su.