Gwamnatin Tarayya Ta Raba Rigunan Kariya Ga Wasu Jihohin Najeriya.
Published: 1st, May 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya.
Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da rayuwar ’yan Najeriya da ke dogaro a kullum kan hanyoyin ruwa na cikin kasa wajen sufuri da kasuwanci.
Ya amince da dimbin karfin tattalin arzikin magudanan ruwa a kasar nan da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon yawaitar hadurra na kwale-kwalen da ke bukatar hada kai, da kuma daukar matakai bisa dabaru don haka aka fara raba riguna 3,500 a matakin farko ga jihohi 12 ciki hadda jihar Neja.
Ministan wanda ya yabawa Gwamna Umar Bago bisa ga kokarin da yake yi na ganin ya inganta harkokin sufurin koguna a cikin Jihar tare da sayo da rarraba jiragen ruwa guda biyar ya yi kira ga sauran gwamnonin Jihohi da shugabannin al’umma da su yi koyi dashi.
A nasa jawabin gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa NIWA da sauran masu ruwa da tsaki za su aiwatar da aikin da aka wajaba na amfani da rigar kariya da kuma bin dukkan ka’idojin kiyaye hanyoyin ruwa a jihar.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkin Daji ya wakilce shi ya yi tir da yadda ake tafka ta’asa a cikin kwale-kwale a jihar inda ya ce gwamnatin jihar ta gano musabbabin hatsarin kwale-kwale a jihar kuma ta kuduri aniyar magance ta ta hanyar tabbatar da doka da oda da kuma zuba jari a hanyoyin ruwa.
Manajan Darakta kuma babban jami’in gudanarwa na hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa NIWA, Bola Oyebamiji wanda shi ma ya amince da kudurin Gwamna Bago na magance matsalolin da suka shafi harkar sufurin ruwa, ya bayyana bukatar kara karfafa hadin gwiwa da abokan hulda wajen dakile bala’in da jiragen ruwa ke tafkawa a hanyoyin ruwa.
Kwamishiniyar Sufuri, Hajiya Hadiza Idris Kuta ta yabawa ma’aikatar harkokin ruwa da tattalin arzikin kasa bisa tallafin da take baiwa jihar Neja da samar da motocin daukar marasa lafiya da kwale-kwalen fasinja da suka hada da samar da jami’an kula da ruwa da aka jibge a yankunan gabar tekun jihar yayin da ta kuma yarda cewa rigunan ceton da aka raba wa jihar zai taimaka matuka.
Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja Alh, Yahaya Abubakar wanda Wambai Nupe, Injiniya Ndagi Aliyu ya wakilta ya sake jaddada bukatar cibiyoyi na gargajiya a matsayinsu na masu ruwa da tsaki a matakin kasa da su kara kaimi wajen wayar da kan al’ummarsu kan bukatar kiyaye hanyoyin ruwa.
KARSHEN ALIYU LAWAL.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: a hanyoyin ruwa kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.
Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban.
Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane take, wato idan an dage kan yakin, ko kadan ba za mu ja da baya ba. Idan an shirya tattaunawa, dole ne mu girmama juna tare da yin zaman daidaito da juna. Ba don hakkinta na kanta ba ne, kasar Sin tana kuma kiyaye muradun bai daya na dukkanin kasashe. Abun da kasar Sin ke kiyayewa ba kawai hadin gwiwar cin moriyar juna ba ne, har ma da ka’idojin kasa da kasa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp