Aminiya:
2025-11-02@11:29:10 GMT

Gwamnonin Arewa maso Gabas sun buƙaci a ɗauki mataki kan matsalolin yankin

Published: 2nd, May 2025 GMT

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin  Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu.

Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu yayin jawabinsa na maraba yadda ya  bayyana fatansa cewa, taron zai samar da sabbin dabarun yaƙi da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.

Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara

Buni ya bayyana wannan ƙungiyar a matsayin wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa da daidaita manufofi, musamman yadda yankin ke fama da sabbin hare-hare daga ƙungiyar Boko Haram da kuma amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare.

“Wannan taron ya zo kan lokaci. Dole ne mu yi aiki da sauri don ƙarfafa nasarorin da muka samu wajen gina zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arziki,” in ji shi.

Ya yi kira da a raba ƙudurori daga taron da hukumomin tsaro na tarayya domin bunƙasa haɗin kai da hanyoyin mayar da martani cikin gaggawa.

Gwamna Buni ya kuma nuna jin daɗinsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayansa da jagoranci, sannan ya mika godiyarsa ga rundunonin sojan ƙasar, rundunar hadin gwiwa ta farar hula da masu aikin sa kai bisa sadaukarwar da suka yi.

A kan farfaɗo da tattalin arziki, ya yi kira wajen neman saka hannun jari a harkar noma, samar da ayyukan yi da kuma shirye-shiryen rayuwa mai ɗorewa.

“Dole ne mu sanya aikin noma ya zama abin sha’awa, mai araha, kuma mai riba don amfani da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam,” in ji shi.

Ana sa ran taron zai fitar da ƙudurori da nufin ƙarfafa ayyukan tsaro na haɗin gwiwa, da daidaita ayyukan jin ƙai da inganta kasuwanci da zuba jari a yankin.

Yayin da yankin ke ci gaba da bin hanyoyin farfaɗowa, hakan ya sake tabbatar da abu guda: hanyar samar da zaman lafiya da walwala wadda  ta ta’allaka ne a cikin haɗin kai da hangen nesa da aiki tuƙuru.

Da yake jawabin maraba ga gwamnonin na Arewa maso Gabas wajen wannan taron shugaban Ƙungiyar gwamnnonin Arewa maso Gabas Farfesa Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya bayyana irin ƙalubalen da wannan yanki ke fuskanta dangane da harkokin tsaro da kuma talauci, yadda ya nemi al’ummomin yankin da su yi ƙoƙari wajen ganin an samu canji.

Ya kara da cewa, akwai buƙatar da haɗa kai don ganin an samu nasarar wajen shawo kan wannan matsala ta dawo da taɓarɓarewar harkokin tsaro a wannan yanki wadda kuwa babbar matsala ce.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Adamawa Taraba Arewa maso Gabas

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya.

Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u

A ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya.

Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen “ceto Kiristoci” a Najeriya da wasu ƙasashe.

Shehu Sani, ya mayar da martani da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce, domin matsalar tsaro a Najeriya ba ta da nasaba da addini.

Ya ce Musulmai da Kiristoci dukkaninsu suna fuskantar hare-haren’yan ta’adda da garkuwa da su.

“Wannan zargi ƙarya ne. ’Yan ta’adda da ’yan bindiga a Najeriya suna kashe mutane ba tare da la’akari da addininsu ba. Wannan abin na faruwa tun kusan shekaru 15 da suka wuce,” in ji shi.

Sani, ya ƙara da cewa, saboda yawan Musulmai da Kiristoci a Najeriya, ba zai yiwu addini ɗaya ya zalunci ɗaya ba.

“Idan aka duba yadda Musulmai da Kiristoci suke kusan daidai a Najeriya, ba zai yiwu ɗaya ya zalunci ɗaya ba. Najeriya kamar zaki da damisa ce, dukkanin ɓangarorin suna da ƙarfi,” in ji shi.

Ya zargi waɗanda suka zuga Trump da amfani da rikice-rikicen cikin gida na Najeriya.

“Trump ya samu bayanan ƙarya daga mutanen da ke son raba Najeriya domin su ci moriya daga wannan,” in ji shi.

“Wannan makirci da aka yi wa ƙasar nan ba zai yi nasara ba.”

Sani, ya roƙi ƙasashen duniya su taimaka wa Najeriya wajen yaƙar ta’addanci, maimakon yaɗa labaran ƙarya.

“Najeriya na buƙatar taimako da haɗin kai wajen shawo kan matsalar tsaro, kamar sauran ƙasashen da ke fama da ta’addanci,” a cewarsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
  • Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja
  • Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin